Buhari da Tsofaffin Ministoci na Shirin Ficewa daga APC Kafin 2027? Gwamna Sule Ya Yi Magana

Buhari da Tsofaffin Ministoci na Shirin Ficewa daga APC Kafin 2027? Gwamna Sule Ya Yi Magana

  • Gwamna Abdullahi Sule ya ƙaryata jita-jitar da ake yaɗawa cewa Buhari, da tsofaffin ministocinsa ƴan tsagin CPC na shirin barin APC
  • Sule ya ce tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, Abubakar Malami da sauran tsofaffin ƴaƴan APC na nan daram a jam'iyya mai mulki
  • Gwamnan ya ce mutum akalla 20 sun nuna sha'awar neman kujerarsa a zaɓen 2027 amma ba shi da wanda ya zaɓa ya zama magajinsa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Nasarawa - Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule, ya musanta rade-radin da ke yawo cewa tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, tsofaffin ministocinsa da wasu ƙusoshin APC na shirin barin APC kafin 2027.

Gwamna Sule ya bayyana cewa yana ƙwarin gwiwar cewa Buhari, tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami, da sauran jiga-jigai na tsagin CPC ba za su bar APC ba.

Kara karanta wannan

An kori manyan ma'aikata daga aiki da Gwamnatin Tinubu ta fara sauye sauye a NNPCL

Gwamna Abdullahi Sule.
Gwamna Sule ya musanta raɗe-raɗin da ake cewa Buhari da tsofaffin ministocinsa za su bar APC Hoto: Abdullahi A. Sule Mandate
Source: Facebook

Vanguard ta ce Abdullahi Sule ya faɗi haka ne yau Juma’a a wani taron karrama sakataren gwamnan Nasarawa, Labaran Magaji a birnin Lafiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƙungiyar shugabannin kananan hukumomi (ALGON) ce ta shirya taron domin karrama sakataren gwamnatin jihar, Labaran Magaji.

Buhari da tsofaffin ministoci za su bar APC?

A cewarsa, maganar cewa tsofaffin ‘yan CPC na shirin ficewa daga APC saboda zargin maida su saniyar ware a gwamnatin Bola Tinubu ba gaskiya ba ce.

“Baba Buhari shi ne CPC. Idan ya ce CPC tana tare da kai, to babu makawa tana tare da kai. Idan kuma ya ce ba ta tare da kai, to ba ta tare da kai.
"Yana da kuri’un mutane miliyan 12 da ke biye da shi, kuma ni na san bai da niyyar barin APC.”

- Abdullahi Sule.

Gwamna Sule na zargin wasu da raba kan APC

Gwamna Sule ya kara da cewa ya na zargin wasu ne ke yunkurin raba kan jiga-jigan APC ta hanyar janye su daga jam'iyyar, amma hakan ba zai yi nasara ba.

Kara karanta wannan

Bayan kalaman Okowa, Atiku ya yi magana kan ficewa daga PDP

Sule ya ce:

"Suna kokarin dauke Malami, amma bari in fada muku, Malami ba zai je ko’ina ba. Mun je wajen Buhari kwanan nan a Kaduna, muka ce masa Baba ba za ka je ko’ina ba. Malami kana nan tare da mu.”
Malami da Buhari.
Buhari da Abubakar Malami na nan daram a APC Hoto: Muhammadu Buhari
Source: Facebook

Wa zai gaji gwamnan Nasarawa a 2027?

Da yake magana kan zaɓen 2027, Gwamna Sule ya bayyana cewa har yanzu bai zaɓi kowa a matsayin magajinsa ba, yana mai cewa Allah ne kadai ya san wanda zai gaje shi.

"Yanzu haka, akwai ‘yan takara guda 20 da ke zawarcin kujerar gwamnan Nasarawa a 2027. Amma ni ban zaɓi kowa ba, Allah ne zai zaba," in ji Sule.

Arewa za ta sake marawa Tinubu baya a 2027

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Abdullahi Sule ya ce ƴan Arewa za su sake marawa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu baya karo na biyu a 2027.

Gwamnan ya ce Arewa za ta ci gaba da mutunta yarjejeniyar da aka kulla ta karba-karba tsakanin Arewa da Kudancin kasar nan.

Abdullahi Sule ya kara da cewa, kamar yadda Arewa ta yi aiki tukuru wajen nasarar Tinubu a zaben 2023, haka za ta sake yi domin ya yi tazarce a 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262