Yadda 'Yan Siyasar Najeriya Ke Rububin Sauya Jam'iyya Gabanin Zaben 2027
Tsakanin Janairu da Maris din 2025, Najeriya ta fuskanci gagarumin sauyin jam’iyyu da ya shafi manyan 'yan siyasa, ciki har da Mallam Nasir El-Rufai.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Wadannan sauye-sauyen sun nuna yadda harkar siyasa a Najeriya ke canzawa, inda ‘yan siyasa ke neman sababbin jam’iyyu da suka dace da manufofinsu.

Asali: Twitter
Wannan rahoto ya jero fitattun 'yan siyasa da suka sauya sheka a farkon watanni uku na 2025 da kuma tasirinsu ga siyasar Najeriya.
'Yan siyasar da suka sauya sheka zuwa APC
1. Engr. Yusuf Buhari
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Engr. Yusuf Buhari, wanda ya tsaya takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar SDP a 2023, ya koma APC a cikin watan Maris, 2025, inji rahoton Daily Trust.
Shi da Bala Mohammed Gwagwarwa da wasu jiga-jigan SDP sun koma APC a lokaci guda a Kano. Wannan sauyin sheka ya kara wa APC karfi a Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan
Sanatocin Arewa sun haɗa kai, sun taso da ƙarfi kan abin da aka yi wa ƴan Arewa a Edo
Masana siyasa na ganin cewa wannan mataki babbar koma baya ce ga tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, wanda kwanan nan ya shiga jam’iyyar gabannin zaɓen 2027.
Yayin da yake jawabi ga masu sauya sheka, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa ya ce ficewar manyan jiga-jigan SDP na nuna cewa shirin amfani da jam’iyyar wajen kalubalantar APC a 2027 ya mutu tun kafin ya fara.
2. Bala Mohammed Gwagwarwa
Mun ruwaito cewa, Bala Mohammed Gwagwarwa ya sauya sheka daga SDP zuwa APC a lokaci guda da Engr. Yusuf Buhari.
Gwagwarwa ya tsaya takarar gwamnan jihar Kano karkashin jam'iyyar SDP a zaben 2023, wanda ake ganin komawarsa APC zai rage tasirin SDP a Kano.
Tsohon dan takarar gwamna a Kano, Bala Muhammad Gwagwarwa, ya ce sun yanke shawarar komawa APC saboda bajintar Shugaba Tinubu cikin kusan shekaru biyu.
3. Sanata Ned Nwoko
A watan Fabrairu 2025, Sanata Ned Nwoko ya fice daga PDP zuwa jam'iyyar APC, yana mai cewa rikicin cikin gida ne ya sa shi sauya sheka.

Kara karanta wannan
Kungiyar Izalah ta yi maganar kisan ƴan Arewa a Edo, ta fadi hanyar dakile lamarin
A cewarsa dan majalisar dattawan, PDP tana fama da matsalolin shugabanci da rashin jituwa tsakanin jagororinta, wanda hakan ya sa ba zai iya ci gaba da zama ba.
Sauya shekarsa zuwa APC na nufin jam’iyyar na kara karfi a Delta, inda PDP take da tasiri kuma ana ganin wannan mataki na iya rage wa PDP karfin da take da shi a jihar.
4. Sanata Shehu Sani
Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya koma APC a Fabrairun 2025 bayan zaman sa na wani lokaci a cikin jam'iyyar PDP.
Shehu Sani ya ce gwamnan Kaduna, Uba Sani ne ya yi sanadin komawarsa jam’iyyar mai mulki bayan tattaunawar sulhu da aka yi a fadin jihar.
Dan gwagwarmayar ya jaddada cewa shi ne daya daga cikin wadanda suka kafa APC a Kaduna kuma ya taka rawa wajen gina tsare-tsaren jam’iyyar a jihar.
Sani ya kuma bayyana cewa ya samu sabani da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, kan bambance-bambancen siyasa da na kashin kai, wanda ya sanya shi shiga PDP.
5. Mukhtar Ramalan Yero
Tsohon gwamnan Kaduna, Mukhtar Ramalan Yero, ya shiga jam'iyyar APC acikin watan Fabrairun 2025 bayan ficewarsa daga PDP.
Yero ya ce:
“Tun ranar da muka sanar da ficewar mu daga PDP, jam’iyyu da dama sun tuntube mu, ciki har da APC mai mulki. Mun hadu da su kuma mun tattauna tun daga ranar da muka bar tsohuwar jam’iyyarmu.
"Don haka, daga yau, 12 ga Fabrairu, 2024, ni da wakilan wasu abokan siyasa mun yanke shawarar komawa APC.
"Bayan wannan matsaya, mun gana da gwamnan jiha kuma mun yi tattaunawa da shi. Mun shaida masa cewa mun yarda da shiga jam’iyyar bisa gayyatar da aka yi mana.”
6. Hon. Jallo Hussaini Mohammed
Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Igabi, jihar Kaduna, Hon. Jallo Hussaini Mohammed, ya koma APC daga PDP a Maris din 2025, kamar yadda muka ruwaito.
Ya bayyana cewa rikice-rikicen cikin gida ne suka sa shi barin PDP zuwa APC, matakin da zai kara wa APC karfi a Kaduna, musamman a yankin da yake wakilta.
Hakan ya nuna yadda PDP ke rasa manyan ‘yan siyasa sakamakon matsalolinta na cikin gida yayin da ya ce zai kawo wa 'yan mazabarsa ayyukan ci gaba a karkashin APC.
7. Hon. Adamu Tanko
Hon. Adamu Tanko ya bar jam'iyyar PDP zuwa APC a 2025, yana mai cewa jam’iyyar ta kasa magance matsalolinta na cikin gida.
Dan majalisar wakilai, mai wakiltar mazabar, Gurara/Suleja/Tafa, a jihar Neja na daga cikin 'yan siyasan da suka koma APC saboda rikicin shugabanci a PDP.
Ana ganin sauya shekar dan majalisar zai kara wa APC karfi a jihar Neja gabanin babban zaben 2027. Sannan, ya kara fito da matsalolin PDP a fili.
8. Hon. Salisu Garba Koko
Hon. Salisu Garba Koko ya shiga jam'iyyar APC ne a watan Fabrairu 2025 saboda rikicin da ya dabaibaye PDP, kamar yadda ya ambata a sanarwar murabus dinsa.
Dan majalisar, mai wakiltar mazabar Besse/Maiyama, daga jihar Kebbi, ya karawa jam'iyyar APC karfi a jihar, da ke fama da rikice-rikicen siyasa.

Kara karanta wannan
'Tsofaffin ministoci da sanatoci sun shiga SDP don kifar da Tinubu a 2027,' Gabam
Ficewar Salisu Koko na zuwa ne jim kadan bayan awanni 24 da wani dan jam’iyyar daga jihar Kaduna, Amos Gwamna Magaji, ya bar babbar jam’iyyar adawa bisa irin dalilinsa.
9. Hon. Amos Gwamna Magaji
Dan majalisa Zangon Kataf/Jaba, Kaduna a majalisar wakilai, Hon. Amos Gwamna Magaji ya koma APC daga PDP a Fabrairu 2025, yana mai cewa jam’iyyar PDP na fama da matsalolin cikin gida.
Mun ruwaito cewa, Magaji ya bayyana rikice-rikicen da ke ci gaba da addabar PDP a matakin kasa da na jiha a matsayin babban dalilin ficewarsa daga jam’iyyar.
Ya gode wa APC bisa kyakkyawar tarba da suka masa tare da jaddada aniyarsa ta yin hidima mafi kyau ga mazabarsa karkashin sabuwar jam’iyyarsa.
Dan majalisar, wanda ke wa’adi na biyu a Majalisar Wakilai, shi ne Shugaban Kwamitin Kula da Ayyukan Lafiya da kuma jagoran ‘yan majalisar Kaduna.
'Yan siyasar da suka sauya sheka zuwa SDP

Kara karanta wannan
Kaduna: Sarki ya samu shirgegen muƙamin gwamnati, Gwamna Uba Sani ya taya shi murna
Ita ma jam'iyyar SDP ta samu wasu manyan ‘yan siyasa da suka fice daga APC da wasu jam'iyya suka shiga cikinta saboda wasu dalilai.
1. Mallam Nasir Nasir El-Rufai
Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya fice daga APC zuwa SDP a cikin watan Maris 2025 saboda rashin gamsuwa da shugabancin jam’iyyar.
Ya bayyana cewa APC ta kauce daga akidarta ta asali, lamarin da ya haifar da cece-kuce a siyasar Najeriya, inda ake ganin zai kara wa SDP karfi.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Malam El-Rufai ya ce abubuwan da suka faru cikin shekaru biyu da suka gabata sun tabbatar da cewa wadanda ke jagorantar APC a halin yanzu ba su da niyyar gane, ballantana magance matsalolin jam’iyyar.
El-Rufai, wanda kuma ya taba zama ministan Abuja, ya ce ya sha bayyana damuwarsa a sirrance, har ta kai ga kwanan nan ya na magana a fili game da tafarkin da APC ke bi wanda bai dace ba.
2. Obinna Simon (MC Tagwaye)
Fitaccen dan wasan barkwanci, Obinna Simon, da aka fi sani a masana’antar nishadi da suna MC Tagwaye, ya koma jam’iyyar SDP.
Mun ruwaito cewa, Tagwaye, kamar yadda aka fi saninsa, memba ne na tawagar yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC a zaben 2023.
Ya koma SDP tare da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, wanda shima ya fice daga APC zuwa jam’iyyar.
A cewarsa, rashin tsarin sakayya ga jajurtattun mambobin, shugabanci na tsofaffi, da manufofin da ke jefa talakawa cikin kunci suka kawo karshen zamansa a APC.
3. Ahmed Babba Kaita
Ahmed Babba Kaita, tsohon sanatan da ya wakilci mazabar Katsina ta Arewa, ya fice daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar SDP.
Kaita, wanda ya wakilci mazabar tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya sauya sheka daga APC zuwa PDP a baya, kafin shiga SDP.
Sanata Kaita ya taba bayyana rikice-rikicen cikin gida da rashin adalci a APC a matsayin dalilan ficewarsa daga jam’iyyar.
A wata sanarwa mai surkulle da ya fitar a shafinsa na Facebook, Sanata Ahmad Babba Kaita, ya wallafa hoton doki, alamar jam'iyyar SDP, 'yan awanni bayan komawar El-Rufai jam'iyyar.
4. Sanata Suleiman Nazif
Mun ruwaito cewa, Suleiman Nazif, tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na kasa, ya yi murabus daga jam’iyyar, kamar yadda muka ruwaito.
Nazif, tsohon sanata mai wakiltar Bauchi ta Arewa, ya sanar da komawarsa SDP a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, 28 ga Maris, 2025.
Ya ce ya yanke shawarar sauya sheka ne bayan shawarwari masu yawa da kuma bukatar mutanen da yake mutuntawa a tafiyarsa ta siyasa.
Nazif ya ce ya koma SDP ne domin kafa dandalin siyasa mai karfi da ke kiyaye dimokuradiyya tare da inganta tsarin zaben shugabanni a Najeriya.
Ya wadannan sauye-sauyen za su shafi zaben 2027?
Sauye-sauyen jam’iyyu daga Janairu zuwa Maris 2025 sun canza akalar siyasar Najeriya, inda APC ta fi amfana da wannan guguwar sauyin.
Duk da haka, SDP na kara samun tagomashi daga wadanda suka gaji da APC.
Yayin da zaben 2027 ke karatowa, ana sa ran karin sauye-sauye, don haka jam’iyyu dole su daidaita matsalolinsu domin su kasance masu karfi a siyasa.
Mai sharhi kan siyasa, Alhaji Hassan Mato Katsina, ya ce kowanne dan siyasa na sauya sheka ne domin muradun kansa, sabanin ikirarin da wasu 'yan siyasar ke yi.
Alhaj Hassan ya ce:
"Su wadanda ake wakilata ko ake shugabanta, ba ruwansu da jam'iyyar da dan siyasa ya fito, ma damar zai yi masu aiki, za su zabe shi, ka ga, sauya shekar da suke yi, amfanin kashin kansu ce.
"Babbar matsalar ita ce, ta yadda sauya jam'iyyar ke ba wasu bata garin 'yan siyasa kariya. Mun sha ganin yadda ake yafe laifin 'yan siyasa idan sun koma jam'iyya mai mulki.
"Sannan, jam'iyya ta koma wani takobi na yakar 'yan adawa, idan har ba ka tare da jam'iyya kaza, to kai mutumin banza ne a wajensu.
"Lallai dole ne 'yan Najeriya su gane cewa, sauya jam'iyya ba shi ke wanke laifi, ko gane adalin shugaba ba, don haka a yi zaben cancanta a 2027 ba wai zaben jam'iyya ba."
Da gaske Atiku ya koma SDP?
A wani labarin, mun ruwaito cewa, hadimin tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya musanta rade-radin cewa tsohon dan takarar shugaban kasa ya sauya sheka.
Jita-jitar ta fara yaduwa ne yayin da ake hasashen yiwuwar hadewar Atiku da wasu ‘yan takarar shugaban kasa da suka fafata a zaben 2023.
Sai dai wani hadiminsa ya sake nanata cewa batun sauya sheka ba gaskiya ba ne, yana mai bayyana shi a matsayin shaci fadi da ke nufin karkatar da hankalin jama’a.
Asali: Legit.ng