Dele Momodu Ya Fito da Bayani kan Rade Radin Komawar Atiku APC

Dele Momodu Ya Fito da Bayani kan Rade Radin Komawar Atiku APC

  • Dele Momodu ya ce sauya sheka da Ifeanyi Okowa ya yi daga PDP zuwa APC ba don jama'a ba ne, sai don son kai da neman dama
  • 'Dan siyasar ya bayyana cewa siyasar Najeriya ta lalace, ya kara da cewa babu kishin kasa ko akida, sai neman kudi da mukami kawai
  • Cif Momodu ya karyata jita-jitar cewa Atiku Abubakar zai koma APC, yana mai cewa Atiku ba dan siyasar da ke cikin rudani ba ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Jigo a jam’iyyar PDP, Dele Momodu, ya soki matakin da tsohon gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, ya dauka na komawa APC.

Dele Momodu ya bayyana cewa hakan wani yunkuri ne na son kai da nuna gazawa a siyasar Najeriya.

Kara karanta wannan

A karshe, Ahmad Isa na Brekete Family ya yi magana, ya caccaki Tinubu

Dele Momodu
Momodu ya ce Atiku ba zai sauya sheka ba. Hoto: Dele Momodu
Source: Facebook

A tattaunawar da gidan talabijin na Arise ya yi da shi, Momodu ya bayyana cewa matakin Okowa ba ya da alaka da hidima ga jama’a, sai dai yana nuni da rashin da’a da rashin akida a siyasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Momodu ya ce Okowa ya rike mukamai da dama a PDP, ciki har da gwamna, Sanata, da sakataren gwamnati, sannan kuma aka ba shi damar zama mataimakin dan takarar shugaban kasa.

Momodu: "Okowa bai da dalilin sauya sheka"

Tsohon 'dan jaridar ya bayyana cewa ganin Okowa yana kokarin kare sauya shekar da ya yi, ya kara nuna cewa babu wata hujja mai karfi da ta sanya shi daukar matakin.

'Dan siyasar ya ce:

“A matsayina na dan dimokradiyya, ba na hana mutum sauya sheka, amma dole ne a fadi gaskiya.
"Wannan mataki na Okowa babu abin da ya haifar sai kunya da ci baya ga siyasar Najeriya,”

Kara karanta wannan

'Saura kiris': Gwamna ya tabbatar da shirin komawa APC bayan jita jitar barin PDP

Ya kara da cewa siyasar Najeriya yanzu ta koma neman riba kawai, ba wai kishin kasa ko akida ba:

“Mutane na sauya sheka ba don kishin kasa ba, sai don bukatar kansu,”
Momodu
Momodu ya zargi Okawa da rashin akida a siyasa. Hoto: Dele Momodu
Source: Twitter

Momodu ya karyata cewa Atiku zai koma APC

Dangane da jita-jitar cewa Atiku zai koma APC, Momodu ya ce hakan ba zai taba yiwuwa ba, yana mai cewa Atiku dan siyasa ne na hakika kuma ba ya neman mulki ta kowane hali.

Dele Momodu ya kara da cewa:

“Atiku bai taba zama dan siyasar da ke neman mulki ta kowace hanya ba. Ya ce mani siyasa ta gaji faduwa, idan ka ci nasara lafiya, idan ka fadi sai ka koma ka sake shiri,”

Momodu ya ce Atiku mutum ne da ke kauracewa tashin hankali da amfani da ‘yan daba:

“Shi ne mutumin da idan ka je gidansa ba za ka ga ‘yan daba ba,”

- Dele Momodu

Momodu ya nuna rashin jin dadinsa da yadda shugaban rikon kwarya, Umar Damagum, ke tafiyar da jam’iyyar, yana mai cewa da a ce ana da kishin kasa, da tuni an kori Nyesom Wike a PDP.

Kara karanta wannan

El-Rufa'i ya gano wanda ya fi dacewa ya mulki Najeriya a 2027

Legit ta tattauna da Adamu Ali

Wani dan jam'iyyar APC a jihar Gombe, Adamu Ali ya bayyana cewa za su yi maraba da Atiku idan da zai dawo APC.

Adamu Ali ya ce:

"Dama ai ya taba shiga APC, saboda haka idan ya dawo ma, ya dawo gida ne."
"Yanzu yayin fita ake daga PDP, ya kamata shi ma ya fita kafin a gama watsewa,"

El-Rufa'i ya yi magana kan hadaka da PDP

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya ce ba za su yi hadaka da jam'iyyar PDP ba.

El-Rufa'i wanda ya koma SDP kwanan nan ya ce dama tun asali ba su da niyyar hadaka da PDP saboda rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar.

Tsohon gwamnan ya kara da cewa a yanzu haka suna kokarin hada kan jama'a ne domin samar da dandalin siyasa da za su samu goyon bayan 'yan kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng