Tinubu Ya Ƙara Ƙarfi, Tsohon Ɗan Takarar Shugaban Kasa Ya Haƙura da Neman Mulki a 2027
- Tsohon ɗan takarar shugaban kasa na APC, Cif Moses Ayom ya ayyana Bola Tinubu a matsayin wanda zai marawa baya a zaɓen 2027
- Ayom ya ce matakin da gwamnonin APC da ƴan Majalisar Tarayya suka ɗauka ya nuna cewa manufofin Tinubu sun samu karɓuwa a Najeriya
- Ya ce bai kamata ƴan Najeriya su kawo sabuwar gwamnati a zaɓen 2027 ba domin za ta iya dakatar da sauye-sauyen da Tinubu ya faro
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Wani jigo a jam’iyyar APC, Cif Moses Ayom, ya bayyana cikakken goyon bayansa ga tazarcen shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027.
Ayom ya amince da matakin da shugabannin APC suka ɗauka na mara wa Shugaba Tinubu baya a matsayin dan takarar shugaban kasa daya tilo na jam’iyyar a zaben 2027.

Source: Twitter
Ayom, wanda ya kasance dan takara a zaben fidda ɗan takarar shugaban kasa na APC a 2023, ya ce yana tare da Tinubu 100 bisa 100, kamar yadda Leadership ta kawo.
Ya ce goyon bayan gwamnoni 22 da ƴan Majalisar Tarayya ga Tinubu alama ce ta karbuwa da kuma tasirin sauye-sauyen da gwamnatinsa ta aiwatar a fannin tattalin arziki da jin dadin ‘yan Najeriya.
'Bola Tinubu ya cancanci tazarce a zaɓen 2027'
A wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kansa, Ayom ya ce tattalin arzikin Najeriya ya bunƙasa da kashi 3.86% a karshen 2024, mafi girma a cikin shekaru uku, kuma ana sa ran zai ƙaru a 2025.
“Shugaba Tinubu ya cancanci wa’adi na biyu domin ya ƙarisa sauye-sauyen da ya fara. Duk da cewa matakan da ya ɗauka suna da radadi a farko, Shugaban kasa yana da kyakkyawan niyya ga kasar nan,” in ji Ayom.
Ayom ya bukaci ‘yan Najeriya da shugabannin APC da su hada kai da gwamnatin Tinubu domin tabbatar da ci gaba da aiwatar da manufofin da za su canza rayuwar jama’a.
Tsohon ɗan taƙarar shugaban kasa ya haƙura
"Wannan goyon baya da manyan jiga-jigan APC ke nunawa wata karfafa gwiwa ce ga Shugaban kasa. Kuskure babba a kawo sabuwar gwamnati da za ta ta dakile wadannan muhimman manufofin tattalin arziki.”
Ayom ya kuma bukaci Bola Tinubu da ya duba yiwuwar mara wa gwamnoni masu aiki tukuru baya, musamman Gwamna Hyacinth Alia na jihar Benue, domin dorewar sauye-sauyen da yake yi a matakin jihohi.

Source: Facebook
Ya ce a cikin kasa da shekaru biyu, Gwamna Alia ya aiwatar da ayyuka da dama da suka taba rayuwar al’umma a fadin jihar Benue, rahoton This Day.
“Ina ganin Shugaban kasa na bukatar gwamnoni irinsu Alia domin manufofinsa su kai ga talakawa kai tsaye," in ji shi.
Wani jigon APC, Usman Kabir ya shaida wa Legit Hausa cewa idan ka ga Shugaba Tinubu bai yi tazarce ba to zaɓen aka fasa.
A cewarsa, matukar za a fita rumfunan zaɓe to babu tantama sai shugaban ƙasa ya doke duka ƴan adawa a karo na biyu.
Usman ya. ce:
"Ni ɗan APC sak ne, tun daga Buhari muke yin sak kuma ba zamu daina ba. Idan ka duba goyon bayan da mai girma shugaban ƙasa ke samu a kowace rana, ka san nasara ta mu ce.
"Bahaushe na cewa Juma'ar da za ta yi kyau, tun daga Laraba ake gane ta, alamu sun nuna Tinubu zai yi shekara takwas a kan mulki."
2027: Tinubu zai fuskanci ƙalubale a APC
A wani rahoton, kun ji cewa Cif Charles Udeogaranya ya bayyana aniyarsa ta neman takarar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar APC a zaɓen 2027.
Jigon ya yi watsi da matakin APC na ba Shugaba Bola Tinubu damar tazarce kai tsaye, ya ce hakan ya saɓa wa tsarin dimokuraɗiyya.
Ya koka cewa ƴan Najeriya na cikin halin talauci, yunwa da rashin tsaro wanda ya haifar da fargaba, yana mai cewa akwai buƙatar a samu canji.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


