Sanata Nazif ya ce babu makawa sai PDP ta kwato kujarar Shugaban kasa a 2023

Sanata Nazif ya ce babu makawa sai PDP ta kwato kujarar Shugaban kasa a 2023

Mataimakin Shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na kasa a arewa, Sanata Suleiman Muhammad Nazif, ya bayyana cewa jam’iyyar za ta kwato kujerar shugaban kasa sannan ta lashe mafi rinjaye na jihohin arewa a zaben 2023.

Nazif ya ce gwamnatin APC mai mulki ta ba yan Najeriya kunya da tsarin shugabancinta a kasar, don haka sun yanke shawarar tsige jam’iyyar a zabe mai zuwa.

Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 23 ga watan Janairu a wani sakon taya murna zuwa ga gwamnonin Adama, Ahmadu Fintiri; Taraba, Ishaku Darius; Bauchi, Sanata Bala Mohammed; Benue, Samuel Ortom da Sokoto, Aminu Tambuwal wadanda suka yi nasarar a shari’an kwanan nan da kotun koli ta yanke.

Ya ce koda dai an yiwa jam’iyyar fashin nasarorinta a zaben da ya gabata, ta yi nasarar kwato wasu jihohi da ta rasa a 2015.

Sanatan ya kuma bayar da tabbacin cewa PDP za ta kawo karin jihohi daga arewa a karkashin jagorancinsa a 2023, inda ya bukaci yan Najeriya da su yi Imani da jam’iyyar sannan su yi aiki ya hadin kai da cigaban ta.

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga na kashe mutanena a kullun ba tare da gwamnati ta dauki mataki ba – Sanata Sani Musa

Da ya ke korafi kan faduwar jam’iyyar a jihohin Gombe, Plateau da Kano a zaben 2019, ya yi kira ga dukkanin magoya bayan jam’iyyar da su ajiye banbanci sannan su yi aiki don hadin kai da ingancin jam’iyyar domin kawo sauyi a kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel