Gwamnatinka ce mafi muni a tarihin Najeriya – Tsohon minista Dalung ya caccaki Buhari

Gwamnatinka ce mafi muni a tarihin Najeriya – Tsohon minista Dalung ya caccaki Buhari

Tsohon ministan wasanni, Solomon Dalung, ya kushe gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan rashin tsaron da ya addabi yankin arewa.

Ya bayyana gwamnatin a matsayin mafi muni da aka taba yi a tarihin kasar nan.

A yayin jawabinsa a wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a jiya, Dalung ya ce duk da makuden kudin da ake warewa tsaro, babu abinda ya sauya a kan kashe rayukan 'yan Najeriya tamkar dabbobi.

A yayin bayyana matsayarsa a harshen Hausa, Dalung wanda ya yi minista tsakanin 2015 zuwa 2019, ya bayyana mulkin shugaba Buhari da mafi munin mulki a Najeriya.

Ya zargi hadiman shugaban kasar da kin sanar da shi gaskiya a yayin yaki da ta'addanci da kuma 'yan bindiga.

Ya ce Buhari ya ja kunnen 'ya'yansa da ke aiki a karkashinsa wadanda basu sanar da shi gaskiya a kan al'amarin tsaro a kasar nan. Ya bukacesu da su daina zagin shugabannin arewa wadanda ke fadin gaskiya, jaridar The Sun ta ruwaito.

Gwamnatinka ce mafi muni a tarihin Najeriya – Tsohon minista Dalung ya caccaki Buhari
Gwamnatinka ce mafi muni a tarihin Najeriya – Tsohon minista Dalung ya caccaki Buhari Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Ya kushe abinda ya bayyana da halin ko in kula na shugaban kasar da yake fitar da makuden kudin Najeriya don kashewa a kan tsaro amma babu wani sauyi.

"Daga Borno zuwa Kwara, Filato zuwa Sokoto, rayuwar dan Najeriya ba komai bace. Ana kisa a arewa tamkar an samu kaji. Da N5,000 za ka siyi kaza amma yanzu miyagu shiga gidan suke suna halaka jama'a.

"Wannan babban abun kunya ne ga gwamnonin arewa. A maimakon su yi taro da shugabannin addinai da sarakunan gargajiya, yanzu sun fi gane zuwa Abuja su karbi kudi tare da bai wa 'yan bindigar don su daina kashe-kashe.

KU KARANTA KUMA: COVID-19: Bafarawa ya yi muhimmin kira ga ma'aikatan gwamnati

"Wadannan gwamnonin sun fi damuwa da yadda za su yi nasarar lashe zabe, basu damu da rayukan talakawa ba. Zan iya tabbatar muku da cewa zaku yi nadama nan da 2021 idan baku dauki matakin gaggawa ba.

"A kowacce rana ana zagin shugaban kasa kuma suna zaginmu saboda muna goyon bayan ka. Su kan tambayemu ko abinda kayi musu alkawari kenan tun a farko.

"Ka zagaye kanka da wasu irin mutane wadanda basu kishin kasar nan. Kana ta fitar da kudi amma kashe-kashe na ci gaba. Idan ka bada kudi a yaki rashin tsaro, shagalinsu suke yi.

"Ka taba cewa basu bin dokokinka. A matsayin ka na shugaban kasa, me yasa ka ci gaba da barinsu tare da kai?," Dalung yace.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel