Bayan Korar Shi, Baffa Bichi Ya Ce Abba Ya fi Ganduje Barna a Gwamnatin Jihar Kano
- Dr Abdullahi Baffa Bichi ya ce gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta fi gwamnatin Abdullahi Ganduje tafka barna da almundahana
- Dakta Bichi ya ce yana da hujjoji da za su fallasa ayyukan barna da gwamnatin yanzu ke aikatawa cikin kasa da shekaru biyu
- A nata bangaren, gwamnatin Kano ta mayar da martani, tana cewa babu kamshin gaskiya a zarge-zargen da Baffa Bichi ya yi
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Sakataren gwamnatin Kano da aka sauke, Dr Abdullahi Baffa Bichi, ya zargi Abba Kabir Yusuf da babakere.
Tsohon sakataren gwamnatin ya bayyana cewa gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf na NNPP na tafiyar da mulki cikin barna da ya fi na gwamnatin da ta gabata.

Kara karanta wannan
Uwar Bari: Fubara zai kara zama da Wike a shirin sulhu a Rivers, APC da PDP sun magantu

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Dr Baffa Bichi, ya yi maganar ne kwanaki kadan bayan ficewar shi daga jam’iyyar NNPP zuwa APC.
A cewarsa, abubuwan da ake zargin Abdullahi Ganduje da aikatawa a tsawon shekara takwas, gwamnatin yanzu ta ninka su cikin shekara biyu kacal.
Bichi ya zargi gwamnatin Abba da barna
Baffa Bichi ya ce duk da abin da aka zargi Ganduje da shi a shekara takwas, gwamnatin Abba ta ninka su sau 10 cikin shekara biyu.
Trust Radio ya rahoto cewa Abdullahi Baffa Bichi ya kara da cewa da kyar gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta kai labari a zaben 2027 mai zuwa.
Ya yi nuni da cewa akwai yawaitar koke daga jama’a dangane da yadda ake tafiyar da al’amuran gwamnati, kuma hakan na iya haddasa juyin siyasa kafin zuwan zaben gaba.
Bichi ya ce yana shirin jagorantar kokarin fallasa barnar gwamnatin Abba, yana mai nuna cewa lokacin da za a yi gyara a siyasar jihar Kano ya kusa.
Komawar Dr. Baffa Bichi zuwa jam'iyyar APC
A makonnin da suka gabata, Dr Bichi da wasu mutum 14 sun sauya sheka zuwa jam’iyyar APC inda aka tarbe su hannu bibbiyu a matakin jiha da na ƙasa.
An sallami Bichi a sakataren gwamnati bisa dalilin rashin lafiya, amma mutane da dama sun bayyana shakku da cewa hakan na da alaka da rikicinsa da Abba Kabir da Rabiu Kwankwaso.
Baya ga haka, Jam’iyyar NNPP a Kano ta dakatar da shi tare da wani kwamishina bisa zargin rashin biyayya.
Gwamnatin Abba ta yi wa Bichi martani
Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na Jihar Kano, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya musanta zarge-zargen da Bichi ya yi, yana mai cewa babu hujjar hakan.

Source: Facebook
Wannan zargin ya kara ƙara rikita siyasar Kano, musamman yayin da ake shirin tunkarar zaben 2027 a Najeriya.
Kwankwaso ya karbi 'yan APC zuwa NNPP
A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya karbi masu sauya sheka daga APC zuwa jam'iyyar NNPP a Abuja.
Rahotanni sun tabbatar da cewa mutanen da suka sauya sheka daga APC sun fito ne daga kananan hukumomi daban daban na Kano.
Bayan karbar masu sauya shekar, Sanata Rabiu Kwankwaso ya gana da jakadan tarayyar Turai a gidansa da ke birnin tarayya Abuja.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

