Kungiyar Yarbawa Ta Faɗi Zaɓinta a 2027, Ta Yi Magana kan Gata da Buhari Ya Samu

Kungiyar Yarbawa Ta Faɗi Zaɓinta a 2027, Ta Yi Magana kan Gata da Buhari Ya Samu

  • Kungiyar Yarbawa ta Afenifere ta bayyana goyon bayanta ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu domin kammala shekaru takwas a mulki
  • A cewar Afenifere, wasu na amfani da kalmar "Gwamnatin Yarbawa" don hana Tinubu wa’adi na biyu, wanda suka ce ba gaskiya ba ne
  • Afenifere ta ce kamar yadda Muhammadu Buhari ya yi shekaru takwas ba tare da cikas ba, dole ne a bar Tinubu ya kammala duka wa'adinsa
  • Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Kungiyar Yarbawa ta Afenifere ta yi magana kan zaben shekarar 2027 da mulkin Bola Tinubu.

Kungiyar ta ce ya kamata a bar shugaban kasa Tinubu ya kammala wa’adin shekaru takwas a mulki.

Kungiyar Yarbawa ta yaba mulkin Tinubu
Kungiyar Afenifere ta ce yana goyon bayan Tinubu a zaɓen 2027. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Kungiyar Yarbawa ta fusata da sukar Tinubu

A cikin wata sanarwa da ta fitar, sakataren shirye-shiryenta na kasa, Abagun Kole Omololu ya ce Tinubu ya hau mulki ne bisa zabin ‘yan Najeriya, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

Rivers: An 'kunyata' matar shugaba Tinubu yayin gagarumin taro, mata sun yi bore

Afenifere ta ce wasu mutane na tayar da jijiyar wuya ta kabilanci ta hanyar kiran gwamnatin Tinubu da “Gwamnatin Yarbawa” domin hana shi wa’adi na biyu.

Omololu ya ce babu wata “kungiyar kabilu” da ta hada kai don hana tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi shekaru takwas.

A cewarsa:

"A bayyana, ba tare da wani ruɗani ba, gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ba Gwamnatin Yarbawa ba ce, Gwamnatin Najeriya ce.
“Bai hau kujerar shugabanci ba saboda gadon kabilanci, sai dai sakamakon kuri’un da ‘yan Najeriya daga kowane yanki suka kada da imani da shi.
Yarbawa sun nuna goyon baya ga Tinubu a 2027
Kungiyar Yarbawa ta bukaci ba Tinubu damar yin wa'adi 2 kamar Buhari. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

'Ba a yiwa Buhari haka ba' - Kungiyar Yarbawa

Kungiyar ta kuma kalubalanci yan Najeriya game da yadda tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi mulki lami lafiya.

Ta ce babu wani wanda ya danganta shi a kabilar Fulani kamar yadda yanzu ake yi Bola Tinubu, cewar The Guardian.

Kara karanta wannan

'Gari ya yi zafi,' Tsohon Sanata ya fadi halin da ake ciki bayan barin majalisa

Ta ce:

“Muna tunatar da kasa: Lokacin da Muhammadu Buhari ya yi shekaru takwas a ofis, babu wanda ya kira mulkinsa da gwamnatin Fulani.
“Babu wata kungiya ta kabilu da ta bayyana don hana shi wa’adi na biyu saboda kabilarsa, an bar shi kuma an ba shi dama ya kammala wa’adinsa.
"Dole ne adalci da ci gaba su kasance a kowane lokaci. Kada wani ya nemi adalci ne kawai idan ya shafi kansa.
"Shugaba Tinubu zai yi cikakken wa’adin shekaru takwas, bisa son al’ummar kasar nan da kuma tsarin kundin tsarin mulki, akasin haka hatsari ne ga kasa.”

Tinubu ya yi sauye-sauye a ma'aikatun tarayya

A wani labarin, kun ji cewa shugaban kasa, Bola Tinubu ya sauya wa wasu manyan sakatarori hudu ma'aikatu domin karfafa aikin gwamnatin tarayya.

Wata sanarwa daga ofishin shugabar ma’aikata ta ce matakin ya yi daidai da manufar 'Renewed Hope Agenda' na gwamnatin Bola Tinubu a Najeriya.

An ce za a kammala dukkanin sauye-sauye da mika aiki a ma'aikatun tarayyar kafin yau Juma'a 2 ga Mayun 2025, kamar yadda shugaban kasa ya umarta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.