Gwamna Namadi Ya Jero Ƴan Majalisar Tarayya 3, Ya Sha Alwashin Kayar da Su a Zaɓen 2027

Gwamna Namadi Ya Jero Ƴan Majalisar Tarayya 3, Ya Sha Alwashin Kayar da Su a Zaɓen 2027

  • Gwamna Umar Namadi na Jigawa ya sha alwashin APC za ta karɓe dukkan kujerun ƴan Majalisar Tarayya na jihar a 2027
  • Umar Namadi ya bukaci sanatan PDP ɗaya da ƴan Majalisar Wakilai biyu su fara shirye-shiryen baro Majalisar Tarayya
  • Gwamnan ya ce yadda APC ke kara shiga lungu da saƙo ya nuna cewa jam'iyyar ba za ta bar kowace kujera ba a zaɓe na gaba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jigawa - Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, ya shawarci ‘yan majalisar tarayya na jam'iyyar PDP su fara shirye-shiryen haɗa kayansu su dawo gida a 2027.

Gwamna Umar Namadi wanda ake kira da Ɗanmodi ya sha alwashin cewa jam'iyyarsa ta APC za ta lashe duk wata kujera a jihar Jigawa a zaɓe mai zuwa.

Gwamna Umar Namadi.
Gwamma Namadi ya ce APC za ta karɓe kujerun ƴan Majalisar tarayya na PDP a Jigawa Hoto: Umar Namadi
Source: Twitter

Ɗanmodi ya bayyana haka ne a ranar Lahadi a wurin wani taron hadin gwiwa da al’umma da aka gudanar a Dutse, babban birnin jihar, kamar yadda Premium Times ta rahoto.

Kara karanta wannan

"Alkawurran kamfe," Mai martaba Sarki ya kunno wa gwamna wuta a taron jama'a

Ƴan Majalisa nawa PDP ke da su a Jigawa?

Wannan taron na baiwa jami’an gwamnati da ‘yan majalisa damar bayyana nasarorin da suka samu da kuma sauraron ra’ayoyin al’umma.

A halin yanzu, PDP na da sanata ɗaya, Mustapha Khabib mai wakiltar Jigawa ta Kudu maso Yamma a majalisar dattawa da ƴan Majalisar wakilai 2 da suka haɗa da na mazaɓar Birnin Kudu/Buji da Dutse/Kiyawa.

Har ila yau, jam'iyyar PDP na da ɗan Majalisa ɗaya tal a Majalisar dokokin jihar Jigawa.

Gwamna Namadi ya yi ikirarin cewa APC ba za ta bar kowace kujera ba a zaɓen 2027 duba da irin yadda al'umma ke kara karɓarta a faɗin Jigawa.

Gwamna Namadi ya buƙaci ƴan PDP su fara shiri

Ya ce nasarorin da ya samu a tsare-tsare da manufofin da ya zo su da suka shafi rayuwar al'umma kai tsaye sun karawa APC ƙarfi a kowane lungu da saƙo.

“Kamar yadda jama'ar Buji da Birnin Kudu suka tabbatar mana da cewa mu ke da nasara, sanatan da ke wakiltar wannan yanki a inuwar PDP ya kamata ya fara kirga kwanakinsa a majalisar dattawa.

Kara karanta wannan

"Tinubu na tsaka mai wuya," PDP ta canza lissafi kan haɗakar Atiku, Obi da El Rufai a 2027

"Haka kuma ‘yan majalisar wakilai da ke wakiltar Dutse/Kiyawa, Birnin Kudu da Buji su ma su fara kirga kwanakinsu a majalisar wakilai."
“Kamar yadda mu ke gani, yawan jama’ar da suka fito nan da goyon bayan da muka samu a Dutse ya tabbatar mana cewa APC ta samu gindin zama sosai a wannan yankin.”

- Gwamna Umar Namadi.

Umar Namadi da Badaru.
Gwamna Namadi ya yi ikirarin cewa talakawa sun kara rungumar APC a Jigawa Hoto: Umar Namadi
Source: Facebook

Gwamna Namadi ya ƙara godewa Allah

Ɗanmodi ya kara da cewa suna kara godewa Allah saboda jama’a sun karbi gwamnatinsa da hannu bibbiyu.

Ya kuma mika godiya ga jama’ar karamar hukumar Dutse bisa kyakkyawar tarba da goyon bayan da suka nuna masa, kamar yadda Leadership ta rahoto.

Aminu Saleh, wani ɗan Birnin Kudu a Jigawa ya shaidawa Legit Hausa cewa ba ya ganin gwamna ya yi laifi a maganar da ya yi duk da kowa ya san Allah ke ba da mulki.

Ya bayyana cewa shi dai a karan kansa zai sake zaɓen Ɗanmodi amma batun ɗan Majalisarsu na Tarayya kuma sai ya kara nazari a kai.

Malamin makarantar ya ce:

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya gama yanke shawara kan jam'iyyar da zai koma kafin 2027? An samu bayani

"Gwamna ɗan siyasa ne, dole ya faɗi haka a matsayinsa na ɗan APC, mutane sai surutu suke cewa wai yana neman shiga hurumin Allah kuma maganarsa ba ta sauka layi ba.
"Ni dai na san mafi yawan ƴan Jigawa za su sake zaɓen Ɗanmodi, amma ƴan Majalisar da ya ambata kuma sai mun sa su a ma'auni, mun gani."

Sule Lamido ya yi hasashen rabewar APC

A wani labarin, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya ce akwai yiwuwar jam'iyyar APC ta tarwatse nan gaba.

Sule ya yi hasashen cewa shugaban APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Ganduje da sauran jiga-jigai za su koma PDP gabanin 2027.

Tsohon gwamnan ya ce yawan bambancin ra’ayoyi tsakanin ‘yan APC ne zai haddasa rabuwar kai da tarwatsewar jam'iyyar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262