SDP: Ana Fafutukar Shirin Kifar da Tinubu, Jam’iyyarsu El Rufai Ta Dakatar da Shugabanta

SDP: Ana Fafutukar Shirin Kifar da Tinubu, Jam’iyyarsu El Rufai Ta Dakatar da Shugabanta

  • Jam'iyyar SDP ta dakatar da shugaban jam’iyyar, Shehu Musa Gabam da wasu biyu saboda zarge-zargen almundahana
  • Kwamitin NWC ya ce an kafa shi domin bincike kuma an sanar da INEC da hukumomin tsaro game da matakin
  • SDP ta ce ta dauki matakin ne don kare mutuncinta a idon jama’a da tabbatar da biyayya ga dokokin cikin gida

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Kwamitin Gudanarwa na Kasa (NWC) na SDP ya dauki mataki mai tsauri kan shugaban jam'iyyar.

Kwamitin ya dakatar da shugaban jam’iyyar na kasa, Alhaji Shehu Musa Gabam saboda wasu zarge-zarge.

SDP ta dakatar da shuganta a Najeriya
Jam'iyyar ta dakatar da shugabanta a Najeriya, Shehu Gabam. Hoto: Shehu Musa Gabam.
Source: Twitter

Musabbabin dakatar da shugabannin SDP a Najeriya

Rahoton Punch ya ce an dakatar da mai binciken kudi na kasa, Nze Nnadi Clarkson, da shugaban matasan jam’iyya, Uchechukwu Chukwuma saboda almundahana.

Kara karanta wannan

Haɗakar adawa: El Rufai ya jero ƙusoshin ƴan siyasar da ke yaƙar Tinubu da APC

Sanarwar ta bayyana cewa akwai hujjoji masu karfi da suka tabbatar da aikata laifukan karkatar da kudaden jam’iyya ba tare da izini ba.

Mai magana da yawun jam'iyyar SDP, Araba Rufus Aiyenigba ya ce matakin ya biyo bayan yanke shawarar NWC a taronsu na baya-bayan nan.

Matakin da jam'iyyar SDP ta dauka a yanzu

Jam’iyyar ta ce matakin ya yi daidai da tanade-tanaden kundin tsarin mulkinta, musamman sashe na 19.1, 19.3(i), da 19.5, cewar The Guardian.

NWC ya ce wannan mataki na dakatarwa yana da nufin tabbatar da gaskiya da adalci da kuma dakile cin hanci da rashawa.

Jam’iyyar SDP ta ce kwamitin bincike na wucin gadi ya fara aiki domin tantance kudaden da aka karkatar da kuma daukar matakin doka.

SDP ta dauki mataki kan shugabanta bayan zarge-zarge
Jam'iyyar SDP ta dakatar da shugabanta, Shehu Musa Gabam. Hoto: Nasir El-Rufai, Shehu Musa Gabam.
Source: Facebook

SDP ta zaɓi wanda zai maye gurbin Gabam

An bai wa mataimakin shugaban jam’iyya na kasa, Dr. Sadiq Umar Abubakar, damar rike shugabanci har zuwa lokacin kammala bincike.

Kara karanta wannan

2027: Tarihin shugabannin jam'iyyar hadaka ta ADA da su Atiku ke son kafawa

Kudaden da aka ce an karkatar sun hada da daruruwan miliyoyin Naira daga tallafi da kudin fom din zabe na 2023.

Sanarwar ta ce an riga an sanar da hukumar zabe ta kasa, INEC, da kuma dukkan hukumomin da ke yaki da cin hanci da rashawa.

Jam'iyyarSDP ta jaddada muhimmancin bin doka

Jam’iyyar SDP ta bukaci jama’a su sani cewa dakatarwar ta fara aiki nan take kuma ba za ta lamunci karya doka ba ko da kuwa wanda ya saba dokar ya fi kowa girma.

SDP ta jaddada cewa ita jam’iyya ce mai gaskiya, tsabta da biyayya ga doka don ceto Najeriya daga rugujewa.

Wannan yana zuwa ne a lokacin da Nasir El-Rufai yake zargin jam'iyya mai mulki da gwamnati mai-ci da kawowa 'yan adawa rikicin cikin gida.

Shugaban SDP ya bugi kirji kan zaben 2027

Mun ba ku labarin cewa jam'iyyar SDP mai adawa ta bayyana cewa ga dukkan alamu ita za ta lashe zaɓen shugaban kasa mai zuwa a shekarar 2027.

Mataimakin shugaban SDP na Arewa ta Tsakiya, Abubakar Dogara ya ce idan Allah ya yarda za su kwace mulki daga hannun Bola Tinubu.

Dogara ya yi kira ga ƴan Najeriya da su marawa SDP baya kuma su yi rijistar zama cikakkun ƴan jam'iyya a mazaɓunsu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.