'Mun Taimake Shi': Tinubu Ya Fadi Abin da Zai Faru da Fubara idan da ba a Dakatar da Shi ba

'Mun Taimake Shi': Tinubu Ya Fadi Abin da Zai Faru da Fubara idan da ba a Dakatar da Shi ba

  • Ministan shari'a, Lateef Fagbemi ya ce dokar ta-baci da Bola Tinubu ya kafa ce ta hana Majalisar Jihar Rivers tsige Gwamna Siminalayi Fubara
  • Fagbemi SAN ya bayyana cewa an riga an shigar da takardar zargin "cin amanar aiki" a kan Simi Fubara da mataimakiyarsa kafin dokar ta-bacin
  • Shugaba Tinubu ya dakatar da Gwamna Fubara, mataimakiyarsa da mambobin majalisar dokoki domin dakile rikicin siyasa da rashin tsaro a jihar
  • Ministan shari'ar ya kare matakin Tinubu, yana mai cewa wannan matsaya ce mai karfin hali wadda ta dakile rikicin da ka iya dagule jihar Rivers

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Port Harcourt, Rivers - Ministan shari'a, Lateef Fagbemi ya fadi dalilin dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara a jihar Rivers.

Fagbemi ya ce da ba don dokar ta-baci ba da gwamnatin tarayya da sanya ba da tuni an tsige Gwamna Simi Fubara daga kujerarsa.

Kara karanta wannan

Dakatar da Fubara: Gwamnatin Tinubu ta yi magana kan 'laifin' Wike

Gwamnatin Tinubu ta fadi dalilin dakatar da Fubara
Gwamnatin Bola Tinubu ta ce taimakon Gwamna Siminalayi Fubara ta yi. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Sir Siminalayi Fubara.
Asali: Facebook

Tinubu ya dakatar da gwamnatin Fubara

Fagbemi ya fadi haka ga manema labarai a Abuja, ya ce dokar ta-bacin ce ta hana Majalisar Dokokin jihar tsige Fubara da mataimakiyarsa, cewar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A jiya Talata 18 ga watan Maris, 2025 Shugaba Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a Jihar Rivers saboda rashin kwanciyar hankali da rikicin siyasa da ya dabaibaye jihar.

Shugaban kasa ya kuma dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara, mataimakiyarsa Ngozi Odu, da dukan 'yan majalisar dokokin jihar.

Kafin wannan mataki, Majalisar Dokokin jihar ta riga ta fitar da sanarwar zargin cin amanar aiki a kan Fubara da mataimakiyarsa.

Tinubu ya ce ya kare Fubara ne daga tsigewar majalisa
Bola Tinubu ya fadi dalilin sanya dokar ta-ɓaci a Rivers. Hoto: Bayo Onanuga.
Asali: Facebook

Tinubu ya fadi taimakon da ya yi wa Fubara

Lateef Fagbemi ya ce ayyana dokar ta-bacin wata dabara ce da shugaban kasa ya yi wanda ta dakile yiwuwar tsige Fubara daga kan mulki.

Ya ce:

“Game da sulhu da sauyi, haka abin ke, kada ku manta, a jiya (Talata) aka fitar da takardar tsige shi daga majalisa.

Kara karanta wannan

Gwamna Fubara ya ɗauki matakin ƙarshe, ya fice daga gidan gwamnatin jihar Ribas

“Idan an bar tsige shi ya ci gaba, da Gwamna zai rasa komai, saboda haka, idan za a ce sulhu ne, na yarda da hakan.”
“Ina ganin cewa maimakon a bar tsige shi ya kammala, wanda zai fitar da su duka daga ofis, wannan matakin yafi alheri.”

Ya kare matakin shugaban kasa na ayyana dokar ta-baci a Jihar Rivers, yana cewa Shugaba Tinubu ya dauki mataki mai karfin hali, Punch ta ruwaito.

Ya kara da cewa:

“Muna nan a lokacin da ya yi jawabi ga jama’a, ya kuma bayyana komai tun daga farko har ƙarshe."

Rivers: Dakatattun ƴan majalisa sun yabawa Tinubu

Mun ba ku labarin cewa majalisar dokokin Jihar Rivers da aka dakatar ta goyi bayan dokar-ta-baci da Bola Tinubu ya ayyana, tana mai dora laifi kan Gwamna Siminalayi Fubara.

Dakataccen shugaban majalisar, Martin Amaewhule, ya ce Fubara ya karya dokoki da dama daga ciki akwai hana majalisa aiki yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

Majalisa ta hargitse ana shirin tattauna maganar dakatar da Gwamna Fubara

Amaewhule ya ce matakin shugaban kasa ya na da amfani ga kasa baki daya, yana kuma kira ga jama'a su kwantar da hankalinsu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng