Gwamnatin Rivers Ta Fadi Mamakin da Tinubu Ya Ba Ta kan Dakatar da Fubara
- Gwamnatin Rivers ta ce abin mamaki ne Bola Tinubu ya dakatar da gwamna Simi Fubara amma ya bar Nyesom Wike
- A cewar gwamnatin, Fubara ya kasance mai bin doka da tafiyar da mulki bisa adalci duk da rikicin siyasa a jihar
- Ta bukaci al’ummar Rivers su ci gaba da zama lafiya tare da yin biyayya ga doka yayin da ake kokarin warware matsalar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Rivers - Gwamnatin Jihar Rivers ta bayyana mamakinta kan matakin shugaba Bola Tinubu na dakatar da Siminalayi Fubara.
Gwamnatin ta ce abin mamaki ne a dakatar da Fubara amma a bar Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, wanda ake zargi da tayar da rikicin siyasa a jihar.

Asali: Twitter
Vanguard ta wallafa cewa kwamishinan yada labaran jihar, Warisenibo Joe Johnson, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Rivers ta ce matakin ba daidai ba ne, domin Fubara yana kokarin tabbatar da zaman lafiya da ci gaban jihar.
Gwamnatin Rivers ta ce Fubara na bin doka
Kwamishina yada labaran Rivers, Warisenibo Joe Johnson ya ce tun bayan hawansa mulki, gwamna Fubara yana ba da muhimmanci ga tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Ya ce duk da matsalolin siyasa da ake fuskanta, gwamnan ya ci gaba da gudanar da aikinsa bisa doka, yana mai fifita bukatun al’umma fiye da siyasa ko bukatun kansa.
A cewarsa, bayan shiga tsakani da shugaba Tinubu ya yi don kawo zaman lafiya, gwamnatin Rivers ta aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma da zuciya daya.
Punch ta wallafa cewa kwamishinan ya ce gwamnati ta bi umarnin kotu ba tare da bata lokaci ba, domin tabbatar da bin doka da oda a jihar.
Mamakin da gwamnatin jihar Rivers ta yi
Kwamishinan ya ce duk da irin kokarin da Gwamna Fubara ke yi na tabbatar da zaman lafiya, ‘yan majalisar dokoki da ke biyayya ga tsohon gwamna Wike ne suka tayar da hargitsi.
Ya ce abin mamaki ne yadda Shugaban kasa ya dakatar da Fubara amma ya bar Wike, wanda ya fi kowa haddasa rikicin siyasa a jihar.
Johnson ya ce:
"Abin mamaki ne yadda Shugaban Kasa ya sauke gwamna amma ya bar minista wanda shi ne babban jigon rikicin,"
Ya kara da cewa akwai bukatar a bar Fubara ya ci gaba da gudanar da mulki domin samar da zaman lafiya da ci gaba a jihar.
Kiran gwamnatin Rivers ga al’umma
Gwamnatin Rivers ta tabbatar wa da al’ummar jihar cewa ana rikicin siyasa ma Fubara ya ci gaba da gudanar da ayyukan gwamnati yadda ya kamata.

Kara karanta wannan
Tinubu ya dakatar da Fubara: Yadda shugaban ƙasa ke ayyana dokar ta ɓaci a jihohi
Kwamishinan ya bukaci al’ummar Rivers da su ci gaba da zama lafiya tare da yin biyayya ga doka, ya na mai cewa gwamnati za ta cigaba da tattaunawa da hukumomin da suka dace.

Asali: Facebook
APC ta yi barazana ga gwamnan Osun
A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar APC ta gargadi gwamnan jihar Osun kan hukuncin da kotu ta yi game da shugabannin kananan hukumomi.
APC ta ce ya zama wajibi gwamnan ya girmama hukuncin ko kuma ya fuskanci barazana dakatarwa kamar yadda aka yi wa gwamna Simi Fubara.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng