Sunaye: ‘Yan majalisar dokokin jihar Kano 6 da zasu bi Kwankwaso PDP
Biyo bayan ficewar tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Kwankwaso, da wasu Sanatocin Najeriya 14 daga APC tare da komawa jam’iyyar PDP, wasu ‘yan majalisar dokokin jihar Kano 6 sun shirya domin bin sahun Kwankwaso.
‘Yan majalisar 6, kamar yadda masana siyasar Kano suka sani, masu biyayya ne ga tsohon gwamna Kwankwaso, kuma nan ba da dadewa ba, cikin wasu ‘yan kwanaki, zasu koma jam’iyyar PDP domin jadda biyayyarsu gare shi.
Jaridar Daily Nigerian, ta wani na kusa da Kwankwaso, ta rawaito cewar ‘yan majalisar su ne;
1. Hamza Sule; mai wakiltar karamar hukumar Bichi
2. Rabi’u Sale Gwarzo; mai wakiltar karamar hukumar Gwarzo
3. Yusuf Falgore; mai wakiltar karamar hukmar Rogo
4. Yusuf Babangida; mai wakiltar karamar hukumar Gwale
5. Isyaku Danja; mai wakiltar karamar hukumar Gezawa da kuma
6. Zubairu Mamuda; mai wakiltar karamar hukmar Madobi
DUBA WANNAN: Hotunan wani matashi da ya sha ruwan gulbi saboda murnar ficewar Kwankwaso daga APC
Saidai bayan wasu kafafen yada labarai sun fara yada jita-jitar cewar mafi yawan mambobin majalisar dokokin jihar ta Kano sun bi Kwankwaso zuwa PDP, shugaban masu rinjaye a majalisar, Muhammad Bello Butu-butu, ya bayyana rahotannin a matsayin marasa tushe balle makama tare da bayyana labarin a matsayin yunkurin haddasa rudanin siyasa a jihar Kano.
Kazalika, Butu-butu ya bayyana cewar duk da kasancewar akwai mambobin majalisar 6 dake biyayya ga Kwankwaso, ya zuwa yanzu babu wani mamba day a fita daga APC.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng