Wani Ɗan Sanda Ya Durƙusa Ya Ɗaurewa Ganduje Takalmi, Bidiyo Ya Ja Hankalin Jama'a

Wani Ɗan Sanda Ya Durƙusa Ya Ɗaurewa Ganduje Takalmi, Bidiyo Ya Ja Hankalin Jama'a

  • Mutane sun yi martani kan wani bidiyo da ya nuna ɗan sandan Najeriya na ɗaurewa shugaban APC, Abdullahi Ganduje takalmi
  • Da alama faifan bidiyon wanda ya nuna ɗan sandan ya durƙusa kasa yana ɗaure wa Ganduje takalmi ya fusata wasu ƴan Najeriya
  • Wasu na ganin abin da ɗan sandan ya yi bai dace ba yayin wasu kuma suka ce wataƙila Ganduje ya taɓa taimakonsa a rayuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Wani dan sanda ya fara shan suka a kafafen sada zumunta bayan bullar wani bidiyo da ya nuna shi yana ɗaurewa shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje takalmi.

A cikin bidiyon, an ga Ganduje tsaye yayin da dan sandan da ba a gane ba ya durƙusa kan gwiwa yana daure wa tsohon gwamnan na Kano igiyar takalmi.

Kara karanta wannan

Turji ya zafafa hare-hare a Sakkwato, mazauna kauyuka 20 sun fara kaura

Ganduje.
Mutane sun yi ca kan wani ɗan sanda aka gani yana ɗaure takalmin shugaban APC, Abdullahi Ganduje takalmi Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje
Source: Twitter

Ɗan sanda ya ɗaure takalmin Ganduje

Wani mai amfani da manhajar X da aka fi sani da Twitter, Chuks ya wallafa bidiyon a shafinsa yau Litinin, 5 ga watan Mayu, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu dai sun soki dan sandan kan abin da suka kira rashin mutunta kayan aikinsa yayin da wasu suka nemi ƙarin hasken halascin jami'in tsaro ya yi haka a bakin aiki.

Galibin waɗanda suka tofa albarkacin bakinsu sun caccaki ɗan sandan, inda suka ce da wani dattijo ne ba Abdullahi Ganduje ba, ba zai masa irin haka ba.

An saba ganin 'yan sanda su na rikewa masu mulki jaka ko su zama tamkar 'yan aike a Najeriya, dabi'ar da ake ganin ba ta dace ba.

Mutane sun yi wa ɗan sandan martani

Wani mi shafin @og_cemoni ya ce:

“Shin zai iya yi wa wani dattijo mai shekaru kwatankwacin na Ganduje haka? Ya kamata ya mutunta kayan aikinsa, ba shekarun mutum ba.

Kara karanta wannan

Bugaje: Tsohon dan majalisa ya yi wa gwamnatin Tinubu wankin babban bargo

"Ba daidai ba ne dan sanda sanye da kayan aiki ya yi irin wannan aiki. Shin Ganduje ba shi da masu taimaka masa na kai-da-kai ne?”

Sai dai wasu sun kare dan sandan, suna ganin watakila Ganduje ya taimake shi a rayuwa. @ayenielijahofficial ya ce:

“Wataƙila Ganduje ya taimaka masa sosai. Akwai mutanen da za su taimake ka wanda za ka iya sadaukar da komai dominsu.”
Shugaban APC, Abdullahi Ganduje.
Yadda ɗan sanda ya durƙusa kan gwiwa ya ɗaure takalmin Ganduje ya ja hankalin masu amfani da kafafen sada zumunta Hoto: @ChuksErice
Source: Twitter

'Gwamnatin APC ta lalata ƙimar kaki'

A bangare guda, Wani Kelvin, @kelvin_kertz ya nuna takaicinsa kan yadda ake wulaƙanta jami’an tsaro a Najeriya, yana cewa:

“A Najeriya, 'yan sanda su ne masu tabbatar da doka ga oda, amma sukan zama bayi ga 'yan siyasa.”

@franknero400 kuwa ya zargi gwamnatin APC da rage kimar jami’an tsaro, yana mai cewa:

“Gwamnatin APC ta mayar da jami’an tsaro kamar bayi. Babu mutunta kayan aiki, abin kunya ne.”

Ganduje ya ce Tinubu zai gama da PDP

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya ce guguwar Tinubu za ta gama da PDP tun kafin zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

"Abin da zai rusa hadakar da Atiku ke jagoranta": Hadimim Wike

Ganduje ya bayyana cewa sauya shekar gwamnan Delta kaɗai ta nuna cewa jama'a sun gamsu da salon mulkin Bola Tinubu.

Tsohon gwamnan ya ce APC na ƙara karfi a kowace rana saboda kyawawan mnufofin mai girma shugaban ƙasa, wanda ke ƙara masa farin jini.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262