Matsala Ta Tunkaro Tinubu, Jarumin da Ya Mara Masa baya a 2023 zai Tsinewa Tafiyarsa
- Fitaccen jarumin Nollywood, Ganiu Nafiu ya bayyana cewa ya yi nadama matuka kan yadda ya mara wa Bola Ahmed Tinubu
- Alapini ya bayyana yadda shi da wasu jarumai suka fuskanci zagi da tsangwama saboda goyon bayan su ga Tinubu
- Sai dai ya ce duk da wahalar da suka yi, babu wani katabus da gwamnati ta iya yi masu, yayin da ake kokarin gangamin 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Fitaccen jarumin fina-finan Nollywood, Ganiu Nafiu, wanda aka fi sani da Alapini, ya bayyana nadama kan yadda ya mara wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu baya a zaben 2023.
Yanzu haka ya shiga jerin 'yan fim da suka fito fili suna nadamar mara wa Tinubu baya, ciki har da Ronke Oshodi-Oke da suka shahara a yankin Kudu.

Source: Facebook
Premium Times ta wallafa cewa dalilin da yasa wasu jaruman ke janye goyon bayansu daga gwamnatin APC shi ne matsanancin halin tattalin arziki da Najeriya ke fuskanta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaruman fim suna baya da Bola Tinubu
Punch News ta ruwaito cewa Alapini, wanda ya shahara a fina-finan Yarbawa, ya bayyana bakin cikinsa, yana mai cewa sun yi matukar jin kunya da gazawar gwamnati.
Ya koka cewa farin cikin da suka shiga da shi lokacin da suke tallata Tinubu ya koma nadama da takaici bayan an watsar da lamarinsu.
Alapini ya ce:
“Mun yi yakin neman zabe cikin farin ciki, muna tunanin mai cetonmu ne ya zo. Mun kwashe wata biyu muna yawon zabe, ba wanda ya koma gida, ba ma zuwa aiki. Amma babu abin da muka samu daga wahalar da muka yi.”
‘An yi watsi da mu,’ Jarumin fim
Alapini ya bayyana cewa yakin neman zaben ya jawo musu asara sosai ta fannoni daban-daban da suka hada da jure cin zarafi a kafafen sada zumunta da na zahiri.
Ya ce:
“Jama’a sun zage mu kamar hauka. Abokina Olaiya, wanda ya cire kaya tsirara a bakin teku saboda Tinubu, an zage shi matuka. Har yanzu ba a daina zagin ba. Kullum sai an tura masa.”

Source: Twitter
Alapini ya bayyana cewa motar da ake cewa an bashi ba daga yakin neman zaben Tinubu ba ce, daga hannun MC Oluomo aka yi masa kyautarta kafin zabe.
Da aka tambaye shi ko zai sake mara wa Tinubu baya a 2027, Alapini ya amsa da cewa:
“Ban fara tunaninsa ba tukuna. Watakila a wannan karon, goyon bayan da za mu bayar shi ne zagi da tsinuwa ga duk wanda ya kada masa kuri’a."
Shugaba Bola Tinubu zai ziyarci Binuwai
A baya, mun kawo labarin cewa Shugaban kasa, Bola Tinubu ya ce zai fasa wasu daga cikin ayyukansa na mako domin kai ziyara ta musamman ga al’ummar jihar Binuwai a ranar Laraba.
Wannan na zuwa bayan rikicin da ya yi kamari, inda ake zargin wasu yan bindiga da yiwa mutane akalla 160 kisan gilla tare da kone dukiyoyi da dama a sassan jihar ta Binuwai.
Tinubu ya bayyana alhininsa kan wadanda suka rasa rayukansu da kuma wadanda hare-haren suka shafa, kuma ya ce tuni ya bayar da umarni ga jami'an tsaro domin magance matsalar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

