Bayan Dakatar da Fubara, Shugaba Tinubu Ya Naɗa 'Gwamnan Riko' a Jihar Ribas

Bayan Dakatar da Fubara, Shugaba Tinubu Ya Naɗa 'Gwamnan Riko' a Jihar Ribas

  • Bola Tinubu ya naɗa tsohon hafsan rundunar sojin ruwa, Vice Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas (mai ritaya) a matsayin wanda zai jagoranci Ribas
  • Mai girma shugaban ƙasa ya naɗa gwamnatin riƙo a jihar Ribas ne bayan ayyana dokar ta ɓaci da dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara
  • Har kawo yanzu Gwamna Fubara ko gwamnatin jihar Ribas ba su ce komai ba dangane da wannan mataki da Bola Tinubu ya ɗauka

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - A ranar Talata, 18 ga Maris, 2025, shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a jihar Ribas sakamakon rikicin siyasar da ya ƙi ƙarewa.

Shugaban kasar ya kuma nada Vice Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas (mai ritaya) a matsayin wanda zai jagoranci gwamnatin rikon ƙwarya a jihar Ribas.

Bola Tinubu.
Shugaba Tinubu ya kafa gwamnatin rikon kwarya a jihar Ribas Hoto: @OfficialABAT
Asali: Facebook

Mai girma Tinubu ya bayyana hakan ne yayin ya yi jawabi kai tsaye ga ƴan ƙasa wanda mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya wallafa a shafin X.

Kara karanta wannan

Tinubu ya dakatar da Fubara: Yadda shugaban ƙasa ke ayyana dokar ta ɓaci a jihohi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bola Tinubu ya ɗauki wannan mataki ne bayan dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara da mataimkiyarsa na tsawon watanni shida.

Vice Admiral Ibas, wanda aka haifa a ranar 27 ga Satumba, 1960, tsohon jami’i ne a rundunar sojin ruwa ta Najeriya wanda ya nuna kwarewa a lokacin da yake bakin aiki.

Ya rike mukamin Babban Hafsan Rundunar Sojin Ruwa ta Najeriya daga 2015 zuwa 2021, ya samu gogewa mai yawa a fannin jagoranci na soja, wanda ake ganin zai taimaka masa a mulkin rikon da zai yi.

Tinubu ya naɗa gwamnatin riko a Ribas

A jawabinsa, shugaba Tinubu ya jaddada cewa bangaren shari’a na jihar Rivers zai cigaba da aiki kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.

A cewarsa hakan zai tabbatar da ci gaba da gudanar da ayyukan shari’a ba tare da tangarda ba a wannan lokaci.

"A yanzu na naɗa Vice Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas (mai ritaya) a matsayin wanda zai jagoranci al'amuran jihar Ribas," in ji Tinubu

Kara karanta wannan

Rikicin Rivers: Tinubu ya dakatar da Gwamna Fubara, ya nada sabon shugaba

Ayyana dokar ta-baci da nada gwamnatin riko wani mataki ne da kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada, wanda ake dauka idan akwai manyan matsaloli a harkar mulki.

Shugaba Tinubu.
Tinubu ya naɗa wanda zai jagoranci harkokin jihar Ribas Hoto: @aonanuga1956
Asali: Facebook

Dalilin ɗaukar wannan mataki a Ribas

Wannan mataki yana nuna cewa gwamnatin tarayya tana kokarin tabbatar da zaman lafiya da ingantaccen shugabanci a jihar Ribas.

Yayin da Vice Admiral Ibas zai fara gudanar da aikinsa, al’ummar jihar Rivers na fatan samun kulawa da gudanarwa mai kyau da za ta magance matsalolin da suka jawo halin da ake ciki.

Gwamnatin tarayya ta tabbatar wa da jama’a cewa wadannan matakai na wucin gadi ne, kuma an dauke su ne domin amfanin ‘yan jihar.

Har yanzu dai ba a bayyana cikakkun dalilan dakatar da Gwamna Fubara ba, haka kuma ba a fayyace tsawon lokacin da dokar ta-bacin za ta dauka ba.

Tinubu ya dakatar da Gwamna Fubara

A wani rahoton, kun ji cewa Bola Tinubu ya dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara, da mataimakiyarsa, Farfesa Ngozi Odu, na tsawon watanni shida.

Kara karanta wannan

Gwamna Nwifuru ya ɗauki zafi, ya sallami hadimai 2 da aka gano sun yi rashin kunya

A cewar Tinubu, ya ɗauki wannan mataki ne bayan duk ƙoƙarin da aka yi na sasanta ɓangarorin da ke faɗa da juna ya ci tura.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng