Bayan Ganduje, APC Ta Budewa Kwankwaso Kofar Sauya Sheka da Aiki da Bola Tinubu

Bayan Ganduje, APC Ta Budewa Kwankwaso Kofar Sauya Sheka da Aiki da Bola Tinubu

  • Jam’iyyar APC ta ce Rabiu Kwankwaso na da ‘yancin dawowa cikin jam’iyyar tare da yin aiki da Shugaba Bola Ahmed Tinubu
  • Daraktan yada labaran APC, Felix Morka, ya ce kofa a bude take ga kowa da kowa ciki har da tsohon gwamnan Kano
  • An fara rade-radin dawowarsa ne bayan Abdullahi Ganduje ya sauka daga shugabancin jam’iyyar APC bisa wasu dalilai

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Jam’iyyar APC ta ce kofofinta a buɗe suke ga tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, idan yana da niyyar dawowa domin yin aiki da shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da hasashen cewa Kwankwaso zai iya komawa jam’iyyar, musamman bayan saukar Abdullahi Ganduje daga shugabancin APC.

Kara karanta wannan

Kwankwaso zai koma APC bayan Ganduje ya yi murabus? Shugaban NNPP na Kano ya yi bayani

APC ta ce za ta iya aiki tare da Kwankwaso
APC ta ce za ta iya aiki tare da Kwankwaso. Hoto: Bayo Onanuga|Saifullahi Hassan
Source: Twitter

Daraktan yada labaran APC, Felix Morka ne ya bayyana haka a wata hira da aka yi da shi a tashar Channels Television.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwankwaso na da 'yancin shiga APC inji Morka

Felix Morka ya ce Kwankwaso ɗan Najeriya ne kuma ɗan siyasa ne da ke da ‘yancin yanke shawara, kamar yadda sauran ’yan kasa ke da wannan dama.

Vanguard ta wallafa cewa Felix Morka ya ce:

“Kwankwaso na da damar yanke shawarar komawa jam’iyyar mu idan ya ga dacewar hakan, kamar yadda sauran ‘yan siyasa ko jama’a ke da wannan dama.
"Mun saba karɓar sababbin mambobi kuma kofa a bude take.”

Morka ya ƙara da cewa APC za ta ci gaba da karɓar mutane daga kowane sashe na ƙasa, domin ƙarfafa jam’iyyar da kuma aiwatar da manufofin gwamnatin Tinubu.

Dalilin hasashen shigar Kwankwaso APC

Rahotanni sun nuna cewa tun bayan saukar Abdullahi Ganduje daga shugabancin APC, ana ta rade-radin cewa Kwankwaso na duba yiwuwar dawowa jam’iyyar.

Kara karanta wannan

'Abin da ya sa APC ke ƙoƙarin jawo Kwankwaso ya haɗe da Tinubu kafin zaɓen 2027'

A baya, Kwankwaso ya taba zama cikin APC a shekarar 2013 lokacin da ya fice daga PDP, yana mai cewa ya yi hakan domin kawo sauyi a siyasar Najeriya.

Sai dai daga bisani a 2018, ya fice daga APC zuwa PDP, inda ya ci gaba da siyasa har zuwa 2022 da ya koma NNPP domin takarar shugaban kasa.

Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso
Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Wasu rahotanni da ba a tabbatar ba suna cewa gwamnatin APC karkashin Bola Tinubu na son jawo Kwankwaso kuma haka ne dalilin murabus din Ganduje.

Karfin Kwankwaso a siyasar Najeriya

Kwankwaso ya yi aiki a mukamai daban-daban a Najeriya ciki har da zama gwamna a Kano sau biyu da ministan tsaro.

A zaben na 2023, Kwankwaso ya zo na huɗu da ƙuri’u fiye da miliyan daya, lamarin da ya tabbatar da cewa yana da farin jini a wasu sassan Arewa.

Kwankwaso zai maye gurbin Ganduje a APC?

A wani rahoton, kun ji cewa wani jigon APC ya bayyana cewa akwai alamar Sanata Rabiu Kwankwaso ya maye gurbin Abdullahi Ganduje.

Jigon jam'iyyar ya ce idan lissafin da ake ya tafi yadda ake so, Kwankwaso zai iya zama shugaban APC duk da bukatar mika shugabanci a Arewa ta Tsakiya.

Baya ga haka, kusa a jam'iyyar ya tabbatar da cewa murabus din da Abdullahi Ganduje ya yi ba shi da alaka da rikicin APC da aka yi a Gombe.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng