An Kaure a Arewa kan Kujerar Kashim Shettima, an Roƙi Tinubu Ya Ɗauki Dogara

An Kaure a Arewa kan Kujerar Kashim Shettima, an Roƙi Tinubu Ya Ɗauki Dogara

  • Wata kungiya a Arewa maso Gabas ta bukaci a maye gurbin Sanata Kashim Shettima da Rt. Hon. Yakubu Dogara a zaben 2027
  • Kungiyar ta ce Dogara ya fi cancanta da wannan kujera saboda kwarewarsa da jajircewa, kuma za ta mika bukatar ga Bola Tinubu a Abuja
  • Sai dai wasu matasan APC a Bauchi sun soki wannan bukata, suna cewa Dogara ba dan jam’iyyar APC ba ne a hukumance

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Bauchi - Wata kungiya a Arewa maso Gabas ta roki Bola Tinubu ya yi amfani da Yakubu Dogara a madadin Kashim Shettima.

Kungiyar mai suna 'Coalition of APC Support Groups' reshen Arewa maso Gabas ta bayyana goyon bayanta ga Yakubu Dogara a matsayin mataimakin Tinubu a 2027.

An bukaci Tinubu ya maye gurbin Shettima da Dogara
An roki Tinubu ya dauki Dogara a matsayin mataimakinsa a 2027. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

An fara kiran Tinubu ya dauki Dogara mataimaki

Kara karanta wannan

Kwankwaso: An fara hasashen wanda Tinubu ke so ya maye gurbin Kashim a 2027

A wani taro da aka gudanar a Gombe ranar Litinin, ‘yan kungiyar sun bayyana Dogara a matsayin wanda ya fi dacewa da kujerar, cewar rahoton Tribune.

Kungiyar ta ce bayan taron, za su tafi Abuja domin ganawa da Tinubu tare da mika masa wannan matsaya da suka cimma.

Kungiyar ta jaddada cewa a yankin Arewa maso Gabas, babu wani ɗan siyasa da ya fi Yakubu Dogara cancanta da wannan matsayi na kasa.

“Yanzu da ake ƙoƙarin gina Najeriya mai ɗorewa bisa hadin kai da wakilci nagari, Dogara shi ne wanda ya fi cancanta."

- Cewar kungiyar

Duk da haka, Dogara bai bayyana sha’awarsa ta tsayawa takarar kowace kujera a zaben 2027 ba tukuna.

Kungiya ta nuna goyon baya a dauki Dogara mataimaki a 2027
Kungiya ta soki neman daukar Dogara a matsayin mataimakin shugaban kasa. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Kashim Shettima.
Source: Twitter

An soki kiran shugaba Tinubu ya dauki Dogara

Sai dai gamayyar kungiyoyin matasa na jam’iyyar APC a Jihar Bauchi sun soki kiran daukar Yakubu Dogara a matsayin mataimaki.

Kungiyoyin sun hada da 'APC Youth Solidarity for Tinubu/Shettima Movement' ƙarƙashin jagorancin Haske No Shaking da 'APC Youth Parliament' ƙarƙashin Alh. Kabiru G. Kobi.

Sai kuma Zauren Sarkin Arewan Bauchi Mai Rasuwa ƙarƙashin jagorancin Yariman Sarkin Arewa, wanda suka gudanar da tattaunawa dangane da siyasar 2027.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace amarya awa 2 kafin ɗaurin aurenta, sun bindige yayanta

Haske No Shaking ya fadawa wakilin Legit Hausa cewa sun nuna goyon bayansu ga Kashim Shettima a matsayin wanda zai tsaya takara da Tinubu.

Ya ce sun yi la’akari da nagarta, kishin kasa da jajircewarsa wajen haɗa kan al’umma da gina ƙasa.

Har ila yau, sun soki ra’ayoyin da wasu ke yadawa na cewa Rt. Hon. Yakubu Dogara ya dace da kujerar Mataimakin Shugaban Ƙasa a 2027.

Matasan sun bayyana cewa:

"Dogara ba dan APC ba ne, domin har yanzu ba a san lokacin da ya dawo APC ba.
"Wannan jam’iyya tana da tsari, kuma a gunduma ake shiga jam’iyya ba ta kafafen sada zumunta ko daukar lokaci kai tsaye ba."

Ana hasashen gwamnoni 4 na neman kujerar Shettima

Kun ji cewa ana rade-radin cewa APC na kokarin cire Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima daga tikitin 2027, saboda rikice-rikicen siyasa.

An ce gwamnoni hudu daga Arewa da manyan 'yan majalisa biyu suna zawarcin tikitin mataimakin shugaban kasa a jam'iyya mai mulki.

Hakan bai rasa nasaba da rikicin da aka samu a jihar Gombe yayin taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.