"Ku Bari Na Nemi Zaɓin Allah," Gwamna Ya Yi Magana kan Yiwuwar Tsayawa Takara a 2027

"Ku Bari Na Nemi Zaɓin Allah," Gwamna Ya Yi Magana kan Yiwuwar Tsayawa Takara a 2027

  • Gwamnan Abia, Alex Otti ya buƙaci magoya bayansa su ba shi lokaci ya ba Allah zaɓi kafin yanke hukunci kan batun neman zango na biyu
  • Alex Otti ya ce kamar yadda ya bar komai a hannun Allah har ya samu nasara a zaɓen 2023, haka zai sake ba Ubangiji zabi a shekarar 2027
  • Gwamnan ya jaddada cewa a yanzu gwamnatinsa ta maida hankali wajen gina ayyukan raya ƙasa da zai amfani al'ummar jihar Abia

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abia - Gwamnan Jihar Abia, Alex Otti, ya bayyana cewa zai fara ba Allah zaɓi kafin yanke hukunci kan ko zai sake tsayawa takara karo na biyu a zaben 2027.

Gwamnan na jam'iyyar LP ya bayyana hakan ne a wurin wani biki da aka shirya a Filin Wasanni na Sam Ihesiulor da ke Okpuala Ngwa.

Kara karanta wannan

'Duk mun koma mayunwata': Tsohon minista ya fadi abin da ke jiran Tinubu a 2027

Gwamna Alex Otti.
Gwamna Abia ya ce zai nemi shawarar Allah kafin sake neman takara a 2027 Hoto: Alex C. Otti
Source: Facebook

Channels tv ta rahoto cewa al’ummar Oha Isiala Ngwa daga ƙananan hukumomin Isiala Ngwa Arewa da Kudu ne suka shirya taron domin nuna goyon bayansu ga Otti.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Otti zai nemi takara a zaɓen 2027?

A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Njoku Ukoha ya fitar, Gwamna Otti ya ce kamar yadda Allah ne ya ba shi nasara a 2023, haka zai sake miƙa komai hannunSa a 2027.

"Kamar yadda muka miƙa lamarinmu ga Allah a zaɓen 2023, haka za mu sake barin komai a hannunsa a zaɓen 2027.
"Na gode da wannan goyon baya, kuma na dauke shi a matsayin yabawa nasarorin da muka cimma wa zuwa yanzu.
"Zan koma na nemi shawarar Ubangijina, nan da wani ɗan lokaci, zan fito na bayyana matakin da na ɗauka. Na san mutanena na jiran amsa.”

- Alex Otti.

Gwamnan Abia ya yi bayanin nasarorin da ya samu

Gwamna Otti ya bayyana cewa gwamnatinsa ta maida hankali sosai kan garin Aba saboda muhimmancinsa wajen bunkasa tattalin arzikin jihar Abia.

Kara karanta wannan

'Ba za su yi nasara ba': Babban malami ya hango abin da zai faru da Tinubu a 2027

“Mun fi mayar da hankali kan Aba ne saboda birnin yana samar da kudaden shiga da za su taimaka wajen zuba ayyukan ci gaba a sauran sassan jihar Abia.
"Aba babbar cibiyar kasuwancinmu ce, ba kawai a Jihar Abia ba, har ma da Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu," in ji shi.

Ayyukan da gwamnatin Abia ke yi

Gwamna Otti ya kuma jaddada kudurin gwamnatinsa na jawo kowa a jiki, inda ya ce yana iya bakin ƙoƙarinsa wajen yin ayyukan raya kasa a kowane ɓangare.

Ya bayyana cewa aikin gina titin Mgboko–Ntigha zai kammala kafin ƙarewar watan Disamba mai zuwa, kamar yadda Daily Post ta kawo.

Gwamna Otti.
Gwamnan Abia ya lissafo wasu daga cikin ayyukan da gwamnatinsa ke yi Hoto: Alex C. Otti
Source: Facebook

Dangane da batun filin jirgin sama na Abia da ke Nsulu, Otti ya bayyana cewa zaɓin wurin ya dogara ne da binciken ƙwararru, ba siyasa ba, sannan dukkan masu gonakin da abin ya shafa an biya su diyya.

Ya bayyana aikin filin jirgin sama a matsayin wani katafaren aikin raya kasa da zai haifar da ɗumbin ci gaba ga al’ummar jihar na dogon lokaci, ba wai don sufurin jirage kawai ba.

Kara karanta wannan

"Kai tsaye na gaya masa": Amaechi ya fadi abin da ya gayawa Tinubu kan zaben 2023

Gwamna Otti ya yi fatali da dakatarwar LP

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Alex Otti na jihar Abia ya yi watsi da dakatarwar da tsagin jam'iyyar LP karkashin jagorancin Julius Abure ya yi masa.

Alex Otti ya yi ikirarin cewa Abure da ƴan twagarsa sun ɗauki wannan matakin ne domin jan hankalin jama'a bayan hukuncin kotun ƙoli.

Gwamna Otti ya ce kotun koli ta riga ta yanke hukunci cewa Julius Abure ba shi ne halastaccen shugaban jam’iyyar LP ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262