‘Yan siyasan Arewa 10 da ke kan gaba wajen neman kujerar shugaban Jam’iyyar PDP
- A watan nan ne Jam’iyyar PDP za ta zabi sababbin shugabanninta na kasa
- Da alamun David Mark, Ahmad Makarfi da Farfesa Jerry Gana su gwabza
- Watakila tsofaffin Gwamnoni irinsu Sule Lamido da Shema su shiga takara
Abuja- An fara buga siyasa domin ganin an zabi sabon shugaban jam’iyyar PDP na kasa. This Day tace jiga-jigan Arewa na kokarin fitar da ‘dan takara daya.
Tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark da tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido sune ‘yan gaba-gaban wajen rike jam’iyyar adawar.
Jaridar tace Olusegun Obasanjo yana tare da Sule, shi kuma Mark ya samu goyon baya ne daga irinsu Janar Aliyu Gusau da wasu tsofaffin sojoji ‘Yan Arewa.
Daga cikin wadanda ake tunani suna sha’awar samun mukamin akwai tsofaffin gwamnoni; Muazu Babangida Aliyu, Ibrahim Dankwambo da Ibrahim Shema.
Aliyu, Dankwambo da Shema sun yi mulki a jihohinsu na Neja, Gombe da Katsina. Barista Shema ne kadai a cikinsu ya fito daga bangaren Arewa maso yamma.
Ana tunanin Mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Sanata Suleiman Nazif yana kwallafa rai a kujerar. Haka zalika Dr. Iyorchia Ayu, da Farfesa Jerry Gana.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Gwamnan Benuwai, Samuel Ortom shi ne yake kokarin ganin kujerar ta fada hannun Iyorchia Ayu, wanda ya taba zama shugaban majalisar dattawa na kasa.
Wani wanda ake tunani za a gwabza da shi wajen zama shugaban jam’iyyar ta PDP shi ne tsohon gwamnan jihar Kaduna, Sanata Ahmad Muhammad Makarfi.
A ranar Lahadi, 10 ga watan Oktoba, 2021, Legit.ng Hausa samu labari cewa Dino Melaye zai nemi mukamin, ganin cewa za a fito da shugaban PDP ne daga Arewa.
Akwai yiwuwar yayin da aka fara saida fam a yanzu, a ji cewa masu neman kujerar sun kara yawa.
Ga jerin ‘yan takarar nan:
1. Sanata David Mark
2. Alhaji Sule Lamido
3. Dr. Muazu Babangida Aliyu
4. Ibrahim Hassan Dankwambo
5. Ibrahim Shehu Shema.
6. Sanata Suleiman Nazif
7. Dr. Iyorchia Ayu,
8. Farfesa Jerry Gana.
9. Ahmad Makarfi
10. Dino Melaye
Dazu ne muka ji cewa jam'iyyar APC mai mulki ta lashe baki ɗaya kujerun da aka yi takara kansu a zaɓen kananan hukumomi na jihar Filato da aka gudanar.
Hukumar zaɓe ta PLASIEC, ta ce APC ta lashe kujerun shugabannin hukumomi 17 da kansiloli 235.
Asali: Legit.ng