Al Mustapha Ya Ziyarci Atiku Awanni da Sauya Sheka zuwa Jam'iyyar SDP

Al Mustapha Ya Ziyarci Atiku Awanni da Sauya Sheka zuwa Jam'iyyar SDP

  • Tsohon dogarin shugaban ƙasa a mulkin soja, Hamza Al-Mustapha, ya kai ziyarar ban girma ga tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar
  • Wannan ziyara ta jawo abin tofa albarkacin baki, kasancewar wasu na ganin alama ce ta wata hadakar siyasa da ke iya kawo sauyi a zaɓen 2027
  • Sai dai PDP ta yi martani a kan labarin cewa akwai yiwuwar tsohon dan takararta ya sauya sheka, domin ya sha musanta zancn cwa zai bar jam'iyyar

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT AbujaAwanni kaɗan bayan ya sauya sheka zuwa SDP, tsohon dogarin shugaban ƙasa a mulkin soja, Hamza Al-Mustapha, ya ziyarci tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar.

Wannan ziyara ta zo ne a daidai lokacin da Atiku Abubakar ya tabbatar da cewa akwai shirin kawancen jam’iyyu da ake sa ran zai kifar da gwamnatin Bola Tinubu a zaɓen 2027 da ke tafe.

Kara karanta wannan

Sanata ya watsawa matasa kasa a ido, ya ki amincewa ya kara da Tinubu a 2027

Atiku
Al-Mustpha ya ziyarci Atiku Hoto: Special Assistant on Broadcast Media to H.E Atiku Abubakar, GCON
Asali: Facebook

A sakon da ofishin mataimakin Atiku ya wallafa a shafin Facebook, an bayyana cewa jagororin biyu sun tattauna batutuwan da suka shafi cigaban ƙasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka kuma, sun duba batutuwan da suka shafi yadda za a tabbatar da haɗin kan ‘yan Najeriya da nufin samar da zaman lafiya mai dorewa da ci gaban talakawa.

Jama’a sun ji daɗin ziyarar Al-Mustapha ga Atiku

Jama’a sun fara martani kan ziyarar da Hamza Al-Mustapha ya kai wa Atiku Abubakar, wanda wasu ke hasashen alama ce da ke nuna tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar zai bar PDP.

Duk da cewa Atiku ko mukarrabansa ba su yi karin bayani kan batun ba, ziyarar Hamza Al-Mustapha ta biyo bayan ziyarar da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ya kai wa Atiku kafin komawarsa SDP.

Atiku
Ana hasashen Atiku zai bar PDP Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Wasu masu amfani da shafin Facebook sun bayyana fatan cewa wannan haɗin gwiwar zai tarwatsa duk wani shiri da APC ke yi na tabbatar da Tinubu ya sake darewa kujerar mulkin ƙasar nan a zaɓe mai zuwa.

Kara karanta wannan

Manjo Hamza Al Mustapha ya sauya sheka zuwa SDP, ya hade da El Rufa'i

Abdul Bawa ya ke cewa:

"Shugaban ƙasa mai jiran gado da mashawarcin shugaban ƙasa a kan harkokin tsaro mai jiran gado a 2027."

Don-p Enobong Inyang ya ce:

"SDP... ci gaba."

AbdusSamad Abubakar Gwamnaty ya ce:

"Abin na yi ne, khairan In Sha Allah, ba za mu ji kunya ba."

Martanin PDP kan yiwuwar ‘sauya shekar’ Atiku

Yusuf Dingyadi, mataimakin shugaban PDP na ƙasa a ɓangaren yaɗa labarai, ya shaida wa Legit cewa Atiku Abubakar ya sha musanta cewa yana shirin sauya sheka daga jam’iyyarsu.

Sai dai ya ƙara da cewa, ko da Atiku ya sauya sheka daga baya, hakan ba zai sauya alkiblar PDP ba, kuma ba zai hana jam’iyyar cigaba da shirin kwace mulkin kasa daga APC a 2027 ba.

Ya ce:

"Idan ana yaɗa jita-jitar cewa Wazirin Adamawa zai bar jam’iyyar PDP, mu a wajenmu wannan dai labari ne kawai, magana ce maras tushe.

Kara karanta wannan

"Jonathan ya yi bankwana da siyasa," PDP ta magantu kan fito da shi takara

Kuma ko da hakan ta tabbata, babu abin da zai canza a PDP, domin wasu sun fita kuma suka sake dawowa."
"Shi kan shi tsohon mataimakin shugaban ƙasa, ya fito fili, karara ya bayyana cewa babu wata magana kan haka, duk waɗannan rade-radin ba gaskiya ba ne."

Atiku ya magantu kan komawa SDP

A wani labarin, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya karyata rahoton da ke cewa ya fice daga jam’iyyarsa ta PDP zuwa SDP.

Bayan wannan zargi, ana zaton akwai magana mai ƙarfi tsakanin Atiku da wasu tsofaffin ‘yan takarar shugaban ƙasa, kamar Peter Obi na jam’iyyar LP da Rabiu Kwankwaso na NNPP.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel