Shekara 1 da Rasuwarsa, Ƴar Uwar Ɗan Majalisa Ta Ajiye Aiki, Za Ta Tsaya Takara a Zaɓe

Shekara 1 da Rasuwarsa, Ƴar Uwar Ɗan Majalisa Ta Ajiye Aiki, Za Ta Tsaya Takara a Zaɓe

  • Fitacciyar 'yar jarida Amina Dogon-Yaro ta ajiye aikinta a NTA bayan shekaru 15, don ta tsaya takarar majalisar tarayya a Garki/Babura
  • Amina ta bi dokar ƙasa ta ajiye aiki kwanaki 30 kafin zaɓe, kuma ta miƙa takardar murabus tare da shaidar biyan albashi na watanni uku
  • Jama'a sun nuna goyon baya da fatan alheri ga burin Amina Dogon-Yaro, yayin da suke ƙarfafa gwiwar sauran mata su shiga fagen siyasa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jigawa - Fitacciyar ma'aikaciyar jarida, wadda take aiki a gidan talabijin na kasa (NTA), Amina Dogon-Yaro ta sanar da ajiye aikinta da gwamnatin tarayya.

Amina Dogon-Yaro ta bayyana cewa ta ajiye aikin ne domin ta samu damar tsayawa takarar kujerar majalisar tarayya ta mazabar Garki/Babura, a jihar Kano.

Amina Dogon-Yaro, 'yaruwar dan majalisar da ya rasu a Jigawa za ta fito neman kujerarsa
Amina Dogon-Yaro, 'yaruwar Isa Dogon-Yaro, dan majalisar Jigawa da ya rasu a 2024. Hoto: Meena Dogon-Yaro
Source: Facebook

Amina Dogon-Yaro za ta fito takarar Garki/Babura

Kara karanta wannan

A ƙarshe, Atiku, El Rufai da Obi sun haɗe kansu, sun zabi jam'iyyar doke Tinubu a 2027

A cikin sakon da ta wallafa a shafinta na Facebook a ranar 30 ga watan Yuni, tsohuwar 'yar jaridar, ta ce ta shafe shekaru 15 tana aiki a NTA.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amina Dogon-Yaro ta ce tuni ta aika takardar ajiye aikin ga hukumar gudanarwar gidan talabijin din na kasa, domin kiyaye dokokin kasa.

A sakon da ta wallafa, ta ce:

"A yau ne, 30-06-25 na ajiye aiki na da Nigeria Television Authority, bayan shekara 15 Ina aiki da su.
"Haka ya faru ne saboda takarar kujerar majalisar wakilai ta mazabar Babura/Garki da na ke nema. Kundin dokar kasa, sashe 182(1)(g) of 1999 ya ce;
"Ya zama wajibi kowanne ma'aikacin gwamnati da zai nemi takarar zabe ya ajiye aikinsa kwanaki 30 kafin ranar zaben."

Dogon-Yaro ta ajiye aiki don maye gurbin kaninta

Tare da wannan sako da ta wallafa, Amina Dogon-Yaro ta wallafa hoton takardar ajiyen aikin da ta aika wa hukumar gudanarwar NTA.

Wasikar an rubuta ne zuwa ga babban darakta, sashen gudanarwa da horaswa, na hukumar gidan talabijin ta Najeriya (NTA), ta hannun babban manaja, gidan talabijin ta Najeriya (NTA), reshen Kano.

Kara karanta wannan

Ku zo ku siya: AMCON ta saka kadarorin gwamnati 10 a kasuwa, ana neman masu saye

Legit Hausa ta ciro bayanan da takardar ta kunsa kamar haka:

"Na rubuto wannan wasiƙa ne domin sanar da murabus di na daga aiki a hukumar talabijin ta Najeriya (NTA) daga ranar 30 ga Yuni, 2025.
"Na fara aiki da hukumar a watan Oktoba, 2009 a matsayin mai shirya shirye-shirye ta II, kuma na kwashe shekaru 15 ina wannan aiki cikin nasara.
"Zan mayar da duk wasu kayayyakin gwamnati da ke hannuna, kuma na haɗa da shaidar biyan albashin watanni 3 na Yuli, Agusta da Satumba, 2025.
"Ina fatan wannan murabus ɗin zai samu karɓuwa yadda ya kamata."

Dalilin shiga zaben majalisar Garki/Babura

Legit Hausa ta fahimci cewa Amina Dogon-Yaro ta shiga zaben ne domin maye gurbin kujerar da a yanzu babu kowa kanta bayan rasuwar Isa Dogon-Yaru.

Isa Dogon-Yaro, ya rasu ne a ranar 10 ga watan Mayun 2024 kamar yadda muka ruwaito, wanda ya sa kujerar majalisar tarayyar ta Babura/Garki ta zamo ba kowa a kanta.

Bincike ya nuna cewa Amina Dogon-Yaro, yayar marigayi Isa Dogon-Yaro ce, kuma tana da burin maye gurbin kujerar da kanin nata ya rasu ya bari.

Kara karanta wannan

Gwamnonin Kudu maso Gabas sun yiwa PDP barazana ana fama da rikicin cikin gida

Amina na kokarin maye gurbin kujerar Garki/Babura da kaninta, Isa Dogon-Yaro ya rasu ya bari
Dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabun Garki da Babura, Isa Dogonyaro, daga jihar Jigawa ya rasu a 2024. Hoto: Isa Dogon-Yaro
Source: Facebook

Mutane sun yi martani kan shiga zaben Dogon-Yaro

Legit Hausa ta tattaro wasu daga cikin ra'ayoyin jama'a dangane da matakin Amin Dogon Yaro:

Mudassir Aliyu:

"Ma'aikatan NTA za su yi kewar mai shirya kayatattun shirye-shirye kamarki. Sai dai kuma siyasa harka ce mai kyau musamman a cikin al'ummarmu inda mata ba su da yawa a harkokin siyasa.
"Ina yi miki fatan alheri, kuma ki tuna muna goyon bayan burin ki na siyasa, za mu ba da gudummawarmu don tabbatar da burin ki. Allah ya ba da nasara Hajiya Meena Dogonyaroo.
"A halin yanzu, za mu ƙarfafi gwiwar irisn su Sumayyah Sarina, Khadija Aliyu Ammani, Zainab Nasir Ahmad su bi sawun ki."

Larai Musa:

"Anty Mino, da izinin Allah sai kin yi, a fara gwada mu a Jigawa, sai mai dan kwali, In sha Allah."

Hassan M A Bamalli:

"Gaskiya ban ji dadi ba! Amma Allah ya sa haka shi ya fi alkhairi, Allah ya ba da sa'a da nasara."

Kara karanta wannan

'Ka ƙaƙaba mana dokar ta ɓaci kawai': Dattawan Arewa sun roƙi Tinubu alfarma

Dokar Najeriya kan ma’aikacin gwamnati da ke son takarar

A bisa tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999, sashe na 182(1)(g) (da kuma sashe 107(1)(g) ga 'yan majalisun jiha), duk wani ma’aikacin gwamnati da ke son tsayawa takara dole ne ya ajiye aikinsa kafin ya shiga harkar siyasa.

Wannan tanadi yana nufin duk wanda ke karɓar albashi daga gwamnati – ko a matakin tarayya, jiha ko ƙaramar hukuma – ba zai iya tsaya wa takara ba muddin yana rike da mukamin gwamnati.

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana a lokuta da dama cewa dole ne ma’aikacin gwamnati da ke son takara ya yi murabus daga mukaminsa kafin aƙalla kwanaki 30 da zabe.

INEC za ta gudanar da zaben cike gurbi a jihohi

Tun da fari, mun ruwaito cewa, INEC ta shirya gudanar da zaɓen cike gurbin kujerun 'yan majalisar jiha da tarayya 12 a ranar 16 ga Agusta, 2025, a jihohi 12 na ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Rigimar APC: Ganduje ya yi murabus daga kujerarsa ta shugabancin jam'iyyar

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa guraben da za a cike sun samu ne sakamakon murabus, rasuwa ko soke zaɓen da aka yi a baya.

Sai dai hukumar ta ce an dage zaɓen cike gurbi a wasu mazabu biyu da ke jihohin Rivers da Zamfara saboda dokar ta-baci da kuma wasu shari’u da ke gaban kotu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com