"Guguwar Tinubu": Kakakin Majalisar Dokoki da Ƴan Majalisa 21 Sun Fice daga PDP zuwa APC

"Guguwar Tinubu": Kakakin Majalisar Dokoki da Ƴan Majalisa 21 Sun Fice daga PDP zuwa APC

  • A hukumance, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Delta, Rt. Hon Emomotimi Guwor, mstaimakinsa da ƴan Majalisa 20 sun fice daga PDP
  • Hon. Guwor ne ya karanta wasikun ƴan Majalisa 21 da aka shi a zamansu na yau Talata, 6 ga watan Mayu, 2025 a birnin Asaba a Delta
  • Ya ce da wannan ci gaban, a yanzu shugabancin Majalisar ya koma hannun jam'iyyar APC da ta karbe mulki a watan da ya wuce

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Delta - Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Delta, Rt. Hon Emomotimi Guwor, tare da ’yan majalisa 21, sun sanar da sauya sheƙa daga PDP zuwa APC a hukumance.

Kakakin Majalisar da mambobi 21 sun tabbatar da ficewa daga PDP zuwa APC ne a wasikun da suka miƙawa Majalisa a zaman ranar Talata, 6 ga watan Mayu, 2025.

Kara karanta wannan

Siyasa ta dauki zafi: Kakakin majalisa da ciyamomi 17 sun fice daga PDP zuwa APC

Majalisar Dokokin Delta.
Kakakin Majalisar Dokokin Delta da ƴan majalisa 21 sun fice daga PDP zuwa APC a hukumance Hoto: @Shaibu_AO
Source: Twitter

Ƴan Majalisar Dokokin Delta sun koma APC

Jaridar The Nation ta tattaro cewa a zaman majalisar, Hon. Guwor ya bayyana cewa ya karɓi wasiku 21 daga ƴan Majalisar da suka bar PDP zuwa APC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka nan kuma shi kansa, kakakin Majalisa ya karanta tasa wasiƙar yana mai sanar da matakin da ya ɗauka na komawa jam'iyya mai mulkin ƙasar nan.

Da yake faɗin dalilansu na ficewa daga PDP, Hon Guwor ya ce sun yanke shawarar sauya sheka ne saboda rikicin shugabanci da ya hana PDP sakat a Kudu maso Kudancin Najeriya.

Har ila yau, ya ce rigingimun da suka addabi PDP a matakin ƙasa na cikin abubuwan da suka kalla suka ga ya dace su bar jam'iyyar zuwa APC.

APC ta zama mai rinjaye a Majalisar Delta

Ya ƙara da cewa da wannan ci gaba, a yanzu Majalisar Dokokin jihar Delta ta zama ta jam'iyyar APC, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Siyasa rigar 'yanci: 'Yan majalisar wakilai 8 sun sauya sheka zuwa APC, PDP

A jawabin da ya yi bayan karanta wasikun ƴan Majalisar, Guwor ya ce:

“Da wannan ci gaba da aka samu, a yanzu Majalisar Dokokin Jihar Delta ta zama ta jam'iyyar APC.”

Wannan al'amari dai ya zama mafarin ssuya akalar siyasar jihar Delta da kuma kawo ƙarshen tsawon lokacin da jam'iyyar PDP ta ɗauka tana mulki.

Majalisar Delta.
APC ta karɓe ragamar shugabanci a Majalisar Dokokin Jihar Delta Hoto: @Shaibu_OA
Source: Twitter

Shugabancin Majalisa ya koma hannun APC

Bugu da ƙari, sauya sheƙar Ƴan Majalisar ya canza akalar shugabancin Majalisar Dokokin daga hannun PDP zuwa APC.

Hakan dai na zuwa ke bayan Gwamna Sheriff Oborevwori da tsohon gwamnan da ya gada, Ifeanyi Okowa sun fice daga PDP zuwa APC.

Tun farko dai gwamnan ya sanar da cewa ya koma APC tare da dukan tsarin PDP na Delta, wanda ya ƙunshi shugannin jam'iyya a kowane mataki da ƴan Majalisar jiha da na tarayya.

Ƴan Majalisar Tarayya 6 sun koma APC

A wani labarin, kun ji cewa ƴan Majalisar Wakilan Tarayya shida daga jihar Delta sun sanar da komawa APC a hukumance.

Kara karanta wannan

Tinubu ya lalata shirin Atiku, Ƴan majalisar wakilai 6 sun fice daga PDP zuwa APC

Kakakin Majalisar, Rt. Hon. Tajudeen Abbas ne ya karanta wasiƙun ssuya sheƙar ƴan Majalisar a zaman yau Talata a Abuja.

Sun bayyana cewa sun yanke shawarar komawa APC ne saboda rikicin cikin gida da ya hana jam'iyar PDP zaman lafiya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262