El Rufai Ya Faɗi Minista 1 da Za Su Bari a Muƙaminsa bayan Sun Tura Tinubu Legas a 2027
- Malam Nasir El-Rufai ya yabawa ministan sadarwa, Bosun Tijani bisa ayyuka masu kyau da yake yi domin bunƙasa harkokin fasaha
- Tsohon gwamnan jihar Kaduna ya ce idan suka karbi mulki daga hannun Shugaba Bola Tinubu a 2027, za su bar Tijani a kan muƙaminsa
- El-Rufai ya bayyana haka ne a wani taron fasaha da ya halarta a jihar Katsina da ke Arewa maso Yammacin Najeriya a ranar Laraba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Katsina - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yaba da irin ayyukan ci gaba da ministan sadarwa, kirkire-kirkire da tattalin arzikin zamani, Bosun Tijani, ke yi.
Malam El-Rufai ya bayyana cewa za su ci gaba da aiki da Bosun Tijani bayan sun tura shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya koma Legas a zaɓen 2027.

Source: Getty Images
Tsohon gwamnan ya bayyana haka ne a wurin taron fasaha watau Arewa Tech Fest karo na biyu wanda ya gudana a jihar Katsina, kamar yadda The Cable ta kawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Taron, wanda ya shafe kwanaki uku, ya hada manyan masu zuba jari, ’yan kasuwa, kwararru a fannin fasaha da masana tsare-tsare, domin tattauna cigaban fasaha, musamman a Arewacin Najeriya.
Wane minista El-Rufai ya yaba da aikinsa?
Nasir El-Rufai ya ce Bosun Tijani zai ci gaba da rike mukaminsa idan haɗakar jam’iyyun adawa ta samu nasarar kayar da Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.
Ministan sadarwa, Bosun Tijani ne ya gabatar da jawabin bude taron a Katsina, wanda Nasir El-Rufai ya halarta.
El-Rufai, wanda ya iso wurin taron a makare, ya nemi afuwa daga mahalarta, yana mai cewa rashin zuwansa da wuri ya samo asali ne daga wani muhimmin taro da suka yi a daren Talata.
"Muna shirin tura Tinubu Legas" - El-Rufai

Kara karanta wannan
2027: Ana neman Peter Obi ya yi watsi da hadaka da Atiku, ya shiga tafiyar Tinubu
"Dole ta sa tawagar da suka shirya taron nan suka taho suka bar ni saboda jiya Talata da daddare na halarci wani muhimmin taro na haɗaka da misalin ƙarfe 8:00 na dare.
"Taron da muka yi yana da matuƙar muhimmanci saboda muna so mu tabbatar da cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya koma Legas a 2027."
- Nasir El-Rufai.

Source: Twitter
El-Rufai ya ce za su bar Bosun Tijani
Dangane da ministan kuma, El-Rufai ya bayyana cewa idan suka karɓi gwamnati, za su bar Bosun Tijani a kan mukaminsa saboda yana aiwatar da ayyuka masu kyau.
"Ko da mun kafa gwamnati, za mu bar Bosun Tijani a kujerarsa saboda yana yin aiki mai kyau," in ji El-Rufai.
El-Rufai na daya daga cikin jiga-jigan ’yan siyasar da ke fafutukar kafa haɗaka domin karbe mulki daga hannun APC a zaben 2027, rahoton Daily Post.
Nasir El-Rufai ya soki ɓangaren shari'a
A wani labarin kun ji cewa tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya caccaki ɓangaren shari'a a Najeriya.
El-Rufai ya ce yanzu mutane sun daina yarda da shari’a a Najeriya saboda jinkirin yanke hukunci da kuma zaluntar mai gaskiya ta hanyar take masa haƙƙi.
A cewarsa, lauyoyi da alƙalai sun lalace da karɓar rashawa da harkokin rashin gaskiya, yana mai cewa lokaci ya yi da za a gyara hakan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
