Bayan El Rufai Ya Yi Fatan Ya Dawo SDP, Alamu Sun Nuna Peter Obi na Shirin Canza Jam'iyya

Bayan El Rufai Ya Yi Fatan Ya Dawo SDP, Alamu Sun Nuna Peter Obi na Shirin Canza Jam'iyya

  • Alamu masu karfi sun nuna cewa Peter Obi na shirin sauya sheka daga LP zuwa jam'iyyar PDP domin haɗa karfi wajen ceto Najeriya
  • Wasu majiyoyi sun ce ziyarar da tsohon gwamnan Anambra ya kai Bauchi na da alaƙa da shirin haɗewar jam'iyyun adawa gabanin 2027
  • Bala Muhammad na Bauchi kuma shugaban gwamnonin PDP ya ce a shirye yake ya yi aiki da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Mista Obi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bauchi - A wani mataki da ke nuna shirin haɗewar jam’iyyun adawa don tunkarar zaɓen 2027, tsohon dan takarar shugaban ƙasa na LP, Peter Obi, ya gana da Gwamna Bala Muhammed na Bauchi.

Wannan ganawa da suka yi a fadar gwamnatin Bauchi tana da alaƙa da ƙoƙarin lallashin Peter Obi ya dawo jam'iyyar PDP.

Peter Obi.
Peter Obi na dab da sauya sheƙa daga LP zuwa PDP Hoto: Mr. Peter Obi
Asali: Twitter

A rahoton The Guardian, majiyoyi daga fadar gwamnatin Bauchi sun bayyana cewa Peter Obi ya ziyarci Bala ne domin tabbatar da cewa kan gwamnonin PDP a haɗe yake.

Kara karanta wannan

"Dama ƙarfa karfa aka mana a 2023," Sanata Tambuwal ya hango faɗuwar Tinubu a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Manyan PDP na ci gaba da lallashin Peter Obi

An ce Obi ya gana da Bala Muhammed, wanda shi ne shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP domin tabbatar da cewa kansu a haɗe yake, suna son ya dawo PDP.

Majiyar ta ce manyan shugabannin PDP, ciki har da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, sun matsa lamba ga Obi da ya dawo jam’iyyar PDP tare da Datti Baba-Ahmed.

Suna son dawowar Peter Obi ne domin ɗinke barakar PDP da kuma haɗa karfi da karfe wajen ceto Najeriya daga halin da take ciki a karƙashin APC.

Wata majiya ta ce:

"An ce Atiku ya ziyarci tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, don neman ya sa baki wajen lallashin Obi ya dawo PDP.
"Wannan shiri ya na da nasaba da ƙoƙarin gyara kura-kuran da PDP ta tafka a zaben da ya gabata, musamman batun tsarin mulkin karba-karba.

Peter Obi ya gana da Gwamna Bala

Kara karanta wannan

Tsofaffin ministocin Buhari 10 da manyan ƙusoshi na shirin bin El Rufai zuwa SDP

Bayan ganawa da Peter Obi, an ji Gwamna Bala Muhammed na cewa a shirye yake ya yi aiki tare da tsohon gwamnan jihar Anambra.

"Obi ne jagoran adawa a Najeriya saboda matsayinsa da kuma kima da ya ke da shi a siyasa. Don haka, zan yi aiki tare da shi don tabbatar da cewa mun kawo gyara ga Najeriya," in ji Bala.
Peter Obi da Bala Muhammed.
Peter Obi ya ce za su yi duk mai yiwuwa wajen ceto Najeriya Hoto: Peter Obi, Bala Muhammed
Asali: Twitter

Abin da Obi ya tattauna da Gwamnan Bauchi

A nasa bangaren, Peter Obi ya bayyana cewa ya gana da Bala Mohammed ne don tattauna halin da Najeriya ke ciki da kuma makomarta.

"Dole ne mu ci gaba da tattaunawa don duba makomar Najeriya. Kuna sane da irin matsalolin da kasar nan ke ciki, musamman a yankin Arewa.
"Idan muna son daidaita Najeriya, dole ne mu magance matsalolin da ke addabar Arewa,"

- in ji Peter Obi.

Ya kuma jaddada cewa babbar matsalar Najeriya ba ta takaita ga ta’addanci kadai ba, talauci ne babbar matsalar da ke haifar da rashin tsaro, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

"Ba mu yarda ba," El Rufai ya ƙara shiga matsala bayan komawa SDP, matasa sun masa rubdugu

Bisa haka, ake hasashen cewa Peter Obi na iya sauya sheka daga LP zuwa PDP idan har tuntuɓa da tattaunawar da yake yi da kusoshin jam'iyya ta tafi daidai.

El-Rufai na fatan haɗewa da Atiku, Obi

A wani labarin, kun ji cewa tsohon gwamnan Kaduna, Nasiru El-Rufai ya ce yana fatan Atiku da Obi za su biyo shi, su haɗu a jam'iyyar SDP.

Malam El-Rufai ya ce akwai bukatar ƴan adawa su haɗa karfi da karfe domin kifar da jam'iyyar APC a zabe mai zuwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng