Hadakar Atiku Ta Fara Gigita APC, An Fallasa Abin da Tinubu ke Kullawa 'Yan Adawa
- Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, ya bayyana cewa Bola Tinubu da mukarrabansa sun soma nuna damuwa
- Ya ce suna sane da yadda hadakar 'yan adawa da tsohon dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ke jagoranta ke tsorata APC
- A cewarsa, akwai ruɗani a cikin fadar shugaban ƙasa saboda irin yadda wannan haɗaka ke ƙara samun karɓuwa a fadin Najeriya
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, ya zargi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da rashin kwanciyar hankali sakamakon haɗakar ‘yan adawa.
Haɗakar adawa wacce ta samu jagorancin tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, na ƙara ƙarfafa gabanin zaɓen 2027.

Source: Facebook
Babachir Lawal ya bayyana hakan ne a cikin wata hira da ta kebanta da jaridar The Punch, inda ya ce fadar shugaban ƙasa na cikin damuwa sosai da yadda haɗakar ke karɓuwa.
Injiniya Babachir ya kuma kara da cewa Bola Ahmed Tinubu yana iya bakin ƙoƙarinsa domin tarwatsa hadakar ta hanyoyi dabam-dabam.
Ana zargin 'yan APC za su bi Atiku
Maganganun Babachir na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙara hasashen wasu 'yan siyasa, musamman daga APC na nuna rashin gamsuwa da halin da jam’iyyar ke ciki.
Hakan na zuwa ne bayan sauya sheƙa da wasu tsofaffin 'yan CPC suka yi zuwa SDP, abin da ya ƙara zafafa jita-jitar cewa jam’iyyar mai mulki na fuskantar barazanar rarrabuwa.

Source: Facebook
A sallar da ta gabata, Atiku da El-Rufai sun jagoranci wata tawaga da ta kai wa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ziyara a Kaduna, inda wasu ke kallon karfafa adawa ga Tinubu ce.
Ana zargin hadakar Atiku ta firgita APC
Ko da yake fadar shugaban ƙasa da APC na ci gaba da yin watsi da ƙarfin hadakar Atiku, Babachir Lawal ya nace cewa Tinubu da mukarrabansa suna cikin rudani da fargaba a asirce.
Ya ce:
"Tinubu ya san muna iya kayar da shi. Ko ma’aikatansa da ke da gaskiya sun san cewa ya shiga garari saboda hadakar gabanin 2027.”
Haɗakar Atiku ta gano lagon Tinubu
Babachir Lawal ya ƙara da cewa Atiku, El-Rufai da sauran ‘yan haɗaka sun san dabarun siyasar Tinubu sosai, domin sun yi aiki tare da shi a baya.
Ya ce:
“Mun taɓa zama tare a baya. Idan har mutane na cewa ni aka tura in siyo wa Tinubu fom ɗin takarar shugaban ƙasa, to wannan ya nuna muna da sanayya sosai.
Atiku da Rauf Aregbesola duk abokan siyasa ne na Tinubu a da. Mun san yadda ake lashe zaɓe a Najeriya — da kuma dabarun da ake amfani da su domin sa adawa su fadi.”

Kara karanta wannan
Bidiyon yadda Rarara ya cashe da sabuwar waƙa a liyafar da aka shiryawa Tinubu a Katsina
APC ta yi watsi da batun haɗakar Atiku
Sai dai Sakataren jam’iyyar APC na ƙasa, Sanata Ajibola Basiru, ya yi watsi da haɗakar da Atiku ke jagoranta, inda ya bayyana ta a matsayin taron 'yan siyasa da suka rasa matsayi.
Basiru ya ce:
“Babu wata haɗaka. Wannan kawai tunanin wasu mutane ne da ke jin su masu muhimmanci ne. Taron ‘yan siyasa ne da suka rasa mafaka kawai.”
Ziyarar Tinubu Katsina
Ziyarar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kai jihar Katsina kwanan nan na daga cikin matakan da yake dauka domin karfafa matsayinsa a Arewacin Najeriya gabanin zaben 2027.
Wannan yunkuri na zuwa ne a daidai lokacin da hadakar adawa da Atiku Abubakar ke jagoranta ke kara karbuwa.
Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, ya ce fadar shugaban kasa na cikin rudani, Tinubu kuma na kokarin tarwatsa wannan hadaka.
Ziyararsa Katsina na iya zama wata dabarar siyasa domin dawo da amincewar jama’ar Arewa tare da rage tasirin Atiku da El-Rufai a yankin.

Kara karanta wannan
Buhari da tsofaffin ministoci na shirin ficewa daga APC kafin 2027? Gwamna Sule ya yi magana
Hadakar Atiku ta magantu kan gwamnonin PDP
A baya, mun wallafa cewa haɗakar 'yan adawa ta zargi gwamnonin PDP da cin amanar jam’iyyar da kuma yi wa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu aiki a asirce gabanin 2027.
A cewar hadakar, gwamnonin PDP na da hannu wajen durƙusar da jam’iyyar, inda suka mamaye ragamar gudanarwa da karɓe ikon sassan jam’iyyar a matakai daban-daban.
Sun zargi gwamnonin da hana PDP fitowa a matsayin jam’iyyar adawa mai ƙarfi, suna masu cewa hakan wata dabara ce da ke taimakawa shugaba Tinubu wajen ci gaba da mulki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

