Ana tsaka da Batun Ribas, Tsohon Ɗan Takara a Kano Ya Dura kan Shugaban Matasan PDP
- Hon. Adnan Mukhtar Adam Tudun-Wada ya caccaki shugaban matasan PDP na ƙasa, Prince Muhammad Kadade kan gaza wakiltar matasa
- Tsohon ɗan takarar Majalisar Dokokin Kano, Hon. Adnan ya ce Kadade ya gaza sauke nauyun da aka ɗora masa na jagorantar matasan PDP
- Ya zargi shugaban matasan da yi wa ministan Abuja, Nyesom Wike aiki, ya na cewa duk da halin da jama'a ke ciki, ba ya iya fitowa ya soki gwamnati
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Tsohon ɗan takarar kujerar majalisar dokoki ta jihar Kano a zaɓen 2023, Adnan Mukhtar Tudun-wada, ya soki shugaban Matasa jam’iyyar PDP na ƙasa, Muhammad Kadade
Adnan Mukhtar ya ce shugaban matasan ya gaza sauke nauyin da aka ɗora masa musamman wajen haɗa kan matasa da jawo su cikin al'amuran kasar nan.

Kara karanta wannan
Ba jira: Ministan Tsaro, Matawalle ya fadi shirin sojoji kan dokar ta baci a Rivers

Asali: Facebook
Matashin ɗan siyasar ya yi wannan suka ne a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ofishin jaridar PR Nigeria da ke Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Adnan ya caccaki shugaban matasan PDP
Adnan Mukhtar ya ce shugaban matasan ya gaza yin abin da ya dace wajen jawo matasa a jiki da tsoma baki a wasu harkokin gwamnati da suka shafi matasa.
Ya nuna takaicinsa kan yadda Kadade ya kasa shirya gangamin wayar da kai da jaddada goyon bayan matasa ga ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP a 2023, Atiku Abubakar, duk da kiraye-kirayen da aka yi masa.
“A matsayin shugaban matasa, ya zama dole ya kasance mai faɗa aji a cikin kwamitin gudanarwa na jam’iyya, domin yana wakiltar dukkan matasan da ke cikin jam’iyyar.
"Amma kun taɓa ganin yana gudanar da taro da ƙungiyoyin matasa sai dai kawai ya tsaya yin hoto da manyan mutane," in ji shi.
Matasa na da muhimmanci a PDP
Hon. Adnan ya jaddada cewa ɓangaren matasa na PDP yana da matukar muhimmanci duba da rawar da matasa ke takawa a kowanne zaɓe
Amma saboda rashin kulawar shugaban matasan, ɓangaren ya yi rauni ba kamar yadda ake tsammani ba, rahoton Politics Digest.

Asali: Facebook
Ya ci gaba da cewa:
“Duk da yake ina da damar yin magana da shi, ya ƙi sauraron kowa da ke so ya gyara kuskurensa.
"Dubi halin da ƙasar ke ciki, rikicin jam’iyya, matsin tattalin arziƙi, da sauran al’amura amma ya yi shiru saboda tsoron Nyesom Wike, wanda ya zama babban abokin hamayyar PDP.
Shugaban matasan PDP ya koma tsagin Wike?
A cewar Adnan, ya samu labarin da ke nuna cewa Muhammad Kadade ba ya tare da PDP, Nyesom Wike yake yi wa biyayya.
Ya buƙaci shugaban matasan PDP da ya gyara kuskurensa domin ba a makara ba. Sannan ya kira ga matasan Najeriya su haɗa kai da nufin ceto ƙasar daga halin da take ciki.
Legit Hausa ta tuntuɓi Hon. Adnan Mukhtar kuma ya shaida mana cewa ya yi wannan suka ne ba don komai ba sai don ya ja hankalin Kadade ya dawo hayyacinsa.
Ya ce har yanzu shugaban matasan yana da sauran kusan shekara ɗaya, don haƙa ya kamata ya yi wa kansa karatun ta natsu, ya gayara kura-kuransa.
"Alal misali taron matasa da gwamnati za ta shirya, ya kamata a ce ya fito ya yi magana domin gwamnati ta kowa ce, amma shiru kake ji," in ji shi.
PDP ta yi Allah wadai da kwace filinta
A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta yi Allah wadai da matakin kwace sakatariyarta da ministan Abuja, Nyesom Wike ya yi.
Mai magana da yawun PDP na ƙasa, Hon. Debo Ologunagba, ya zargi APC da ƙoƙarin murƙushe adawa da gudanar da mulkin danniya a ƙasar nan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng