Zaben 2027: Peter Obi Ya Bayyana Hanyar da Jam'iyyarsa Za Ta Bi don Yin Nasara
- Tsohon ɗan takarar ahugaban ƙasa ƙarƙashin jam'iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya bayyana cewa ba za su yi sakaci da ƙuri'un da za a kaɗa musu ba
- Peter Obi ya bayyana cewa za su tsaya su tabbatar da cewa an ƙirga ƙuri'un da aka kaɗa musu a zaɓen 2027, alamun zai yi takara
- Tsohon ɗan takarar ya kuma koka kan halin ƙaƙaniƙayi da aka jefa ƴan Najeriya, inda ya ce an maida su ƴan gudun hijira
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - 'Dan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya buƙaci magoya bayansa da su tabbatar an ƙirga ƙuri’unsu yadda ya kamata a zaɓen shekarar 2027.
Peter Obi ya ce jam’iyyarsa za ta nemo mutanen kirki domin gudanar da wannan aiki, ya gargaɗi waɗanda ke tunanin ba za a ƙirga ƙuri’un ba, cewa za a ƙirga su.

Source: Facebook
Ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi wajen ƙaddamar da wani littafi mai taken “Obi, the Political Change Agent” wanda Mr. Ike Abonyi, ya rubuta a birnin Abuja, cewar rahoton jaridar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Peter Obi ya ce da shi ne shugaban ƙasa a lokacin da aka aiwatar da cire tallafin man fetur da kuma sakin darajar Naira, farashin fetur zai kasance tsakanin N500 zuwa N600 kowanne lita, sannan Naira za ta tsaya a kusan N1000/$.
Obi ya ce zai cimma hakan ta hanyar fitar da kuɗi marasa tushe daga cikin tattalin arziƙi da kuma rushe badaƙala da laifuffuka da suka shafi tallafin fetur, rahoton jaridar Tribune ya tabbatar.
Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya kuma buƙaci ƴan Najeriya da su ci gaba da sadaukarwa.
Wane shiri Peter Obi zai yi?
“Mu ci gaba da sadaukarwa. Babu hanya ta dabara da za ta kai mu inda muke so. Idan muka nemi hanya mai sauki, ba za mu kai ga nasara ba. Za mu nemo mutane daga ko’ina, waɗanda za su shiga majalisun dokoki, majalisar wakilai."

Kara karanta wannan
"Abubuwa sun lalace," Peter Obi ya faɗi hanya 1 da ƴan Najeriya za su ƙifar da Tinubu a 2027
"Wannan ne kuskuren da muka yi a baya. Muna so mu samu mutane masu gaskiya da suka fito da niyyar yin wakilci. Idan kana son shiga siyasa ne domin samun kuɗi, to kai ma kana cikin matsalar."
“Wannan karon, za mu tabbatar mun kasance a ko’ina. Za mu kaɗa ƙuri’a, za a ƙirga su, kuma waɗanda ke tunanin ba za a ƙirga ba, mu za mu ƙirga su. Za mu tabbatar tsarin ya yi aiki.”
- Peter Obi

Source: Twitter
Peter Obi ya tausayawa ƴan Najeriya
Peter Obi ya koka kan yadda ƴan Najeriya suka koma tamkar ƴan gudun hijira a cikin ƙasarsu.
Ya ce yan Najeriya dole ne su tashi tsaye domin canza tsarin siyasar ƙasar, yana mai cewa tsarin da ke yanzu bai damu da rayuwar talaka ba.
Tsohon gwamnan ya bayyana wasu daga cikin abubuwan da ke jefa ƴan Najeriya cikin wahala irinsu rashin tsaro, talauci, sata da sauransu.
Peter Obi ya yi magana kan daina takara
A wani labarin kuma, kun ji cewa Peter Obi wanda ya yi takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, ya yi magana kan lokacin da zai daina neman mulki.

Kara karanta wannan
An shirya gangami, Ɗan Majalisar Tarayya, shugabanni da ƴan siyasa 10,000 sun koma APC
Peter Obi ya bayyana cewa akwai yiwuwar shekarar 2027, shi ne lokaci na ƙarshe da zai sake fitowa yana neman muƙami.
Ya bayyana cewa ko da ya daina neman takara, zai ci gaba da matasa masu son kawo sauyi na gaskiya shawarwari.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
