Wike Ya Samu Yadda Yake So, PDP Ta Sanar da Sahihin Sakataren Jam'iyya Na Ƙasa
- Jama'iyyar PDP ta amince ta dawo da Sanata Samuel Anyanwu a kan kujerar sakatarenta na ƙasa bayan tsawon lokaci ana kai ruwa rana
- Muƙaddashin shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Ambasada Umar Damagum ne ya sanar da hakan a taron manema labarai a Abuja yau Laraba
- Damagum ya kuma sanar da soke taron kwamitin zartarwar PDP karo na 100, yana mai cewa za a sanar sabuwar ranar taron nan gaba kaɗan
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya watau PDP ta fara ɗaukar matakan warware rigingimun cikin gida da suka daɗe suna addabarta.
PDP ta sanar da dawo da Sanata Samuel Anyanwu, wanda ake ganin yana da alaƙa ta siyasa da Ministan Abuja, Nyesom Wike, kan kujera sakataren jam'iyyar na ƙasa.

Source: Facebook
Muƙaddashin shugaban PDP, Ambasada Umar Damagum, ne ya sanar da hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar Laraba a Abuja, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan
Kwana 1 bayan kalaman El Rufai, sabuwar jam'iyyar haɗaka 'ADA' ta gamu da matsala a INEC
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
PDP ta fara ɗaukar matakan shawo kan rikicinta
Gwamnan Bauchi kuma shugaban kungiyar gwamnonin PDP, Bala Mohammed da tsohon shugaban majalisar dattawa kuma shugaban kwamitin sulhu, Bukola Saraki sun halarci taron manema labaran.
Bayansu, Damagun ya samu rakiyar wasu manyan kusoshin PDP zuwa wurin, inda ya tabbatar da Sanata Anyanwu a matsayin sahihin sakataren jam'iyya na ƙasa.
Ya ce matakin dawo da Anyanwu kan kujerarsu, "ya kasance mai wahala, amma yawancin shugabannin PDP sun amince da hakan."
Jam'iyyar PDP ta soke taron NEC karo an 100
Bugu da ƙari, Ambasada Damagum bayyana cewa jam'iyyar PDP ta soke taron Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) karo na 100 wanda aka shirya yi kwanan nan.
A cewarsa:
"Za mu gudanar da taron shugabanni wanda za a faɗaɗa shi a jawo mutane a ciki, a wannan taro za mu yanke lokacin da ya kamata a shirya taron NEC na gaba.

Kara karanta wannan
SDP: Ana fafutukar shirin kifar da Tinubu, jam'iyyarsu El Rufai ta dakatar da shugabanta
"Anyanwu zai koma bakin aikinsa a matsayin sakataren PDP na ƙasa, shiyasa na ce wannan hukunci ne mai mahimmanci da wahala.
"Kamar yadda INEC ta faɗa, ba su karɓi sanarwarmu ta shirya taron NEC ba, don haka abin da za mu yi a ranar 30 ga Yuni shi ne taron jagororin PDP da aka faɗaɗa.”

Source: Twitter
Ana ganin dai wannan mataki na iya kawo ƙarshen rikicin kujerar sakataren PDP na ƙasa, wanda aka jima ana yi tsakanin Anyanwu da Ude Okoye.
Tawagar jiga-jigan PDP ta gana da jami'an INEC
A wani rahoton, kun ji cewa tawagar PDP ƙaraƙshin jagorancin Umar Damagum ta kai ziyara hedikwatar hukumar zabe ta kasa watau INEC da ke Abuja.
Tawagar wacce ta kunshi shugabanni, gwamnoni da manyan kusoshin PDP sun gama da INEC domin warware ruɗanin da aka samu game da taron NEC.
Sai dai shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu ya ce sun kira wannan taro ne kamar yadda PDP ta buƙata domin tattaunawa kan wasu kujerun shigabancin jam'iyyar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng