Matasan PDP sun bayyana wanda su ke son a nada mataimakin shugaban jam'iyya na kasa

Matasan PDP sun bayyana wanda su ke son a nada mataimakin shugaban jam'iyya na kasa

- Matasan jam'iyyar PDP sun bukaci jam'iyyarsu da ta cike gurbin mataimakin shugaban jam'iyyar na kasa

- Sun zabi Sanata Nazif ne daga jihar Bauchi sakamakon jajircewarsa da biyayyarsa ga jam'iyyar

- Sun bayyana tarihin aiki tukuru na sanatan a duk matsayin da ya rike a baya, hakan kuwa na nuna cewa zai kai jam'iyyar ga wani mataki mai girma idan aka zabe shi

Matasan jam'iyyar PDP sun bukaci jam'iyyarsu da ta cike gurbin mataimakin shugaban jam'iyyar na kasa da wani jigon jam'iyyar daga jihar Bauchi, Sanata Suleiman Nazif.

Gurbin ya kasance ne tun bayan canza sheka da sanata Babayo Gamawa yayi zuwa jam'iyyar APC.

DUBA WANNAN: Shari'ar Buhari da Atiku: Tambuwal ya yi tsokaci kan hukuncin da kotun koli ta yanke

Matsayar matasan na kunshe a takardar da Ambasada Bala Aboki da Babagana Ishaq Maliya suka sa hannu.

Kungiyar ta kwatanta Sanata Nazif da dan jam'iyya mai matukar biyayya da aiki tukuru.

Sun bayyana cewa, idan aka zabeshi a matsayin mataimakin shugaban jam'iyyar na kasa, za a samu nasarar a kowanne mataki na jam'iyyar.

"Sanata Nazif jigo ne a siyasa, aboki ne kuma mai kare matasa. Ya bar tarihin da ba zai gogu ba a duk matsayin da ya rike a baya kuma magoyin bayan cigaban jam'iyyar PDP ne," in ji kungiyar.

Kungiyar ta yi kira ga duk sassan jam'iyyar ta kasa da su goyi bayan Nazif. Sun kuma yi kira ga shuwagabannin jam'iyyar da su hanzarta yin duk tarurrukan da suka dace da zasu tabbatar da matsayin ga sanata Nazif.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel