A Ƙarshe, Atiku, Obi, El Rufai Sun Zabi Jam'iyyar da Za Su Koma don Kayar da Tinubu

A Ƙarshe, Atiku, Obi, El Rufai Sun Zabi Jam'iyyar da Za Su Koma don Kayar da Tinubu

  • Atiku Abubakar, Peter Obi da Nasir El-Rufai sun amince da kafa hadakar adawa don tunkarar 2027 tare da komawa jam’iyyar ADC
  • Rahotanni sun nuna cewa an gudanar da wata ganawa ta manyan ‘yan siyasar uku a Abuja, suka amince suyi aiki tare a jam’iyyar ADC
  • Babachir Lawal ya ce PDP ba ta cancanci zama jam'iyyar hadaka ba saboda lalacewar da ta yi ya kai matakin da ba za a iya gyara ta ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Alhaji Atiku Abubakar (PDP), Peter Obi (LP), da Mallam Nasir El-Rufai (SDP), sun amince da kulla hadaka domin kifar da APC a 2027.

Domin cimma kudurinsu, Atiku, Obi, El-Rufai sun amince su koma ADC, wadda za ta zama jam'iyyar dukkanin 'yan adawar da ke cikin hadakar.

Kara karanta wannan

'Ta yi wa PDP, LP da NNPP': El Rufai ya bankaɗo makircin APC a siyasar Najeriya

Atiku Abubakar, Nasir El-Rufai da Peter Obi sun zabi ADC matsayin jam'iyyar hadaka
Kusoshin siyasar Najeriya: Peter Obi, Atiku Abubakar da Nasir El-Rufai. Hoto: @atiku, @elrufai, @PeterObi
Source: UGC

Atiku, Obi da El-Rufai sun zabi jam'iyyar ADC

Wani rahoto daga Arise News ya bayyana cewa waɗannan manyan ‘yan siyasa uku sun yanke shawarar ne bayan wata ganawa a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya nuna cewa ganawar Atiku, Obi da El-Rufai ta kasance ta koli, kuma an gudanar da ita a ranar Talata, wanda ya fito da kawancen da aka dade ana hasashe a hukumance.

Wata majiya mai tushe da ta tabbatar da sakamakon taron ta ce:

“Sun amince da African Democratic Congress a matsayin jam’iyyar kawancen dukkaninsu (Atiku, Obi, El-Rufai), inda za su yi aiki tare.
“Sun kammala shawarar ne daga daren jiya zuwa safiyar yau. Kamar yadda aka sani, ‘yan siyasa sukan gana da daddare yayin da jama’a ke barci.”

An kafa kwamitin kaddamar da hadakar Atiku

Majiyar ta ƙara da cewa taron ya haɗa da sauran shugabanni da masu ruwa da tsaki, inda suka kafa kwamitoci don samar da cikakken tsarin kawancen da kuma shirye-shiryen kaddamar da shi a bainar jama’a.

Kara karanta wannan

Sanatocin PDP sun gindaya sharaɗin shiga haɗakar su Atiku domin kifar da Tinubu a 2027

Atiku Abubakar, Peter Obi, da Nasir El-Rufai sun zabi ADC matsayin jam'iyyar hadakar 'yan adawa.
Atiku Abubakar ya karbi bakuncin Peter Obi a gidansa na Abuja. Hoto: @atiku
Source: Facebook
“Dukkanin shugabannin da masu ruwa da tsaki sun halarci taron. An kafa kwamitoci don kammala shirye-shiryen kaddamar da kawancen. A gaskiya, kawancen ya riga ya samu tushe mai karfi."

- A cewar majiyar.

Ko da yake ba a bayyana ranar kaddamar da jam'iyyar da shi kan shi kawancen ba tukunna, amma majiyar ta nuna cewa hakan zai faru 'nan ba da jimawa ba.'

Kafofin sada zumunta sun cika da maganganu kan wannan hadaka, yayin da wasu ke mamakin abin da ya sa ba ayi amfani da jam'iyyar PDP ko SDP ba.

Dalilin su Atiku na kin zabar jam'iyyar PDP

A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, ya tabbatar da cewa ana ci gaba da tattaunawa kan kawancen.

Da aka tambaye shi ko Atiku yana shirin komawa ADC da kuma dalilin da ya sa PDP ba ta dace da zama jam'iyyar kawancen ba, Babachir Lawal ya bayyana PDP a matsayin “gidan da ya yi lalacewar da ba za a iya gyarawa ba.”

Babachir Lawal ya ce matsalolin cikin gida da suka dabaibaye PDP sun yi tsanani matuƙa, don haka ba za ta iya zama ingantacciyar jam'iyyar kawo sauyi ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com