Gwamnan Kebbi da Gwamnoni 4 Za Su Bar APC, Su Shiga Hadakar Atiku? An Ji Gaskiya
- An samu ruɗani a APC ta Kebbi bayan jita-jitar cewa Gwamna Nasiru Idris da wasu gwamnoni na shirin sauya sheƙa zuwa PDP
- Gwamna Idris ya musanta jita-jitar barin APC, inda ya bayyana cewa zai kasance a cikin APC har sai ya ga abin da ya ture wa buzu nadi
- Duk da cewa APC ce mai mulki a Kebbi, amma PDP na da tasiri sosai a jihar, dukkan sanatocin jihar na karkashin jam’iyyar adawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kebbi - An samu ruɗani a jam’iyyar APC mai mulki a jihar Kebbi bayan yaɗuwar jita-jitar cewa Gwamna Nasiru Idris na shirin sauya sheƙa zuwa PDP kafin zaɓen 2027.
Wani rahoto da ya karade kafafen sada zumunta ya zargi Idris da wasu gwamnoni huɗu na APC da shirin haɗa kai da Atiku Abubakar don kayar da Tinubu a 2027.

Source: Facebook
Gwamnan Kebbi ya karya rahoton barin APC
Sai dai, Gwamnan Kebbi, Dr. Nasir Idris, ya musanta wannan jita-jita, yana mai cewa "labarin na cike da rashin kunya," kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, Gwamna Idris ya ce rahotannin "ba su da tushe," yana bayyana su a matsayin "ruwayoyin sojojin bakan 'yan siyasa."
Da yake mayar da martani ga zargin haɗin gwiwa da Atiku, gamnan jihar Kebbi ya tabbatar da biyayyarsa ga APC, yana mai cewa cewa, "APC ta yi ni, a cikin APC, kuma don APC."
Gwamnan ya ƙara da cewa:
"Ba ni da wani dalili na sauya sheƙa. Ni zan kasance mutum na ƙarshe da zai bar wannan jam'iyya mai ƙarfi da nagarta."
"Ina nan daram a APC" - Gwamnan Kebbi
Gwamna Idris mai rike da sarautar Kauran Gwandu, ya jaddada cewa ya himmatu wajen cika alkawurran APC ga al’ummar Kebbi da tallafa wa manufofin gwamnatin Bola Tinubu.
Jaridar Vanguard ta rahoto gwamnan Kebbi yana cewa:
"Idan wani ya sake faɗa muku Kauran Gwandu zai bar APC, ku fada masa cewa Kaura ne mutum daya tilo da zai zai tsaya a APC komai wuya."
Sanarwar da jami’in yaɗa labaransa, Ahmed Idris, ya fitar, ta nanata cewa Kebbi na nan daram cikin APC, kuma jita-jitar da ake yadawa aikin ‘yan siyasa marasa hankali ne.
Idris ya tabbatar wa jama’ar Kebbi cewa yana da cikakken ƙuduri na ci gaba da ayyukan raya jihar karkashin tutar jam'iyyar APC.

Source: Facebook
Jam'iyyar PDP na da karfi a jihar Kebbi
Duk da cewa jam'iyyar APC ce me mulki a Kebbi, amma an lura da cewa PDP tana da ƙarfi a jihar, inda dukkanin sanatoci uku na jihar ke karkashin jam’iyyar.
Sanatocin Kebbi atau Adamu Aliero (Kebbi ta Arewa), Yahaya Abdullahi (Kebbi ta Tsakiya) da Garba Musa Maidoki (Kebbi ta Kudu), duk ‘yan PDP ne.
Ko da yake Sanata Aliero ya koma PDP, tasirinsa a siyasa bai gushe ba, kuma ana ganin yana da tasiri wajen fitar da dan takara mai nasara a zaɓen jihar.
Gwamnan Yobe ya karyata shiga hadakar Atiku
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, ya bayyana cewa ba zai shiga kawancen siyasa da Atiku Abubakar ke jagoranta ba.
Daraktan yaɗa labaransa, Mamman Mohammed, ya musanta zargin, yana mai cewa Buni babban jigo ne a APC, kuma gudunmuwarsa ga jam’iyyar tabbatacciya ce.
Mohammed ya ƙara da cewa masu yaɗa irin wannan jita-jita na mafarkin mallakar irin ƙwarewar siyasar Buni, amma hakan ya tsaya a mafarki kawai.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


