Atiku, El Rufai, Obi da Jiga Jigan APC Sun Hadu domin Shirin Kifar da Tinubu a 2027
- Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da wasu jiga-jigan APC sun kafa kawance saboda rusa shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027
- Peter Obi na jam’iyyar LP ya samu wakilcin jigo a jam'iyyar, Yunusa Tanko, yayin da Nasir El-Rufai da Babachir Lawal suka halarci taron a Abuja
- Tsohon gwamna, Kayode Fayemi da Rotimi Amaechi da kuma Abdullahi Adamu ba su halarta ba, amma sun tura saƙon uzuri ga mahalarta taron
- Taron na nuna sabuwar haɗin gwiwar ‘yan siyasa masu shirin kalubalantar mulkin Tinubu a zaɓe mai zuwa nan da shekara kusan biyu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Manyan jiga-jigan siyasa a Najeriya sun sake haduwa a Abuja domin shirin kwace mulkin Bola Tinubu a 2027.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da wasu jiga-jigan jam’iyyar APC sun kafa kawance da nufin kalubalantar Shugaba Tinubu a 2027.

Asali: Twitter
2027: Jiga-jigai sun hadu da Atiku a Abuja
Daga cikin mahalarta taron akwai tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai wanda ya koma SDP a kwanakin nan, cewar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sauran shugabannin adawa da ke wajen taron sun haɗa da ɗan takarar shugaban ƙasa na LP 2023, Peter Obi wanda Yunusa Tanko ya wakilta.
Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, da tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, da wasu shugabanni duk sun halarci taron.
Mutanen Buhari ba su samu zuwa taron ba
Wadanda ba su samu damar zuwa ba amma suka ba da haƙuri sun haɗa da tsohon gwamnan jihar Rivers, Rotimi Amaechi.
Sai tsohon gwamnan Ekiti, Dr. Kayode Fayemi da kuma tsohon shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Adamu daga jihar Nasarawa.

Asali: Twitter
Menene Atiku ya ce kan haɗaka a 2027?
Lokacin da aka tambayi Atiku ko taron na nufin fara hadaka domin kifar da Tinubu a 2027, tsohon mataimakin shugaban ya kada baki ya ce:
Eh, haka ne."
Yayin taron Atiku da abokan tafiyarsa sun bukaci ‘yan Najeriya, musamman na majalisa, da su yi watsi da dokar ta-baci da Tinubu ya ayyana a Jihar Rivers.
Atiku ya kara da cewa:
“Mun hadu ne domin mu magance mummunan matakin da ba bisa doka ba da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu GCFR ya dauka a ranar 18 ga Maris, 2025.”
“Wannan ya hada da ayyana dokar ta-baci a Jihar Rivers da kuma dakatar da gwamna da mataimakinsa da majalisar jihar ba bisa doka ba.”
Tinubu ya magantu kan hadaka a 2027
Mun ba ku labarin cewa Fadar shugaban ƙasa ta yi martani kan shirin da ƴan jam'iyyun adawa suka fara yi na yin haɗaka kan zaɓen shekarar 2027.
Hadimin shugaban kasa, Bola Tinubu ya bayyana cewa ko kaɗan mai gidan na su bai damu da batun zaɓe mai zuwa ba saboda akwai abin da ya sanya a gaba saboda yan kasa.
Sunday Dare ya bayyana cewa abin da shugaban ƙasan ya sanya a gaba shi ne yadda zai inganta rayuwar ƴan Najeriya da kawo musu ci gaba mai ɗorewa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng