Gwamnonin PDP Sun Gamu da Matsala a Kotun Koli bayan Gwamnan Delta Ya Koma APC

Gwamnonin PDP Sun Gamu da Matsala a Kotun Koli bayan Gwamnan Delta Ya Koma APC

  • Gwamnonin APC sun gamu da cikas a ƙarar da suka shigar gaban kotun ƙoli suna ƙalubalantar ayyana dokar ta ɓaci a jihar Ribas
  • Rahotanni sun nuna cewa gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori, wanda ya koma APC kwanan nan, ya janye kan shi daga ƙarar
  • Gwamnan ya ce tun da ya bar PDP, babu dalilin da zai sa ya ci gaba da zama a ɓangaren waɗanda ke ƙalubalantar Bola Ahmed Tinubu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Wani sabon rikici ya sake tasowa a ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP kan ƙarar da ta shigar gaban kotun koli game da sa dokar ta ɓaci a Ribas.

Gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori ya janye kansa daga cikin karar da gwamnonin PDP suka kalubalanci ayyana dokar ta-baci da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi a jihar Ribas.

Kara karanta wannan

Shirin 2027: Gwamnonin PDP da Wike sun yi zama don dawo da zaman lafiya a jam’iyyar

Gwamnonin PDP.
Gwamnonin PDP Sun gamu da cikas a ƙarar da suka shigar da Tinubu gaban kotun koli Hoto: Seyi Makinde
Source: Twitter

Wannan ci gaba ya faru ne kimanin kwanaki 12 bayan Gwamna Sheriff Oborevwori, tare da dukkan jagororin PDP na Delta, sun fice daga PDP zuwa APC, rahoton Vanguard.

Gwamnan da magabacinsa, Ifeanyi Okowa da dukkan magoya bayansu sun ayyana cikakken goyon baya ga Shugaba Tinubu.

Rikicin Ribas: Gwamnonin PDP sun gamu da cikas

Jihar Delta na cikin jerin jihohin PDP 11 da suka shigar da kara mai lamba: SC/CV/329/2025 a gaban Kotun Koli, inda suka kalubalanci ayyana dokar ta ɓaci a Ribas.

Gwamnonin sun ce shugaban kasa ba shi da ikon dakatar da zababbun jami’an gwamnati na jihohi, ciki har da gwamna da mataimakinsa, sannan ya maye gurbinsu da wasu daban.

Sauran jihohin da suka shigar da wannan karar sun hada da, Adamawa, Enugu, Osun, Oyo, Bauchi, Akwa Ibom, Filato, Taraba, Zamfara da Bayelsa.

Abin da gwamnonin suke bukata daga kotu

Gwamnonin sun bukaci kotu ta masu karin haske kan ko shugaban kasa na da hurumin dakatar da gwamnoni da mataimakansu da sunan ayyana dokar ta-baci.

Kara karanta wannan

Ayyukan gwamna sun ja ra'ayin Ɗan Majalisar Tarayya, ya sauya sheƙa zuwa PDP

Haka kuma, sun kalubalanci matakin majalisar dokoki na amincewa da dokar ta-baci ba tare da kaso biyu bisa uku na ‘yan majalisa ba.

Gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori.
Gwamnonin PDP Sun gamu da cikas a ƙarar da suka shigar da Tinubu gaban kotun koli Hoto: Rt. Hon Sheriff Oborevwori
Source: Facebook

Gwamnan Delta ya janye daga ƙarar

Wata majiya daga gwamnatin jihar Delta ta tabbatar wa da jaridar cewa Gwamna Oborevwori ya umurci lauyoyinsa da su janye daga karar.

A cewar majiyar, Gwamna Oborevwori ya ce, “Tun da yanzu ni ba gwamnan PDP ba ne, babu dalilin ci gaba da kasancewa cikin wannan kara.”

Wasu rahotanni kuma na nuna cewa jihar Akwa Ibom na shirin bin sawun Delta wajen janye kanta daga karar.

Gwamnonin PDP sun yi watsi da haɗakar adawa

A wani labarin, kun ji cewa gwamnonin PDP sun nesanta kansu daga shirin haɗakar ƴan adawa, wadda tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ke jagoranta.

Wannan matsaya dai na ɗaya daga cikin abubuwan da suka cimmawa a taron gwamnonin PDP da aka gudanar a birnin Ibadan, jihar Oyo.

Shugaban ƙungiyar gwamnonin kuma gwamnan Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya ce ƙofar PDP a buɗe take ga duk wanda ke son shiga jam'iyyar amma ba za su shiga haɗaka ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262