'Ku Biyo Ni TikTok': El Rufai Ya Bude Shafinsa, Ya Tara Dubban Mabiya cikin Sa'o'i 24
- Tsohon gwamna, Nasir El-Rufai, ya bude shafin TikTok domin yada tunaninsa game da siyasar Najeriya da jam’iyyarsu ta SDP
- El-Rufai ya bayyana cewa wannan ne kadai shafinsa na TikTok, yana gayyatar jama'a su halarci tattaunawa da kallon bidiyonsa
- A cikin sa’o’i 24, shafinsa ya samu mabiya fiye da 184,000 tare da kallon bidiyonsa sau miliyan 1.5
- Hakan ya biyo bayan barin jam’iyyar APC yana mai zargin ta da watsi da al'umma da mayar da gwamnati tamkar kasuwanci
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya bude shafinsa a manhajar TikTok inda ya gayyaci yan Najeriya.
Tsohon gwamnan ya bude shafin TikTok na kansa domin yada tunaninsa kan lamarin siyasar Najeriya da kuma lamuran jam'iyyar SDP.

Asali: Facebook
Musabbabin barin El-Rufai jam'iyyar APC
A cikin bidiyon da ya wallafa a TikTok a ranar Laraba, El-Rufai ya ce ya kirkiri shafin ne domin ya bayyana ra’ayinsa kan siyasar Najeriya da SDP.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan ya biyo bayan sauya sheka da Nasir El-Rufai ya yi daga jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya zuwa SDP mai adawa.
Tun farko, El-Rufai ya dade yana sukar tsarin mulkin gwamnatin Bola Tinubu da kuma jam'iyyar APC da ya ce ta yi watsi da muradun al'umma.
Menene dalilin El-Rufai na bude shafin TikTok?
El-Rufai ya kuma gayyaci masu amfani da TikTok su biyo shi don kallon bidiyo, sharhi da tattaunawa kan wadannan batutuwa.
Ya ce:
“Wannan shi ne kadai kuma sahihin shafina na TikTok, ku biyo ni don bidiyo, sharhi da tattaunawa kan siyasar Najeriya.”
“Haka kuma domin ganin ayyukan jam’iyyarmu ta SDP mai adawa, maraba da zuwa shafin.”

Asali: TikTok
Yawan mabiya da El-Rufai ya samu a shafin TikTok
Shafin TikTok dinsa ya samu sama da mabiya 180,000 a cikin awa 24 da fara amfani da shi yayin da mutane fiye 200,00 suka so bidiyon da ya wallafa.
Ya zuwa yanzu da muke tattara wanann rahoto, Legit Hausa ta leka shafin inda ta gano mabiyan sun kai fiye da 184,700, sannan mutane fiye da 19,000 sun yi martani kan bidiyon.
A bidiyon sanarwar da ya fitar, an samu mutane fiye da miliyan 1.5 da suka kalla zuwa lokacin da aka tattara wannan rahoto.
El-Rufai ya fadi yadda suka yi da Buhari
Kun ji cewa tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya tabbatar da cewa da sanin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya fice daga jam'iyyar jam'iyyar APC zuwa SDP.
El-Rufai ya ce ya je har gidan Buhari, a nan ne ya faɗa masa cewa ga shirin da yake yi na barin APC kuma ya amince da hakan.
Tsohon gwamnan ya bayyana yadda yake daukar Buhari a siyasa yana mai cewa mai gidansa ne na farko a kuma ba ya ɗaukar kowane irin mataki tun yana gwamna sai ya tuntuɓe shi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng