Tsohon Na Kusa da Atiku Ya Fadi Fannin da Tinubu Ya Yi Wa Abokan Hamayyarsa Zarra

Tsohon Na Kusa da Atiku Ya Fadi Fannin da Tinubu Ya Yi Wa Abokan Hamayyarsa Zarra

  • Jigo a jam'iyyar adawa ta PDP, Segun Showunmi, ya shiga cikin sahun masu kwararo yabo ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu
  • Segun Showunmi ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya yi wa abokan hamayyarsa fintinkau wajen yadda yake mu'amala da mutane
  • Jigon na PDP ya kuma musanta zargin cewa ya ci amanar tsohon ubangidansa Atiku Abubakar, saboda ya ziyarci Tinubu a Legas

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Babban ƙusa a jam'iyyar PDP, Segun Showunmi, ya kwararo yabo ga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu na APC.

Segun Showunmi ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya fi sauran abokan hamayyarsa wayau, ciki har da Peter Obi na jam'iyyar LP.

Segun Showunmi ya yabi Shugaba Tinubu
Showunmi ya ce Tinubu ya fi Peter Obi wayau Hoto: @SegunShowunmi, @DOlusegun
Source: Twitter

Segun Showunmi ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin 'Politics Today' na tashar Channels tv a ranar Lahadi, 9 ga watan Yunin 2025.

Kara karanta wannan

Bayan ganawarsa da Tinubu, tsohon gwamna ya yi maganar yiwuwar barin PDP

Showunmi ya yabi Shugaba Tinubu

Tsohon mai magana da yawun bakin ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya kuma kare kansa kan ziyarar da ya kai wa Shugaba Tinubu a Legas.

Showunmi ya bayyana cewa ziyarar da ya kai wa shugaban ƙasan, ba ita ke nuna cewa ya ci amanar alaƙar da ke tsakaninsa da Atiku Abubakar ba.

"A matsayina na babban mutum wanda ya mallaki hankalin kansa, ina da ƴancin yanke hukunci kan abin da zan yi."
"Babu wanda na ke maƙale da shi. Ni ba ni daga cikin masu adawa da Tinubu. Bakina nawa ne, kalamai na nawa ne sannan ni ne nake da alhaki kan abubuwan da na faɗa."
"Na ɗauki dogon lokaci a wannan jam'iyyar. Lokacin da kawai muke zuwa wajensu shi ne idan sun yi rashin nasara domin mu ƙarfafa musu gwiwa."
"Ka san bambancin Bola da su? Ba hanya ɗaya kawai gare shi ba wajen yin mu'amala da kowa. Nesa ba kusa ya fi su wayau. Ya fi Peter Obi wayau, ya fi su wayau su duka."

Kara karanta wannan

'Hanya 1 da 'yan adawa za su bi domin kayar da Tinubu a 2027,' inji Dele Momodu

- Segun Showunmi

Segun Showunmi ya ce bai ci amanar Atiku ba
Showunmi ya musanta cin amanar Atiku Hoto: Segun Showunmi
Source: Twitter

Showunmi ya kare kansa kan Atiku

Dangane da batun cewa ya ce amanar Atiku, Showunmi ya bayyana cewa Atiku yana jagorantar haɗaka ce wadda shi kuma bai shiga cikinta ba.

"Shin yanzu Atiku takarar shugaban ƙasa yake yi? Yana jagorantar haɗaka ce wadda kowa ya san ba na cikinta."
"Meyasa za a yi tunanin cewa ban da ƴancin yin abin da nake so, saboda me? Ka san tsawon lokacin da na kwashe kuwa a jam'iyyar?"

- Segun Showunmi

Bola Tinubu ya samu goyon baya

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan majalisar tarayya daga jihar Benue sun nuna goyon bayansu ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Ƴan majalisun waɗanda suka ƙunshi na majalisar wakilai da majalisar dattawa sun nuna gamsuwarsu kan Shugaba Tinubu ya nemi tazarce a zaɓen 2027.

Hakazalika, sun kuma yi kira ga gwamnan jihar Benue, Rabaran Hyacinth Iormem Alia da ya haɗa kai da gwamnatin tarayya domin ganin an magance matsalar rashin tsaro.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng