2027: A ƙarshe, LP Ta Faɗi Matsayarta kan Shirin Haɗaka, Za Ta Binciki Gwamna

2027: A ƙarshe, LP Ta Faɗi Matsayarta kan Shirin Haɗaka, Za Ta Binciki Gwamna

  • Jam’iyyar LP ta ce ba za ta shiga kowace irin kawance ba kafin zaben 2027, Julius Abure mai ikirarin shugabanci ya fadi haka
  • Abure ya bayyana cewa maimakon kawance, za su mayar da hankali ne wajen sake gina jam’iyyar da fadada mambobinta a 2027
  • LP ta kafa kwamitin ladabtarwa don bincikar Gwamna Alex Otti da wasu, bisa kalamansa da ake ganin sun zagi jam’iyyar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Tsagin jam'iyyar LP ya yi magana kan jita-jitar shiga haɗaka da sauran jam'iyyu.

Tsagin da ke karkashin Julius Abure ya ce ba zai shiga haɗaka ko hadin gwiwa ba kafin babban zaben 2027.

LP ta yi watsi da maganar haɗaka a zaben 2027
Jam'iyyar LP ta ce babu abin da zai sanya ta a hadakar da ake shirin yi. Hoto: Peter Obi, Asiwaju Bola Tinubu, Atiku Abubakar.
Source: Facebook

Matsayar LP kan shirin haɗaka a 2027

Wannan na daga cikin abubuwa 12 da aka cimma a taron kwamitin zartarwa (NEC) na jam’iyyar da aka yi a Abuja, da shafin LP ya wallafa a X.

Kara karanta wannan

'SDP za ta wawushe manyan 'yan siyasa,' El-Rufa'i ya yiwa jam'iyyarsa albishir

Da yake karanta sanarwar, shugaban tsagin jam'iyyar LP na kasa, Julius Abure, ya bayyana cewa ba za su shiga kowace irin kawance ba kafin zaben 2027.

Sanarwar ta ce:

“Jam’iyyar LP ba za ta shiga kowace kawance ba kafin babban zaben 2027, maimakon haka, za mu mayar da hankali wajen sake gina jam’iyyar, tsara sababbin dabaru, sasanci da mambobi.”

Ya bayyana shakku kan tattaunawar kawance da ke faruwa, yana cewa wadanda ke jagoranta ba su da kwarewa ko halin da ya dace.

“Mutanen da ba za su iya hada jam’iyyarsu ba, ba za su iya hada kawancen kasa ba.
“Gina sabuwar jam’iyya da ke bukatar a mika tsarinta na bukatar shugabanci mai karfi, wanda yanzu babu shi."

- Cewar sanarwar

Abure ya fadi matsayar jam'iyyar LP kan haɗaka
Jam'iyyar LP ta yi magana kan haɗaka a zaben 2027. Hoto: @NgLabour.
Source: Twitter

Jam'iyyar LP za ta binciki gwamna Alex Otti

Abure ya ce kwamitin NEC ya yi nazari kan abin da ta kira sabawa da doka da Gwamna Alex Otti na Abia da wasu suka aikata.

Kara karanta wannan

ACF: Dattawan Arewa sun gindaya sharadin goyon bayan 'dan takara a zaben 2027

A cewarsa, NEC ta kafa kwamitin ladabtarwa don bincike da bayar da rahoto cikin makonni biyu.

Abure ya ce an dauki matakin ne bayan kalaman Gwamna Otti a talabijin da suka zargi jam’iyyar LP.

Mambobin kwamitin sun hada da: shugaban kwamitin, Ayo Olorunfemi; sakatare, Umar Farouk, Edun, Manuga da Ihejiagwa da sauransu.

Ya kara da cewa:

“NEC na taya Cif George Moghalu murna tare da bukatar hadin kan ’yan jam’iyya da mutanen Anambra don nasara a zaben Nuwamba 8.”
“Za mu tsayar da ’yan takarar da ke mutunta kundin tsarin jam’iyya da ka’idoji. Muna kokarin kaucewa matsalolin da muke fuskanta a Abia.”

An fadi shirin Atiku da Obi a 2027

Kun ji cewa wani na kusa da Atiku Abubakar ya ce tattaunawar sirri tsakanin abokinsa da Peter Obi domin hada karfi su fitar da Bola Tinubu daga ofis.

Majiyar ta ce Atiku da Obi sun fahimci cewa hadin guiwa ce kadai mafita don cimma nasarar shugabanci nagari tare da ceto Najeriya.

Wasu na zargin Shugaba Tinubu da kokarin raba kawunan 'yan Arewa da na Kudu domin samun rinjayen kuri'un 'yan kasa a zaben shekarar 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.