'Gwanda Buhari': Shugaban Jam'iyya Ya Fadi Azabar da Ake Sha a Mulkin Tinubu
- Shugaban jam'iyyar ADP, Injiniya Yabagi Sani, ya ce mulkin Bola Ahmed Tinubu zai shiga tarihi a matsayin mafi muni a tarihin Najeriya
- Injiniya Yabagi Sani ya ce a halin azaba da kuncin rayuwa da 'yan Najeriya ke ciki a yanzu, har gwanda lokacin mulkin Muhammadu Buhari
- Ya bukaci gwamnati da ta magance matsalar hauhawar farashi, da tsadar sufuri, yana mai cewa wahalar da ‘yan ƙasa ke sha ta yi yawa
- Shugaban jam'iyyar ya ce dole ne gwamnati ta bunkasa masana’antu da dakile cin hanci domin farfaɗo da tattalin arziki da rage radadin talauci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugaban jam’iyyar ADP na ƙasa, Injiniya Yabagi Sani, ya ce mulkin shugaba Bola Tinubu zai zama ɗaya daga cikin mafi muni a tarihin Najeriya.

Kara karanta wannan
"An takura wa shugaban kasa" Seyi Tinubu ya kare mahaifinsa daga sukar 'yan adawa
Ya zargi gwamnatin Tinubu da haddasa wahala da yunwa ga 'yan Najeriya, yana mai cewa halin da ake ciki ya fi na lokacin Muhammadu Buhari muni.

Asali: Facebook
'Yan Najeriya na shan bakar wahala' - Yabagi Sani
Da yake magana a shirin siyasar Lahadi na Trust TV, Injiniya Yabagi Sani ya bayyana damuwarsa kan halin da tattalin arzikin ƙasa ke ciki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bukaci gwamnati ta magance hauhawar farashin kaya, matsalar kuɗin waje, da tsadar sufuri domin rage wahalhalun da ‘yan Najeriya ke fuskanta.
"A yau 'yan Najeriya ba sa farin ciki. Azabar da mutane ke sha a wannan gwamnatin ba a sha ta a gwamnatin da ta shude ba.
“Na fahimci cewa sai an sha wahala kafin a jin daɗi, amma idan wahalar ta dauki dogon lokaci, mutane ba za su iya morar jin dadin ba."
- Shugaban jam'iyyar ADP.
Shugaban ADP ya ba gwamnatin Tinubu shawara

Asali: Twitter
Injiniya Yabagi Sani ya ce dole ne gwamnati ta ɗauki matakan dakile cin hanci da rashawa, yana mai cewa wannan matsala ce da ke ƙara dagula tattalin arziki.
A cewarsa, hauhawar farashin kayayyaki ya yi yawa, kuma tilas gwamnati ta ɗauki matakan rage matsin tattalin arziki da ke addabar 'yan ƙasa.
Ya bukaci gwamnatin Tinubu da ta magance matsalar faduwar darajar Naira domin hana hauhawar farashin kayayyakin da ake shigo da su cikin ƙasar.
Injiniya Yabagi Sani ya ce:
"Idan gwamnati ta mayar da hankali kan masana’antu, hakan zai taimaka wajen samar da kayayyaki a farashin da talaka zai iya saya."
An nemi gwamnatin Tinubu ta sauya dabaru
Shugaban jam'iyyar ya ce gwamnatoci su kan ɗauki wasu matakai da ake ganin dole ne, amma wannan bai kamata ya jefa ‘yan ƙasa cikin halin ni-'yasu ba.
Ya ce Najeriya na da arziki sosai, amma sai gwamnati ta ɗauki sahihan matakai don ceto tattalin arzikin ƙasa daga durƙushewa.
Ya ƙara da cewa dole ne gwamnatin Bola Tinubu ta sauya dabarunta idan tana son rage wahalar da ke addabar ‘yan Najeriya a halin yanzu.
'Gwanda mulkin Buhari a kan Tinubu' - Mabaraciya
A wani labarin, mun ruwaito cewa, wata mabaraciya a jihar Oyo, ta kwatanta mulkin tsohon shugaba Muhammadu Buhari da na shugaba Bola Tinubu,
Sadiya Ado, ‘yar asalin karamar hukumar Wudil a jihar Kano, ta ce a gare ta, gwamnatin Buhari ta fi sauƙi fiye da ta gwamnatin Tinubu da ake ciki yanzu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng