Ayyukan Gwamna Sun Ja Ra'ayin Ɗan Majalisar Tarayya, Ya Sauya Sheƙa Zuwa PDP

Ayyukan Gwamna Sun Ja Ra'ayin Ɗan Majalisar Tarayya, Ya Sauya Sheƙa Zuwa PDP

  • Jam'iyyar PDP ta samu ƙarin ɗan Majalisar Wakilan Tarayya a daidai lokacin da take takaicin rasa gwamnan Delta da ya koma APC
  • Hon. Dennis Agbo, mai wakiltar mazaɓar Igbo Eze ta Arewa/Udenu a Majalisar Dokoki ta ƙasa ya sauya sheka daga LP zuwa PDP
  • Ya bayyana cewa ayyukan ci gaba da Gwamna Peter Mbah ke aiwatarwa a jihar Enugu na cikin dalilansa na komawa jam'iyyar PDP

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Enugu - Dan Majalisar Wakilan Tarayya, Hon. Dennis Agbo, ya fice daga jam’iyyar LP zuwa PDP mai mulki a jihar Enugu.

Agbo, wanda aka fi sani da “Mr. Integrity," shi ne mamba mai wakiltar mazaɓar Igbo-Eze ta Arewa/Udenu ta jihar Enugu a Majalisar Wakilan Tarayya.

Hon. Dennis Agbo.
Dan Majalisar Tarayya daga jihar Enugu ya fice daga LP zuwa jam'iyyar PDP Hoto: Onyekachi C Ugwu
Source: Facebook

Ɗan majalisar wanda ke wa’adi biyu, ya bayyana cewa rikicin cikin gida da ya dabaibaye jam'iyyar LP na cikin dalilansa na sauya sheƙa, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Saƙon APC ga gwamnan PDP bayan ya fara shinshinar shiga jam'iyyar

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me yasa Ɗan Majalisar ya koma PDP?

Hon. Agbo ya ce dalilansa na shiga PDP sun hada da ayyukan alherin Gwamna Peter Mbah na Enugu, rikicin cikin gida a LP da kuma matsin lamba daga al’ummar mazabarsa.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, ɗan Majalisar ya ce:

“Ayyukan da Gwamnan Jihar Enugu, Mai Girma Dr. Peter Ndubisi Mbah ke yi tun bayan rantsar da shi abin alfahari ne matuka."

Agbo zai haɗa kai da Gwamna Mbah a PDP

Ya kara da cewa sauya sheƙarsa zuwa jam'iyyar PDP za ta kara ba shi cikakkiyar damar tallafawa gwamnatin Gwamna Mbah wajen ciyar da Enugu gaba.

Agbo ya bayyana cewa ba zai iya jure rikicin da ke cikin LP, kuma akwai bukatar daidaiton siyasa da gwamnatin jihar domin amfanin al’ummarsa.

“Saboda girmama ra’ayin jama’ar mazabar Igbo-Eze ta Arewa/Udenu, na yanke shawarar ficewa daga LP domin komawa PDP,” in ji shi.

Kara karanta wannan

"Ba za ta tsira ba": Tsohon kakakin PDP ya hango babbar musibar da ke tunkaro APC

Ya ce aiki da gwamnan a inuwa daya ta siyasa zai bada damar samun hadin gwiwa da kawo ci gaba a mazabarsa da sauran sassan jihar Enugu.

Peter Mbah.
Jam'iyyar PDP ta samu ƙarin Ɗan Majalisar Tarayya Hoto: Peter Mbah
Source: Twitter

PDP ta shirya taron karɓar Ɗan Majalisar

An ruwaito cewa za a gudanar da taron komawar ɗan Majalisar jam’iyyar PDP a hukumance ranar Alhamis, 1 ga Mayu, 2025, a hedkwatar PDP da ke GRA, Enugu.

A baya, Agbo ya wakilci mazabarsa a Majalisar Wakilai ta 8 (2015–2019) karkashin jam’iyyar PDP.

An sake zabensa a 2023 a karkashin LP, amma kotu ta soke zabensa tare da umarnin sake kada kuri’a a wasu rumfunan zabe, Vanguard ta ruwaito.

Ko da yake dan takarar PDP ya sha rantsuwa na dan lokaci, Agbo ya kalubalanci sakamakon kuma ya dawo da kujerarsa a shekarar 2024.

Jiga-jigan LP 2 sun koma PDP a Enugu

A wani labarin, kun ji cewa mai magana da yawun LP a jihar Enugu, Titus Odo, tare da tsohon kwamishina sun sauya sheka zuwa PDP a ranar Laraba.

Sun bayyana cewa sun baro LP zuwa PDP ne domin ba da gudunmuwarsu a ƙoƙarin da Gwamna Peter Mbah ke yi na kawo sauyi a jihar Enugu.

Shugaban PDP na Enugu, Dakta Martin Chukwunwike, wanda ya karɓe su hannu bibbiyu ya ce sun yi farin ciki da manyan ƴan siyasar suka dawo gidansu na usuli.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262