Siyasa Mugun Wasa: El Rufa'i Na Fatan Atiku da Obi Su Hade da Shi a SDP

Siyasa Mugun Wasa: El Rufa'i Na Fatan Atiku da Obi Su Hade da Shi a SDP

  • Tsohon gwamnan Kaduna, Nasiru El-Rufa’i, ya ce yana fatan Atiku Abubakar da Peter Obi su koma jam’iyyar SDP
  • Nasir El-Rufa'i ya bayyana cewa adawa na bukatar haɗa kai domin fuskantar jam’iyyar APC mai mulki a zaben 2027
  • Duk da cewa ya raba hanya da shugaba Bola Tinubu, Nasir El-Rufa’i ya ce bai yi da-na-sanin mara masa baya ba a 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasiru El-Rufa’i, ya bayyana cewa yana fatan manyan jagororin ‘yan adawa, ciki har da Atiku Abubakar da Peter Obi, za su koma jam’iyyar SDP.

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa ana bukatar 'yan adawa su hada murya daya domin yin takara da tunkarar APC a 2027.

Atiku
El-Rufa'i na fatan 'yan adawa su hada kai a Najeriya. Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

A wata hira da BBC ta yi da shi, El-Rufa’i ya ce SDP na da cikakkiyar damar zama wata sabuwar APC, ba tare da an buƙaci rijistar sabuwar jam’iyya ba.

Kara karanta wannan

El Rufa'i ya fadi matsayarsa kan takara da Tinubu a zaben 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Fatana da addu’ata su ne duk shugabannin adawa su haɗu, su shiga SDP mu fuskanci waɗanda ke mulki."

- Nasiru El-Rufa’i

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa SDP na da tsari mai karfi kuma ba ta da wata matsala da za ta hana adawa yin amfani da ita.

Me yasa El-Rufa'i ya goyi bayan Tinubu a 2023?

Tsohon gwamnan na Kaduna ya kuma bayyana cewa, duk da cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu bai bi alkawuran da suka yi ba, bai yi da-na-sanin mara masa baya a zaɓen 2023 ba.

A cewar Nasir El-Rufa'i, akwai dalilai guda biyu da suka sa ya tsaya tsayin daka wajen tallata Tinubu a Arewa:

"Dalili na farko shi ne manyan malaman kudu maso yamma sun roƙe ni in mara wa Tinubu baya saboda a cewarsu, ana cutar da Musulmin yankin a lokacin da shugabancin ƙasa ke Arewa,"

Ya kara da cewa a yanzu da Bola Tinubu ya hau mulki, Musulmi daga Kudu maso Yamma sun samu dama.

Kara karanta wannan

"Ba mu yarda ba," El Rufai ya ƙara shiga matsala bayan komawa SDP, matasa sun masa rubdugu

Bola Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

El-Rufa’i: "Ba mu saba karya alƙawari a Arewa ba"

El-Rufa’i ya bayyana cewa dalili na biyu da ya sa ya goyi bayan Tinubu shi ne domin yarjejeniyar da aka yi cewa mulki zai koma Kudu bayan mulkin Buhari.

"Mu ‘yan Arewa ba mu saba karya alƙawari ba. Saboda haka, na goyi bayan Tinubu domin cika wannan yarjejeniya,"

- Nasir El-Rufa’i

A makon da ya wuce ne Malam Nasir El-Rufa’i ya koma SDP bayan fita daga APC, inda kuma ya sha alwashin fara adawa da salon mulkin Bola Tinubu.

MC Tagwaye ya koma SDP

A wani rahoton, kun ji cewa dan barkwanci da ya shahara da koyi da shugaba Muhammadu Buhari ya koma SDP mai adawa.

A ranar Juma'a MC Tagwaye ya bayyana dalilan da suka sanya shi sauya sheka daga APC bayan ya yi shawara da makusantansa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng