'Dan Sule Lamido Ya Bi Sahun Mahaifinsa, Ya Fadi Kuskuren Ƴan Najeriya a Zaben 2023

'Dan Sule Lamido Ya Bi Sahun Mahaifinsa, Ya Fadi Kuskuren Ƴan Najeriya a Zaben 2023

  • Tsohon dan takarar gwamna a Jigawa, Mustapha Sule Lamido ya ce PDP ta gargadi ‘yan Najeriya game da wahala tun kafin zaben 2023, amma mutane suka ki sauraro
  • Ya soki tsarin APC, inda ya ce tallafi ba zai magance matsalolin tattalin arziki ba, sai dai ya kara dogaro da gwamnati
  • Lamido ya bukaci matasa su koyi darasi daga kura-kuran baya su zabi shugabanni nagari masu hangen nesa a 2027
  • Wani ɗan majalisar tarayya, Hon. Yakubu Danmaliki ya raba shinkafa, babura, injunan dinki da tallafin karatu ga jama’ar mazabarsa don rage radadin rayuwa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Dutse, Jigawa - Tsohon dan takarar gwamnan PDP a Jihar Jigawa, Mustapha Sule Lamido, ya caccaki APC da masu kada kuri’a, yana cewa an ki kaucewa wahala.

Kara karanta wannan

Mene ake kitsawa?: Barau ya gana da Baffa Bichi da tsohon kwamishinan Abba

Dan tsohon gwamna Jigawa ya ce tun a zaben 2023 sun gargadi yan Najeriya kan zaben APC amma sun ki ji.

Dan tsohon gwamnan ya sake gargadin al'umma kan zaben APC
'Dan Sule Lamido ya soki tsarin ba da tallafi inda ya ce ba zai dore ba. Hoto: Mustapha Sule Lamido.
Asali: Facebook

Mustapha Sule Lamido ya koka kan halin kunci

Yayin wani shirin tallafawa al’umma a Birninkudu/Buji da Yakubu Danmaliki ya shirya, Lamido ya yabawa wakilin PDP bisa jajircewarsa ga jama’a, cewar The Guardian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai ya soki salon tattalin arzikin kasar, yana cewa dogaro da tallafi kamar kiwon saniya ba tare da barinta ta nemo ciyawa ba ne.

Ya ce:

“Ina ganin ana bukatar tallafi yanzu, amma ba mafita ba ce mai dorewa, tattalin arzikin ya tabarbare.
“Mun fadawa jama’a su yi hankali da zaben 2023, APC ba ta damu da ci gaban kasa ko na jama’a ba."
Dan tsohon gwamna ya fadi gargadin da suka yi a zaben 2023
'Dan Sule Lamido ya ce ya kamata matasa su hankalta a zaben 2027. Hoto: Mustapha Sule Lamido.
Asali: Twitter

Gargadin da PDP ta yi a zaben 2023

Mustapha ya ce PDP ta riga ta gargaɗi jama’a a lokacin kamfen, inda suka nuna rashin hangen nesa da kwazo daga APC.

Matashin ya bayyana cewa matsin lambar yau da talauci da rashin aikin yi duk abin da PDP ta hango ne tun da farko.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Shugaban Amurka, Trump ya samu izinin kakaba takunkumi ga Najeriya

Ya bukaci matasa su koyi darasi daga kuskuren baya, su zabi shugabanni masu gaskiya da hangen nesa a 2027.

Ya kara da cewa:

“Tun 2015 APC ke mulki, mun gani a 2019 da 2023, yanzu kasa na cikin matsala, matasa su farka.
“Tallafi hadari ne ga tattalin arzikinmu, siyen kaya da rabawa ba zai habbaka kasa ba."

Ya ce dogaro da tallafi hanya ce ta dagula tattalin arziki, domin gwamnati ba za ta ci gaba da sayar da kaya kawai ba.

Mustapha Lamido ya kara da cewa shigo da kaya daga waje ba zai taimaka wajen ci gaban tattalin arzikin kasar ba.

Yayin da Najeriya ke fama da kalubale, kalaman Lamido sun nuna yadda jama’a ke nuna rashin jin dadi da gwamnati.

Sule Lamido ya caccaki Nasir El-Rufai

Kun ji cewa tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido ya ce Nasir El-Rufai ba ya da darajar shugabanci, ba zai iya janyo ‘yan PDP su bi shi SDP ba.

Lamido ya ce El-Rufai bai cancanci gayyatar manyan ‘yan adawa zuwa sabuwar jam’iyyarsa ba domin ba shi da kishin kasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel