"Ku Kwantar da Hankalinku," Gwamna Adeleke Ya Yi Maganar batun Ficewa daga PDP

"Ku Kwantar da Hankalinku," Gwamna Adeleke Ya Yi Maganar batun Ficewa daga PDP

  • Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke ya jaddada cewa yana nan daram a PDP kuma ba shi da wani shiri na sauya sheƙa zuwa APC
  • Adeleke ya bayyana hakan ne a wurin taron masu ruwa da tsakin PDP na Osun wanda ya gudana a gidan gwamnatin jihar dake Osogbo
  • Shugabanni da sauran ƙusoshin PDP sun yi farin ciki da kalaman gwamnan tare da tabbatar masa cewa za su mara masa baya ya yi tazarce

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Osun - Gwamnan Osun, Ademola Adeleke, ya tabbatar wa da shugabannin PDP a jihar cewa ba shi da wani shiri na barin jam’iyyar ya koma APC mai mulki.

Gwamna Adeleke ya tabbatarwa dukkan masu ruwa da tsaki da shugabannin jam'iyyar cewa yana nan daram a PDP kuma zai nemi zango na biyu a zaɓen Osun na 2026.

Kara karanta wannan

'Saura kiris': Gwamna ya tabbatar da shirin komawa APC bayan jita jitar barin PDP

Gwamna Adeleke.
Gwamna Adeleke ya musanta raɗe-raɗin cewa yana shirin komawa APC Hoto: @Aadeleke_01
Source: Twitter

Daily Trust ta ruwaito cewa hakan na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Olawale Rasheed, ya fitar a ranar Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa gwamnan ya faɗi haka ne wani taron masu ruwa da tsakin PDP da ya jagoranta a gidan gwamnatinsa ranar Laraba da daddare.

Gwamna Adeleke na shirin barin PDP?

A wajen taron wanda shugaban PDP na Osun, Sunday Bisi, ya halarra, Gwamna Adeleke ya karyata jita-jitar cewa yana shirin sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.

“Mutanena, dattawan jam’iyya da shugabanni, ina tabbatar muku a yau cewa ba zan sauya sheka zuwa APC ko wata jam’iyya ba. Ina nan daram a PDP, ku yi watsi da duk wata jita-jita,” in ji Adeleke.

Taron ya samu halartar manyan ƙusoshin PDP da suka hada da dan majalisar amintattu (BoT), Sanata Olu Alabi da tsohon Sakataren Jam’iyya na Kasa, Farfesa Wale Oladipo.

Haƙa zalika tsohon Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Lasun Yusuf, da Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Osun, Wale Egbedun, da jiga-jigai da dama sun halarci zaman.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta yi babban kamu ana tsaka da batun sauya sheƙar gwamnan Delta

Shugabannin PDP sun yabawa Adeleke

Masu ruwa da tsakin jam’iyyar sun amince da shugabancin gwamnan wanda suka kira da na adalci, hangen nesa da aiki tuƙuru.

Bugu da ƙari, sun ayyana cikakken goyon bayansu ga shirin Gwamna Adeleke na sake neman mulkin Osun a karo na biyu, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Gwamna Adeleke.
Gwamnan Osun ya fara samun goyon bayan neman tazarce a zaɓen 2026 Hoto: Ademola Adeleke
Source: UGC

Shugabannin PDP sun kuma yi murna da Gwamna Adeleke ya tabbatar masu da cewa ba shi da shirin sauya sheƙa, sannan sun yaba da ayyukan alherin da yake yi wa al'umma.

Har ila yau, sun yaba da jajircewar shugabannin jam’iyya na yankin Oriade/Obokun da suka ci gaba da zama a PDP duk da ficewar wani mutum guda da suka kira “marar godiya”.

An ba gwamnan Osun shawara kan 2027

A wani labarin, kun ji cewa ƙungiyar manyan Osun watau OLT ta buƙaci Gwamna Ademola Adeleke ya yi zamansa a jam'iyyar PDP, ka da ya kuskura ya koma APC.

Sai dai kungiyar ta shawarci Adeleke ya marawa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu baya idan ya nemi tazarce a zaɓen 2027.

Shugaban OLT, Adesola Adigun ne ya ba gwamnan wannan shawara a wata sanarwa da ya fitar kan jita-jitar da ake yaɗawa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262