NNPP Ta Gaskata El Rufa'i a Zargin Gwamnatin APC da Haddasa Rikici a Jam'iyya

NNPP Ta Gaskata El Rufa'i a Zargin Gwamnatin APC da Haddasa Rikici a Jam'iyya

  • Rahotanni na nuni da cewa jam’iyyar NNPP ta nesanta kanta daga wata sanarwa da ke sukar Nasir El-Rufai kan rikicinta
  • Kakakin jam’iyyar ya ce bangaren da ke sukarsa ba ‘yan jam’iyya ba ne, kuma ba su da hurumin magana a madadin NNPP
  • Biyo bayan hakan, kakakin NNPP ya yi kirarin gwamnatin tarayya na da hannu a rikicin da ke addabar jam'iyyar a Najeriya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Jam’iyyar NNPP ta bayyana cewa wasu mutane da ke ikirarin suna da iko a jam’iyyar ba ‘yan jam’iyya ba ne, kuma ba su da hurumin magana a madadin NNPP.

Wannan na zuwa ne bayan da wani bangare na jam’iyyar ya bukaci tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, da ya janye maganarsa kan rikicin NNPP tare da neman afuwa.

Kara karanta wannan

Mutum sama da 200,000 sun yanyame El Rufa'i, an ragargaje shi daga shiga TikTok

Kwankwaso
NNPP ta goyi bayan maganganun El-Rufa'i. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso|Nasir El-Rufa'i
Asali: Facebook

The Cable ta wallafa cewa jam’iyyar ta ce tana goyon bayan El-Rufai, tana mai cewa akwai hannun gwamnatin tarayya a rikicin da ke faruwa a cikinta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zargin da El-Rufa'i ya yi a rikicin NNPP

A cikin wani faifan bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta, Nasir El-Rufai ya bayyana cewa gwamnatin tarayya karkashin jam’iyyar APC ce ke haddasa rikici a cikin jam’iyyun adawa.

Tsohon gwamnan ya ce dakatar da Rabiu Musa Kwankwaso daga jam’iyyar NNPP da wasu ke ikirarin sun yi, wata makarkashiya ce don ruruta rikici a cikin jam’iyyar.

Nasir El-Rufai ya yi wannan bayani ne yayin da yake zantawa da wasu shugabannin jam’iyyar SDP a Abuja.

Kaduna
Tsohon gwamnan jihar Kaduna. Hoto: Nasiru El-Rufa'i
Asali: Facebook

NNPP: "Oginni ba 'dan jam’iyya ba ne"

A wata sanarwa da NNPP ta fitar a ranar Alhamis ta hannun kakakinta, Ladipo Johnson, jam’iyyar ta nesanta kanta daga bangaren Oginni, tana mai cewa ba ‘yan jam’iyya ba ne.

Kara karanta wannan

An sake rikita Tinubu, Kwankwaso, Obi da gwamnonin PDP sun shirya raba shi da mulki

Bayan haka, Ladipo Johnson ya kara da cewa ba su da hurumin magana a madadin jam'iyyar a Najeriya.

The Guardian ta wallafa cewa Johnson ya ce:

“Oginni da mabiyansa ba ‘yan jam’iyyar NNPP ba ne a doka da gaskiya. Ba su da wani iko na magana a madadin jam’iyyar.”

Ya ce yadda mutanen suka nuna goyon baya ga APC a lokacin da NNPP ke kotu kan kujerar Abba Kabir Yusuf, da rikicin masarautar Kano, yana tabbatar da cewa ba su da wata alaka da NNPP.

Ya kara da cewa:

“Kamar yadda El-Rufai ya fada, a fili yake cewa akwai wata muguwar dabara da ke haddasa wadannan rigingimu a cikin jam’iyyar.”

Johnson ya ce akwai alamar cewa bangaren da ke haddasa rikici a jam’iyyar NNPP na aiki ne bisa umarnin wasu manyan masu hannu da shuni.

Kara karanta wannan

'Ku biyo ni TikTok': El-Rufai ya bude shafinsa, ya tara dubban mabiya cikin sa'o'i 24

Ya ce:

“Duk mai hankali zai fahimci cewa mutanen nan suna aiki ne bisa umarnin ubannin gidansu.
Saboda haka, muna goyon bayan maganar El-Rufai cewa akwai wata muguwar dabara a bayan fage.”

Hamza Al-Mustapha ya bi El-Rufai zuwa SDP

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon dan takarar shugaban kasa Manjo Hamza Al-Mustapha ya sauya sheka zuwa SDP.

A ranar Alhamis Manjo Hamza Al-Mustapha ya ce yanke shawarar sauya-sheka, ya ce hakan zai zamo sabon babi a siyasar Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen hausa na legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel