Ministan Buhari, Malami Ya Fice daga APC, Ya Zaɓi Sabuwar Jam'iyyar Haɗaka

Ministan Buhari, Malami Ya Fice daga APC, Ya Zaɓi Sabuwar Jam'iyyar Haɗaka

  • Tsohon Ministan Shari'a Abubakar Malami SAN ya fice daga jam’iyyar APC, yana cewa Najeriya na cikin mawuyacin hali a yau
  • Malami ya ce matsalolin tsaro da na tattalin arziki sun jefa talakawa cikin wahala, yayin da gwamnati ke fifita siyasa fiye da rayukan jama'a
  • Babban lauyan ya ce shigarsa ADC ba cikin fushi ba ne, sai dai kishin kasa da yunkurin ceto Najeriya daga halin da take ciki

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Tsohon minista kuma babban lauyan gwamnatin Muhammadu Buhari ya yi murabus daga jam'iyyar APC mai mulki.

Tsohon ministan Shari'a, Abubakar Malami SAN ya ce ya dauki matakin ne saboda tabarbarewar lamura.

Ministan Buhari ya yi murabus daga jam'iyyar APC
Abubakar Malami ya koma jam'iyyar ADC a Najeriya. Hoto: Abubakar Malami.
Source: Twitter

Abubakar Malami ya watsar da jam'iyyar APC

Hakan na cikin wata sanarwa da ya wallafa a yau Laraba 2 ga watan Yulin 2025 a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: Tsohon gwamna da ya bar APC ya fallasa shirin INEC na murde zaben 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon ministan ya ce ya dauki wannan matakin ne bayan shawarwari da tunani mai zurfi.

Malami ya tabbatar da cewa bayan nazari mai zurfi ya yanke shawarar shiga jam'iyyar ADC domin kawo sauyi a Najeriya.

"Ƴan uwa ’yan Najeriya da mutanen Jihar Kebbi, bayan shawarwari da tunani mai zurfi, na sanar da ficewata daga jam’iyyar APC.
"Na yanke shawarar shiga jam’iyyar ADC, wacce hadakar masu kishin kasa suka amince da ita domin ceto Najeriya daga tabarbarewa.
"Wannan ba matakin fushi ba ne ko sha’awar mulki, amma saboda ƙaunar ƙasa da damuwa da wahalhalun da mutane ke fuskanta."
Abubakar Malami ya tattara kayansa a APC zuwa ADC
Abubakar Malami ya fice daga APC zuwa jam'iyyar ADC. Hoto: Abubakar Malami.
Source: Facebook

Dalilan Malami na barin jam'iyyar APC

Abubakar Malami ya ce ana yawan zubar da jini a Najeriya kuma babu tsaro kwata-kwata musamman a Arewacin kasar.

Malami ya tabo batun tattalin arziki inda ya soki gwamnatin APC ta durkusar da komai wanda zai kawo cigaba.

"Ana zubar da jini a Najeriya, Tsaro ya ɓaci, musamman a Arewa, ’Yan bindiga da masu garkuwa sun mamaye ko ina.

Kara karanta wannan

Zaɓen 2027: Matsalar farko da haɗakar Atiku da ƴan adawa ta fara cin karo da ita

"Tattalin arziki ya durƙushe, farashin abinci ya tashi sau uku, Talakawa sun kasa ciyar da iyali, matasa ba su da aikin yi.
"An watsar da shugabanci, aiki da nade-nade yanzu sun koma bisa biyayya ba ƙasa ba, ba zan zauna cikin wannan tsarin ba."

Tsohon minista ya shawarci yan Najeriya

Malami ya ce ya shiga ADC domin adalci, kwarewa da farfado da kasa inda ya ce ya gaskata cewa tare da hadin kan jama’a za a yi nasara.

Ya ce har yanzu shi ɗan mutanen Jihar Kebbi ne kuma zai ci gaba da kare muradunsu da yaki domin makomar al’umma ta gaba.

Ya shawarci yan Najeriya da cewa lokaci ya yi da za a tashi tsaye a cire tsoro domin kwato ƙasar inda ya ce Najeriya mallakin kowa da kowa ce.

Malami ya caccaki Tinubu, APC kan tsaro

Mun ba ku labarin cewa tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya soki jam’iyyar APC bisa nuna goyon baya ga Bola Tinubu a 2027 duk da halin da kasa ke ciki.

Kara karanta wannan

ADC: Haɗakar Atiku ta fara ƙarfi, tsohon shugaban Majalisar Dattawa ya fice daga PDP

Malami ya ce gwamnati ta fi maida hankali kan siyasa maimakon warware matsalolin da ke damun talakawa musamman a Arewa.

Tsohon ministan ya yi magana ne yayin da wasu 'yan siyasa a Arewa suka cimma matsaya kan hada kai don samun madafa mai ƙarfi a siyasar Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.