Hasashen El Rufai Ya Tabbata, SDP Mai Kokarin Kwace Mulki Ta Shiga Matsala

Hasashen El Rufai Ya Tabbata, SDP Mai Kokarin Kwace Mulki Ta Shiga Matsala

  • Sabon rikicin cikin gida ya lullube jam'iyyar adawa ta SDP yayin da ake fafutukar kwace mulki daga gwamnatin Bola Tinubu
  • An samu bullar sabon rikicin shugabanci, inda tsagin Alfa Mohammed ya yi watsi da jagorancin Alhaji Shehu Gabam a NWC
  • An zargi wadanda suka shigo cikin SDP a baya-bayan nan da haddasa kalubalen shugabanci yayin da suke kokarin kwato mulki

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT AbujaJam’iyyar adawa ta SDP, dake yunkurin hambarar da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC, na fuskantar rikicin cikin gida mai tsanani.

Wannan na biyo bayan matakin da wani bangare daga cikin jam’iyyar ya dauka na yin watsi da shugaban jam’iyyar na kasa a karkashin, Alhaji Shehu Gabam.

Kara karanta wannan

Yadda mata suka karbi haramta bikin 'kauyawa day' a Jihar Kano

Jam'iyya
SDP ta kara fadawa matsalar shugabanci Hoto: @SDPHQ, @OfficialABAT
Source: Twitter

This Day, ta wallafa cewa wannan bangare ba wai kawai ya nesanta kansa daga Gabam ba, har ma ya soki yadda ake maye gurbin wasu daga cikin shugabannin SDP na jihohi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dama can Nasir El-Rufai ya fara hangen cewa gwamnatin Bola Tinubu za ta cinno rikici a SDP yadda ya ce ta yi a sauran jam'iyyu.

Tsohon gwamnan ya na ganin da gangan aka haifar da rigingimu a jam'iyyun hamayya da APC, LP, da NNPP domin APC tazarce.

SDP ta marawa Alfa Mohammed baya

Matakin tsagin SDP na cikin wata sanarwa da tsagin Alfa Mohammed ke jagoranta, mai taken: ‘Kawancen adawa da Tinubu’ kuma dauke da sa hannun, sakataren yada labaransa , Cif Wole Adedina.

Sanarwar da aka rabawa manema labarai a jiya, ta bayyana cewa za su ci gaba da biyayya ga Cif Wole Adedina a matsayin sabon shugaban jam’iyyar na kasa.

Kara karanta wannan

2027: An samu wanda zai buga da Tinubu, jigo zai fito takarar shugaban ƙasa a APC

Sanarwar ta ce:

“Sabuwar kwamitin zartaswa na kasa ta SDP da Cif Adedina ke jagoranta na da sahihanci, kasancewar ta samo asali ne daga kwamitin Oba Olu Falae wanda ya karbi ‘yan gudun hijira daga PDP. Sai dai bangaren da Shehu Gabam ke jagoranta na dogaro da wata takardar INEC da aka samu ba bisa ka’ida ba tun 2019, wadda har yanzu tana gaban kotu."
“Saboda haka, kwamitin zartaswa na SDP na bayyana cewa jam’iyyar ba za ta sayar ko ba haya ga kowanne rukuni ba, kuma ba za ta shiga kowanne shiri na adawa da gwamnati ba."

SDP ta caccaki shigowar sababbin ’yan siyasa

Sanarwar ta ce Alhaji Alfa Mohammed ya dora laifin rikicin SDP ke fuskanta a kan shigowar wasu ‘yan siyasa da ke cikin hadin gwiwar da ke kokarin kayar da Bola Tinubu.

Ya bayyana cewa tsarin mayar da Tinubu Legas da wasu 'yan siyasa ke da shi ba shi da wata manufa ko ingantaccen tsari na canza Najeriya ba.

Kara karanta wannan

A hukumance, gwamnan Akwa Ibom ya bayyana kudirinsa na ficewa daga jam'iyyar PDP

Nasir
SDP ta zargi sababbin masu shiga jam'iyyar da haddasa mata rikici Hoto: Nasir El Rufa'i
Source: Facebook

Ya ce:

“Kwamitin zartaswa na kasa ta SDP na nanata cewa jam’iyyar ba za ta sayar ko bada haya ga kowane rukuni ba, kuma ba za ta shiga cikin kowanne shiri na adawa da gwamnati ba, wanda babu wani bayyani na yadda za a canza Najeriya.”

Bangaren ya kuma bukaci shugabannin jam’iyyar a dukkan matakai su dakile duk wani yunkuri na kwace shugabanci daga hannunsu da sunan hadakar adawa.

Jigon SDP ya ragargaji masu komawa APC

A baya, mun wallafa cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a SDP, Adewole Adebayo, ya bayyana ra’ayinsa kan yadda ‘yan siyasa ke cigaba da sauya sheƙa zuwa APC.

Prince Adeboye ya bayyana cewa sauya shekar da ke ta faruwa a yanzu, ya zama hanya ta gane gaskiyar wadanda suke da hannu a cikin yadda aka jefa kasar nan a cikin halin ni 'ya su.

Ya kuma kalubalanci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya yi amfani da ƙwarewar sa ta siyasa wajen kyautata rayuwar al’ummar ƙasar, maimakon ya tsaya kan dabarun da suka shige.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng