'Ta Yi Wa PDP, LP da NNPP': El Rufai Ya Bankaɗo Makircin APC a Siyasar Najeriya
- Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya zargi APC da shirin kawo rikici a SDP kamar yadda ta yi wa PDP da LP da kuma NNPP domin rikita su
- El-Rufai ya ce tun bayan shigarsa SDP a Maris, ‘yan Najeriya da dama sun nuna kauna da goyon baya, suna kallon jam'iyyar a matsayin mafita
- Ya kara da cewa SDP na daukar matakan hana rikici ta hanyar binciken cancantar shugabanni da tsauraran matakai wajen daukar sabbin ‘yan jam’iyya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya yi magana kan makircin da jam'iyyar APC mai mulki ke kullawa jam'iyyun adawa.
El-Rufai ya ce babu abin da APC ba za ta iya yi ba domin nakasa jam'iyyun adawa kafin zaben shekarar 2027 da suka sanya a gaba.

Kara karanta wannan
APC ta ƙara yunkurowa, shirin haɗakar Atiku, Obi da El Rufai ya gamu da babban cikas

Source: Twitter
Zargin da Nasir El-Rufai ke yi wa APC
Yayin da yake magana kan sauya shekar da ya yi, El-Rufai ya ce yawancin ‘yan Najeriya sun daina yarda da APC da PDP, cewar The Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon gwamnan wanda ya sauya sheka daga APC zuwa SDP, ya ce yana sa ran APC za ta kawo rikici a SDP.
An ji tsohon ministan na harkokin Abuja ya yi godiya matuka ga 'yan kasa bisa goyon bayansu bayan ya koma SDP.
A cewarsa:
“Ina godiya da irin tarbar da ‘yan Najeriya suka nuna tun bayan shiga ta SDP a ranar 10 ga Maris, 2025.
“Yana da kyau mu fahimta cewa yawancin mutane sun rasa ƙarfi guiwa a wurin APC da PDP, suna neman wata jam’iyya mai nagarta.”

Source: Twitter
El-Rufai ya fadi nasarar jam'iyyar SDP
El-Rufai ya danganta wannan ci gaba da tarihin jam’iyyar SDP, inda ya ce shigarsu da wasu yan siyasa cikin jam’iyyar ya kara janyo hankalin jama’a.
Game da yawaitar sababbin mambobi, El-Rufai ya ce yana sa ran APC za ta saka kwayar cuta a jam'iyyar domin haddasa rikici a cikin jam'iyyar SDP saboda son rai.
Ya ce:
“Don haka, kodayake ana shigowa jam’iyyar da yawa, muna kuma sa ran gwamnati da APC za su shigo da cutar da ke haifar da rikici.
“Kamar yadda suka taba yi a LP, NNPP da PDP, jam'iyyar SDP za ta kare kanta daga rikici."
El-Rufai ya kara da cewa SDP ta dauki matakai na bincike da kulawa wajen amincewa da sababbin shugabanni don kaucewa matsaloli a cikin jam’iyyar.
Ana zargin APC da kokarin jawo jam'iyyun adawa
Mun ba ku labarin cewa wasu rahotanni sun yi zargin APC na tuntubar gwamnoni na jam’iyyun adawa da alkawarin mukamai.
An ce jam'iyyar na yin haka ne domin ganin nasarar Bola Tinubu a 2027 cikin sauki da hadin guiwar jam'iyyun adawa.
Hakan ya zo a daidai lokacin da jam’iyyun PDP, NNPP da LP na fama da rikice-rikicen cikin gida, wanda ya haddasa sauya sheka da dama zuwa jam’iyya mai mulki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
