Siyasar Kano: Kwankwaso Ya Hadu da Sanata Barau Jibrin a Abuja
- Jagoran jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya hadu da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin a Abuja
- Tsohon gwamnan Kano zai samu digirin girmamawa daga Jami’ar Aliko Dangote bisa gudunmawarsa wajen kafa jami’ar da cigaban ilimi
- An yaba da hangen nesan Rabiu Musa Kwankwaso a fannin shugabanci da ci gaban kasa, musamman a wajen bunkasa ilimi da matasa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Jagoran jam’iyyar NNPP na kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya gana da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, a filin jirgin sama.
Rahotanni sun nuna cewa 'yan siyasar sun hadu ne a filin jirgin saman kasa da kasa na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

Source: Facebook
Legit ta tattaro bayanai kan lamarin ne a cikin wani sako da mai magana da yawun Kwankwaso, Saifullahi Hassan ya wallafa a X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwankwaso da Barau, duk ’yan jihar Kano ne, sai dai suna jam’iyyun siyasa mabambanta, domin Barau na jam’iyyar APC ne, yayin da Kwankwaso ke jagorantar NNPP.
Yanzu Sanatan na Arewacin Kano shi ne shugaban majalisar dattawa, Kwankwaso ya taba zama mataimakin shugaban majalisar wakilai a 1992.
Wasu hotuna da suka bayyana sun nuna lokacin da su biyun ke musabaha cikin girmamawa da dariya, alamar mutunta juna da nuna hadin kai duk da sabanin siyasa.
Jami’ar Dangote za ta karrama Kwankwaso
A wani labari na daban Jami’ar Aliko Dangote da ke Wudil, Kano, ta bayyana shirin ta na ba Sanata Kwankwaso digirin girmamawa na digirgir.
Karramawar, a cewar jami’ar, na zuwa ne a matsayin girmamawa bisa yadda Kwankwaso ya assasa jami’ar a lokacin da yake gwamnan Kano, da kuma yadda ya fifita ilimi a ayyukansa.
Kwankwaso ya kasance daya daga cikin fitattun shugabannin da suka sadaukar da kansu wajen farfado da ilimi da bai wa matasa damar karatu.
An yaba da jajircewar Kwankwaso kan ilimi
Jami’ar ta bayyana cewa ya dace a karrama Kwankwaso saboda gudunmawar da ya bayar wajen bunkasa makarantar da tallafawa dalibai a lokacin gwamnatinsa ta shekarar 2011 zuwa 2015.
Hon. Saifullahi Hassan ya wallafa a Facebook cewa jami’ar ta ce:
“Kwankwaso jagora ne mai hangen nesa, wanda ya fahimci muhimmancin ilimi ga cigaban kasa. Wannan karramawa alama ce ta godiya da yabon irin kokarinsa.”
Jama’a da dama sun tofa albarkacin bakinsu, suka roki Allah SWT ya kara masa lafiya da karin nasarori a rayuwa da shugabanci.

Source: Facebook
Ana sa ran bikin karramawar zai samu halartar manyan baki daga sassa daban-daban na kasar nan.
Baffa Bichi ya zargi Abba Kabir da badakala
A wani rahoton, kun ji cewa Dr Abdullahi Baffa Bichi ya zargi gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf da yin ba daidai ba a gwamnatinsa cikin shekara biyu.
Dr Baffa Bichi ya ce gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta yi badakala mai tarin yawa cikin shekara biyu da ta zarce matsalolin da aka samu a lokacin gwamnatin Abdullahi Ganduje.
Bichi ya fito da maganganun ne watanni bayan sallamar shi daga matsayin sakataren gwamnatin Kano da Abba Kabir Yusuf ya yi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

