Ana Zancen Natasha, Dattawan APC Sun Tura wa Tinubu Zarge Zarge kan Akpabio
- Wasu dattawan APC a Akwa Ibom sun zargi shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, da yin aiki da PDP domin cin gajiyar siyasa
- An ruwaito cewa dattawan jam'iyyar sun bayyana a wata wasika cewa Akpabio na kokarin raunana APC a jihar don amfanar kansa
- Sai dai kakakin shugaban majalisar ya musanta zarge-zargen, yana mai cewa labarin kage ne daga masu son tayar da hargitsi APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Akwa Ibom - Wasu dattawan jam’iyyar APC a jihar Akwa Ibom sun zargi shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, da cin amanar jam’iyyar ta hanyar hada kai da PDP.
A cewar dattawan, Akpabio na kokarin raunana APC domin bai wa PDP damar samun galaba a zaben 2027.

Kara karanta wannan
'Dan Sule Lamido ya bi sahun mahaifinsa, ya fadi kuskuren ƴan Najeriya a zaben 2023

Asali: Facebook
Rahoton jaridar Punch ya bayyana cewa wasikar ta samu sa hannun dattawan APC daga yankuna uku na jihar, wadanda suka hada da Okokon James, Peter Ibanga, da Chief Victor Affiah.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dattawan sun bayyana damuwarsu a cikin wasikar da suka aika wa shugaban kasa Bola Tinubu, suka bukaci a dauki mataki cikin gaggawa.
Zargin Godswill Akpabio da mika APC ga PDP
Dattawan APC a Akwa Ibom sun ce shugaban jam'iyya na jihar, Stephen Ntukekpo, da ministan man fetur, Ekperikpe Ekpo, sun shaida cewa Akpabio ne ya umarce su da raunana jam’iyyar.
A cewar dattawan, za a raunana APC a jihar ne domin bai wa PDP damar yin nasara a babban zabe mai zuwa.
A cikin wasikar, sun ce:
“Tun daga jam’iyyar ACN har zuwa hadewar da aka yi da CPC da ANPP, muna tare da kai, shugaba Bola Tinubu.
"Amma ba mu taba ganin irin wannan cin amanar APC ba. Jam’iyyar ta ruguje a jihar.”
Vanguard ta wallafa cewa dattawan sun gargadi Tinubu cewa, idan ba a dauki mataki ba, ba za a sami magoya bayan APC da za su tarbe shi ba idan ya zo yakin neman zabe jihar.
An zargi Akpabio da rashin taimakon APC
A cewar wasikar, dattawan sun bayyana cewa Akpabio bai nuna wani kokari na taimakawa APC da muradin Tinubu na zarcewa ba.
Sun ce duk da cewa APC ce ta samar da shugaban majalisar dattawa, jam’iyyar ta kasance cikin mawuyacin hali a jihar.
Haka kuma sun musanta jita-jitar da ke cewa gwamnan jihar, Umo Eno, yana shirin komawa APC, suka ce hakan ba gaskiya ba ne.

Asali: Twitter
Sun bukaci shugaban kasa Tinubu da ya gaggauta daukar matakin ceto APC daga durkushewa a jihar domin kada jam’iyyar ta rushe.
Akpabio ya musa zargin cin amanar APC
Da yake mayar da martani, hadimin shugaban majalisar dattawa kan harkokin yada labarai, Jackson Udom, ya musanta wadannan zarge-zarge.
Udom ya ce:
“APC na nan daram a Akwa Ibom. Wadanda ke kokarin haddasa rabuwar kai ne ke yada wadannan jita-jita marasa tushe.”
Ya kara da cewa akwai kyakkyawar fahimta tsakanin Akpabio da gwamnan jihar, Umo Eno, don haka wasu ke kokarin yada labarin cewa an sayar da jam’iyyar APC.
El-Rufa'i ya bukaci a yi wa APC taron dangi
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya yi kira ga manyan 'yan adawa da su hada kai da jam'iyyar SDP.
Nasir El-Rufa'i ya yi kira ga Atiku Abubakar, Peter Obi da sauran manyan 'yan adawa da su taru a jam'iyyar SDP domin tunkarar APC a 2027.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng