El Rufai Ya Yi Kamu: Babban Ƙusa a Jam'iyyar PDP kuma Tsohon Sanata Ya Koma SDP

El Rufai Ya Yi Kamu: Babban Ƙusa a Jam'iyyar PDP kuma Tsohon Sanata Ya Koma SDP

  • Tsohon mataimakin shugaban PDP, Sanata Suleiman Mohammed Nazif ya sauya sheka daga jam'iyyar zuwa SDP tare da magoya bayansa
  • Sanata Nazif ya ce ya sauya sheka zuwa jam'iyyar SDP ne bayan shawarwari da amincewar al'ummar da suke kallonsa a matsayin wakili
  • SDP ta yi maraba da Sanata Nazif, tana mai cewa kwarewarsa da tasirinsa za su taimaka wajen kara karfin jam’iyyar a matakin kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Bauchi - Sanata Suleiman Mohammed Nazif, tsohon mataimakin shugaban PDP, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar SDP tare da magoya bayansa da abokan siyasa.

Sauya shekar Sanata Suleiman Nazif na nuni da sabon babi a siyasar sa, yayin da yake kokarin samar da shugabanci na gari ga al’ummar da ya taba wakilta.

Tsohon sanatan Bauchi ya fice daga jam'iyyar PDP zuwa SDP
Tsohon shugaban PDP na kasa, Sanata Nazif ya sauya sheka zuwa SDP. Hoto: Shehu Musa Gabam
Asali: Facebook

Sanata Nazif ya fice daga jam'iyyar PDP

Kara karanta wannan

Siyasa kenan: Bayan kare El Rufai a baya, shugabar matan APC ta dawo caccakarsa

Bayan dogon nazari da shawarwari, da kuma amincewa da bukatar sauyin daga mabiyansa, Sanata Nazif ya sanar da murabus dinsa daga jam’iyyar PDP, inji rahoton The Cable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce Sanata Nazif ya dauki wannan matakin ne domin tabbatar da aniyarsa ta yi wa al’umma hidima fiye da bukatun siyasa na kashin kansa.

Sanata Nazif ya rike manyan mukamai a PDP, ciki har da mamba a kwamitin zartarwar jam'iyyar (NEC) da kwamitin amintattu (BOT).

Ana yi wa Sanata Nazif kallon gwarzon siyasa mai kishin kasa, wanda ke fafutukar ganin ci gaban Najeriya da samar da kyakkyawan shugabanci.

Dalilin Sanata Nazif na shiga jam'iyyar SDP

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, 28 ga Maris din 2025, Sanata Nazif ya bayyana sauya shekarsa daga PDP zuwa jam’iyyar SDP.

“Na dauki wannan mataki ne bayan shawarwari da tuntubar mutane da dama, tare da la’akari da ra’ayin al’ummar da nake wakilta,” inji Sanata Nazif.

Kara karanta wannan

'Tsofaffin ministoci da sanatoci sun shiga SDP don kifar da Tinubu a 2027,' Gabam

Ya kara da cewa:

“Kishina ga dimokuradiyya da ci gaban kasa yana nan bai gushe ba. Ina fatan zan yi aiki domin samar da tsarin shugabanci na gari a cikin jam'iyyar SDP.”

An ce sauya shekar Sanata Nazif na zuwa ne yayin da PDP ke fuskantar ficewar kusoshinta zuwa wasu jam’iyyu sakamakon rikicin da ya dabaibaye ta.

SDP ta yi maraba da Sanata Nazif

Jam’iyyar SDP ta yi maraba da Sanata Nazif, tana mai cewa zuwansa zai karfafa kokarinta na gina jam’iyyar masu kishin kasa.

Shugaban SDP na kasa, Shehu Musam Gabam, a shafinsa na Facebook, ya jaddada cewa kwarewa da tasirin Sanata Nazif za su taimaka wajen ciyar da jam’iyyar gaba.

Jam’iyyar ta bukaci ‘yan Najeriya masu kishin gaskiya da adalci su shiga SDP domin tallafa wa yunƙurinta na samar da sauyi mai ma’ana a Najeriya.

Kara karanta wannan

Malamin Musulunci ya gano hanya, ya jagoranci 'yan PDP da APC zuwa SDP

Sanarwar shugaban SDP ta ce:

"Ina farin cikin tarbar Sanata Suleiman Mohammed Nazif da jajirtattun mabiyansa zuwa jam’iyyar mu ta SDP.
"Sanata Nazif bai zo shi kaɗai a wannan tafiya ba, ya zo tare da magoya bayansa, abokan siyasa, dauke da sakonnin tarin mutanen da ke neman sabon shugabanci a Najeriya."

Karanta sanarwar Shehu Gabam a nan kasa:

'Yan takarar gwamna sun sauya sheka zuwa SDP

A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsofaffin ‘yan takarar gwamna a jam’iyyar PRP a zaben 2023 da ya gabata sun bi sahun Nasir El-Rufai, inda suka koma SDP.

Rahotanni sun nuna cewa tun bayan sauya shekar Mallam El-Rufai daga APC zuwa SDP, jam’iyyar na samun karin mambobi a sassa daban-daban na Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng