A ƙarshe, Atiku, El Rufai da Obi Sun Haɗe Kansu, Sun Zabi Jam'iyyar Doke Tinubu a 2027

A ƙarshe, Atiku, El Rufai da Obi Sun Haɗe Kansu, Sun Zabi Jam'iyyar Doke Tinubu a 2027

  • Ƙungiyar hadakar 'yan adawa da Atiku Abubakar ke jagoranta ta zaɓi ADC a matsayin jam'iyyar da za ta kalubalantar APC a 2027
  • An naɗa David Mark a matsayin shugaba, Rauf Aregbesola matsayin sakatare da kuma Bolaji Abdullahi a matsayin kakakin ADC
  • Atiku Abubakar, Peter Obi, Nasir El-Rufai sun nuna yakini cewa jam'iyyar ADC za ta doke Shugaba Bola Tinubu da APC a 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja – Ƙungiyar hadakar 'yan adawa da Atiku Abubakar ke jagoranta ta zabi ADC a matsayin jam'iyyar da za ta yi amfani da ita wajen doke Shugaba Bola Tinubu a 2027.

Wannan mataki ya biyo bayan ganawar da shugabannin ƙungiyar suka gudanar daga Talata zuwa Laraba, bayan jinkirin INEC na yi wa jam'iyyar da ƙungiyar ke so, watau ADA, rajista.

Kara karanta wannan

Haɗaka: An faɗi ƴan siyasa 7 a ADC da ke neman takara domin karawa da Tinubu

Atiku Abubakar, Peter Obi, Nasir El-Rufai da sauran 'yan adawa sun zabi ADC domin doke APC a 2027
Peter Obi, Nasir E-Rufai da Atiku Abubakar sun haɗa kansu gabanin 2027. Hoto: @muhammaddayyiib/Pius Utomi Ekpei
Source: Twitter

Atiku, El-Rufai, Obi sun zabi jam'iyyar ADC

Tsohon sanatan Katsina ta Arewa, Ahmad Babba Kaita, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Talata, 1 ga Yuli.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar, wadda Dr. Uche Diala, daya daga cikin shugabannin ƙungiyar hadakar ta kasa (NCM) ya fitar, ta bayyana cewa:

“Muna sanar da ku cewa ƙungiyar hadakar 'yan adawa ta kasa (NCM) ta ɗauki ADC a matsayin jam'iyyarta domin tunkarar zaɓen 2027.”
“An cimma wannan matsaya ne a wani taron manyan shugabannin ƙungiyar da aka yi ranar 1 ga Yuli, 2025. Wannan shawarar ta samu amincewar dukkanin 'ya 'yanta."

David Mark ya zama shugaban hadakar ADC

Domin tabbatar da nasarar wannan matakin, shugabannin NCM sun amince da naɗa fitattun ‘yan siyasa a matsayin shugabannin rikon kwarya na jam'iyyar ADC:

Wadanda aka nada su ne:

  1. Tsohon shugaban majalisar dattawa David Mark a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa,
  2. Tsohon gwamnan Osun, Rauf Aregbesola a matsayin sakataren jam'iyyar na kasa,
  3. Tsohon ministan matasa da wasanni, Bolaji Abdullahi, a matsayin kakakin jam'iyyar

Kara karanta wannan

'Babu abin da zai raba ni da Buhari': Tsohon minista ya musanta barin jam'iyyar APC

An ce nada wadannan ƙwararrun a matsayin shugabannin ADC zai tabbatar da cewa jam'iyyar 'yan adawar ta doke APC mai mulki a matakin kasa da ma jihohi.

Manyan 'yan adawa sun zabi ADC matsayin jam'iyyar hadaka gabanin zaben 2027
Atiku Abubakar da wasu jiga-jigan PDP sun tattauna tare da amince da amfani da ADC a 2027. Hoto: Imran Muhammad
Source: Facebook

An aika sako ga 'yan takarar SDP da LP

A cewar sanarwar Dr. Uche Diala:

“Yana da muhimmanci mu sanar da magoya bayanmu da mambobin SDP cewa waɗanda suka riga suka shirya tsayawa takara a jam’iyyunsu kamar SDP da LP za su ci gaba da zama a can. Kuma ƙungiyar haɗin gwiwa za ta tallafa musu.
“Muna tabbatar maku da cewa wannan jam'iyyar ta haɗin gwiwa ta ginu ne a kan gaskiya, sadaukarwa da kishin ƙasa da shugabanninmu suka nuna.”

Rahoton jaridar Premium Times ya nuna cewa ƙungiyar za ta ci gaba da bin hanyoyin shari’a domin ganin an yi wa jam’iyyar ADA rijista.

Ƙungiyar adawar na kunshe da manyan jiga-jigan siyasa irin su Atiku Abubakar, Peter Obi, Nasir El-Rufai, Bukola Saraki, Rotimi Amaechi, Abubakar Malami da sauransu.

"Muna tare da Atiku har gaban ADC" - Surajo Caps

Matashin dan siyasar nan na jihar Bauchi, Alhaji Surajo Caps ya shaidawa Legit Hausa cewa yana tare da Atiku Abubakar ko a PDP, ko ADC ko kuma ADA.

Kara karanta wannan

Atiku ko Obi?: Malamin addini ya hango wanda jam'iyyar ADC za ta ba tikiti a 2027

Surajo Caps ya ce:
"Mu muna tare da Atiku Abubakar a duk inda zai je. Yanzu da suka jagoranci shiga ADC, to za mu shiga ADC tare da shi, idan kuma INEC ta yiwa ADA rajista, nan ma za mu shige tare da shi.
"Mu canji muke nema, mun gaji da wannan gwamnatin, muna neman canji, kuma muna da yakinin cewa Atiku ne zai iya kawo mana wannan canjin tare da sauran jagororin adawa."

Surajo Caps ya ce yana fatan shugabannin adawar za su hade kansu tare da tsayar da Atiku matsayin dan takarar ADC domin kayar da gwamnatin Tinubu a 2027.

ADC: 'Za a tara miliyoyin kuri'u don doke Tinubu'

A wani labarin, mun ruwaito cewa, jam’iyyar ADC ta bayyana shirin ta na tattara masu kada kuri’a miliyan 35 domin kalubalantar APC da Bola Ahmed Tinubu a 2027.

Shugaban jam’iyyar na ƙasa, Ralphs Okey Nwosu, ne ya bayyana hakan yayin wani muhimmin taro da jam’iyyar ta gudanar a birnin tarayya Abuja.

ADC ta ce tana haɗa kai da ƙungiyoyin fararen hula da na matasa, tare da shirin kulla babban kawance da sauran jam’iyyu domin kifar da APC a gaba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com